WAƘA TA 97
Kalmar Allah Za Ta Sa Mu Rayu
Hoto
	- 1. Kalmar Allah na ba da rai - Mai inganci sosai. - Kalmar tana da tamani, - Fiye da abinci. - Muna cin amfanin Kalmar, - Yau da kuma gobe. - (AMSHI) - Wajibi ne mu karanta - Kalmar Allah sosai. - Karanta Kalmar za ta sa - Mu amfana sosai. 
- 2. Kalmar Allah na sa mu san - Labaran mutane, - Mutane amintattu fa, - Masu gaba gaɗi. - Karanta duk labarinsu - Yana ƙarfafa mu. - (AMSHI) - Wajibi ne mu karanta - Kalmar Allah sosai. - Karanta Kalmar za ta sa - Mu amfana sosai. 
- 3. Koyaushe in mun karanta - Kalmar Maɗaukaki, - Tana ƙarfafa mu sosai, - Tana sa mu jimre. - In mun daraja Kalmarsa, - Za mu sami bege. - (AMSHI) - Wajibi ne mu karanta - Kalmar Allah sosai. - Karanta Kalmar za ta sa - Mu amfana sosai. 
(Ka kuma duba Josh. 1:8; Rom. 15:4.)