Littattafan da Aka Ɗauko Bayanai Daga Cikinsu a Littafin Taro don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu
2-8 GA AFRILU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 26
“Bambanci da Kuma Alaƙar da Ke Tsakanin Idin Ƙetarewa da Jibin Maraice”
(Matta 26:17-20) Ananan a kan rana ta fari ga kwanakin gurasa mara-yeast, almajiran suka zo wurin Yesu, suka ce, A wane wuri kake so mu shirya maka ka ci Faska? 18 Ya ce, ku tafi cikin birni wurin wane, ku ce masa, in ji Malam, sa’ata ta kusa; A gidanka zan ci Faska tare da almajiraina. 19 Almajiran fa suka yi yadda Yesu ya umurce su; Suka shirya Faska kuma. 20 Ana nan sa’ad da maraice ta yi, yana nan zaune wurin ci tare da almajiran goma sha biyu.
nwtsty hotuna da kuma bidiyo
Abincin Idin Faska
Abincin da ake ci a lokacin idin Faska su ne: gasashen ɗan rago (ba a karya kashin ɗan ragon) (1); gurasa mara yisti (2); da ganyaye masu ɗaci (3). (Fit 12:5, 8; L. Li 9:11) Ganyaye masu ɗacin suna tuna wa Isra’ilawan irin wahalar da suka sha sa’ad da suke bauta a ƙasar Masar. Yesu ya yi amfani da gurasa mara yisti don ya kwatanta kamiltaccen jikinsa. (Mt 26:26) Manzo Bulus ma ya kira Yesu “Ɗan Ragonmu na Idin Ƙetarewa.” (1Ko 5:7, Littafi Mai Tsarki) A ƙarni na farko, ruwan inabi (4) ma yana cikin abincin idin Ketarewa. Yesu ya yi amfani da ruwan inabin don ya kwatanta jininsa da za a yi hadaya da shi.—Mt 26:27, 28.
(Matta 26:26) Suna cikin ci, sai Yesu ya ɗauki gurasa, ya yi godiya, ya karya; ya ba almajiran, ya ce, Ku karɓa, ku ci; wannan [“wakiltar,” NW ] jikina ne.
nwtsty na nazarin Mt 26:26
ya ɗauki gurasa . . . ya karya: Gurasar da aka fi ci a ƙasashe da suke kewaye da Isra’ila tana da laushi, amma idan an yi gurasar babu yisti, takan yi ƙarfi. Yadda Yesu kakkarya gurasar ba ta wakiltar kome, domin haka ne ake karya gurasa mara yisti a zamaninsa.—Ka duba na nazarin Mt 14:19.
ya yi godiya: furucin nan yana nufin addu’a da Yesu ya yi yana yabon Allah da kuma gode masa.
wakilta: Manufar kalmar Helenancin nan e·stinʹ da aka yi amfani da shi tana nufin “ma’ana” ko “nufin.” Kuma Manzannin sun fahimci abin da Yesu yake nufi domin a lokaci da ya yi wannan maganar, yana tare da su a wurin kuma gurasar da suke so su ci ma tana gabansu. Saboda haka, gurasar da suka ci ba asalin jikin Yesu ba ne. Kalmar Helenancin ba ta nufin asalin jikin Yesu, shi ya sa aka yi amfani da ita a littafin Mt 12:7, kuma wasu juyin Littafi Mai Tsarki da yawa sun fassara kalmar, “wakilta.”
(Matta 26:27, 28) Kuma ya ɗauki ƙoƙo, ya yi godiya, ya ba su kuma, ya ce, Dukanku ku sha daga cikinsa; 28 gama wannan jinina ne na alkawari, wanda an zubar domin mutane da yawa zuwa gafarar zunubai.
nwtsty na nazarin Mt 26:28
jinina ne na alkawari: Jehobah ya yi alkawari da shafaffun Kiristoci ta wurin hadayar da Yesu ya yi. (Ibr 8:10) Furucin da Yesu ya yi amfani da shi a nan ya yi daidai da wanda Musa ya yi amfani da shi a dutsen Sinai, a lokacin da Jehobah yake ƙulla yarjejeniya da Isra’ilawa kuma Musa ne mai shiga tsakaninsu. (Fit 24:8; Ibr 9:19-21) Kamar yadda Jehobah ya yi alkawari da Isra’ilawa ta wurin jinin awaki da bijimai, haka nan Ya yi alkawari da shafaffun Kiristoci ta wurin jinin Yesu. Wannan alkawarin ya soma aiki a ranar Fentakos 33 bayan haihuwar Yesu.—Ibr 9:14, 15.
Neman Abubuwa Masu Tamani:
(Matta 26:17) Ananan a kan rana ta fari ga kwanakin gurasa mara-yeast, almajiran suka zo wurin Yesu, suka ce, A wane wuri kake so mu shirya maka ka ci Faska?
nwtsty na nazarin Mt 26:17
A kan rana ta fari ga kwanakin gurasa mara-yisti: Akan soma yin Idin Gurasa Mara Yisti a ranar 15 ga watan Nisan, wato kwana ɗaya ke nan bayan Idin Ƙetarewa (14 ga watan Nisan), ana kuma yin Idin Gurasa Mara Yistin na kwana bakwai. (Ka duba sashe na 19 na littafin nan Taimako don Nazarin Kalmar Allah.) A zamanin Yesu, bayan an yi Idin Ƙetarewa, sai a yi “Idin Gurasa Mara-Yisti” na kwanaki bakwai. Da yake ranar da ake yin Idin Ƙetarewa da ranakun Idin Gurasa Mara-Yisti sun yi kusa da juna kuma suna da alaƙa, akan kira dukan kwanaki takwas ɗin ‘Idin Gurasa Mara-Yisti.’ (Lu 22:1) Ana iya maye gurbin furucin nan “A kan rana ta fari ga,” da “Kafin rana ta.” (Ka gwada da Yoh 1:15, 30, a Juyi Mai Fitar da Ma’ana, a wurin an fassara kalmar Helenanci da ke nufin “ta fari” [proʹtos] zuwa “kafin” yayin da ake magana a kan abu kusan iri ɗaya. Ayar ta ce: “Kafin [proʹtos] ni yana nan.”) Da yake haka Helenawa da Yahudawan suka saba yi, shi ya sa almajiran Yesu suka yi masa wannan tambayar a ranar 13 ga Nisan. A ranar 13 ga Nisan, almajiran Yesu sun shirya abincin Idin Ƙetarewar kuma suka ci ‘sa’ad da yamma ta yi’ a farkon ranar 14 ga Nisan.—Mk 14:16, 17.
(Matta 26:39) Kuma ya yi gaba kaɗan, ya fāɗi a fuskatasa, ya yi addu’a, ya ce, Ya Ubana, idan ya yiwu, ka bar wannan ƙoƙo ya shuɗe mani: amma dai, ba nawa nufi za a bi ba, sai naka.
nwtsty na nazarin Mt 26:39
ka bar wannan ƙoƙo ya shuɗe mani: A cikin Littafi Mai Tsarki, akan yi amfani da “ƙoƙo” don a wakilci nufin Allah ko kuma aikin da aka ba wa wani don a cika nufin Allah. (Ka duba na nazarin Mt 20:22.) Yesu ya damu sosai cewa tuhumar sa da za a yi cewa shi mayaudari ne da mai yin saɓo kuma a kashe shi zai ɓata sunan Allah. Shi ya sa ya yi addu’a cewa a bar ‘ƙoƙon’ ya shuɗe masa.
Karatun Littafi Mai Tsarki:
(Matta 26:1-19) Da Yesu ya gama duk wannan magana, sai ya ce wa almajiransa, 2 “Kun san Idin Ƙetarewa saura kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum a gicciye shi. 3 Sai manyan firistoci da shugabannin jama’a suka taru a gidan babban firist, mai suna Kayafa. 4 Suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci su kashe shi. 5 Amma suka ce, “Ba dai a lokacin idi ba, don kada jama’a ta yi hargitsi.” 6 To, sa’ad da Yesu ke Betanya a gidan Saminu kuturu, 7 sai wata mace ta zo wurinsa da wani ɗan tulu na man ƙanshi mai tsadar gaske, ta tsiyaye masa a kā, lokacin da yake cin abinci. 8 Amma da almajiran suka ga haka, sai suka ji haushi suka ce, “Wannan almubazzaranci fa! 9 Gama da ma an sayar da man nan kuɗi mai yawa, an ba gajiyayyu! 10 Yesu kuwa da ya lura da haka, sai ya ce musu, “Don me kuke damun matan nan? Ai, alheri ta yi mini, na gaske kuwa. 11 Kullum kuna tare da gajiyayyu, amma ba kullum ne kuke tare da ni ba. 12 Zuba man nan da ta yi a jikina, ta yi shi ne domin tanadin jana’izata. 13 Hakika, ina gaya muku, duk inda za a yi bisharan nan a duniya duka, abin da matan nan ta yi za a riƙa faɗarsa don tunawa da ita.” 14 Sai ɗaya daga cikin sha biyun nan, mai suna Yahuza Iskariyoti, ya je wurin manyan firistoci, 15 ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi a gare ku?” Sai suka ƙirga kuɗin azurfa talatin, suka ba shi. 16 Tun daga lokacin nan ne ya nemi hanyar da zai bashe shi. 17 To, a ranar farko ta idin abinci marar yisti sai almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, “Ina kake so mu shirya maka cin Idin Ƙetarewa?” 18 Sai ya ce, “Ku shiga gari wurin wāne, ku ce masa, ‘Malam ya ce lokacinsa ya yi kusa, zai ci Idin Ƙetarewa a gidanka tare da almajiransa.’ ” 19 Almajiran kuwa suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka shirya Idin Ƙetarewa.
9-15 GA AFRILU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 27-28
“Ku Je ku Taimaki Mutane Su Zama Mabiyan Yesu—Me Ya Sa, A Ina, Ta Yaya?”
(Matta 28:18) Yesu kuwa ya zo wurinsu, ya yi zance da su, ya ce, Dukan hukunci a cikin sama da ƙasa an bayar gare ni.
(Matta 28:19) Ku tafi fa, ku almajirtar da dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma zuwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki:
nwtsty na nazarin Mt 28:19
ku almajirantar: Kalmar aikatau na Ibranancin nan ma·the·teuʹo da aka yi amfani da ita tana iya nufin “koyarwa,” wato koyar da mutane su zama almajirai. (Ka duba abin da ke littafin Mt 13:52, a wurin an yi amfani da “almajirtar.”) Furucin nan “kuna yi musu baftisma” da “koyarwa” sun nuna abin da “almajirtarwa” ta ƙunsa.
dukan al’ummai: Ko da yake ayar ta ce dukan al’ummai, amma wannan wajen yana magana ne game da mutanen da suka fito daga al’ummai ko ƙasashe dabam-dabam. An yi amfani da kalmar Helenancin nan “musu” a furucin nan kuna musu baftisma, saboda hakan, yana nufin mutane ne ba “al’ummai” ba. Wannan umurnin da Yesu ya bayar cewa a yi wa’azi ga “dukan al’ummai” sabon umurni ne. Kafin a haifi Yesu, Littafi Mai Tsarki ya nuna mana cewa idan mutanen da ba Isra’ilawa ba suka amince su soma bauta wa Jehobah, za su iya zama tare da Isra’ilawa. (1Sa 8:41-43) Amma a wannan karon, Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa su je su yi wa dukan mutane wa’azi ba Yahudawa kawai ba. Ya kuma nuna cewa Kiristoci za su yi wa’azi a duk faɗin duniya.—Mt 10:1, 5-7; R. Yoh 7:9; ka duba bayanin da ke nazarin Mt 24:14.
(Matta 28:20) kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku: ga shi kuwa ina tare da ku kullayaumi har matuƙar zamani.
nwtsty na nazarin Mt 28:20
kuna koya musu: Kalmar Helenancin nan da ke nufin “a koyar” ta ƙunshi ba da umurni da yin bayani da bayyana ma’anar wani abu da kuma ba da hujjoji. (ka duba bayanin da ke nazarin Mt 3:1; 4:23.) Za a ci gaba da koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da Yesu ya koyar. Hakan ya ƙunshi bayyana musu koyarwarsa da yadda za su bi koyarwar da kuma misalinsa.—Yoh 13:17; Afi 4:21; 1Bi 2:21.
Neman Abubuwa Masu Tamani:
(Matta 27:51) Sai labulen da ke cikin Haikalin ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. Ƙasa ta yi girgiza, duwatsu kuma suka tsattsage.
nwtsty na nazarin Mt 27:51
labule: Wannan abin yana da kyau sosai kuma shi ne ya raba wuri Mai Tsarki da wuri Mafi Tsarki. Al’adar Yahudawa ta nuna cewa wannan labulen yana da tsayin kafa 60 da faɗin kafa 30, kuma kaurinsa ya kai kusan inci 3. Yadda Jehobah ya tsage labulen ya nuna fushin da yake yi da mutanen da suka kashe Ɗansa. Ƙari ga haka, ya nuna cewa daga lokacin ’yan Adam za su iya zuwa sama.—Ibr 10:19, 20.
haikali: Kalmar Helenancin nan na·osʹ tana nufin tsakiyar hankalin, inda aka raba wurin Mai Tsarki da kuma Mafi Tsarki.
(Matta 28:7) Ku tafi da sauri kuwa, ku faɗa wa almajiransa, Ya tashi daga matattu; ga shi kuwa yana tafiya gabanku zuwa cikin Galili; can za ku gan shi: ga shi, na faɗa maku.
nwtsty na nazarin Mt 28:7
ku faɗa wa almajiransa ya tashi daga matattu: Waɗannan matan ne aka fara gaya musu cewa an ta da Yesu daga mutuwa kuma aka umurce su su gaya wa sauran almajiransa. (Mt 28:2, 5, 7) A al’adar Yahudawa, ba a amincewa da shaidar mace a kotu. Amma mala’ikan Jehobah ya daraja matan nan ta wajen ba su wannan aiki mai kyau.
Karatun Littafi Mai Tsarki:
(Matta 27:38-54) Sai kuma aka gicciye ’yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a dama, ɗaya a hagun. 39 Masu wucewa suka yi ta yi masa baƙar magana, suna kaɗa kai, 40 suna cewa, “Kai da za ka rushe Haikalin, ka kuma gina shi cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, to, sauko daga gicciyen mana!” 41 Haka kuma manyan firistoci da malaman Attaura da shugabanni suka riƙa yi masa ba’a, suna cewa, 42 “Ya ceci waɗansu, ya kuwa kasa ceton kansa. Ai, Sarkin Isra’ila ne, yā sauko mana daga gicciyen yanzu, mu kuwa mā gaskata da shi. 43 Yā dogara ga Allah, to, Allah ya cece shi mana yanzu, in dai yana sonsa, don ya ce wai shi Ɗan Allah ne.” 44 Har ’yan fashin nan da aka gicciye su tare ma, su suka zazzage shi kamar waɗancan. 45 To, tun daga tsakar rana, duhu ya rufe ƙasa duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma. 46 Wajen ƙarfe uku kuma sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktāni?” Wato “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?” 47 Da waɗansu na tsaitsayen suka ji haka, sai suka ce, “Mutumin nan na kiran Iliya ne.” 48 Sai nan da nan ɗaya daga cikinsu ya yiwo gudu, ya ɗauko soso ya jiƙa shi da ruwan tsami, ya soka a sanda, ya miƙa masa ya sha. 49 Amma sauran suka ce, “Ku bari mu gani ko Iliya zai zo ya cece shi.” 50 Sai Yesu ya sāke ɗaga murya da ƙarfi, sa’an nan ya sāki ransa. 51 Sai labulen da ke cikin Haikalin ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. Ƙasa ta yi girgiza, duwatsu kuma suka tsattsage. 52 Aka bubbuɗe kaburbura, tsarkaka da yawa da ke barci kuma suka tashi. 53 Suka firfito daga kaburburan, bayan ya tashi daga matattu, sai suka shiga tsattsarkan birnin, suka bayyana ga mutane da yawa. 54 Sa’ad da jarumin da waɗanda ke tare da shi suna tsaron Yesu suka ga rawar ƙasar da kuma abin da ya auku, sai duk tsoro ya kama su, suka ce, “Hakika wannan Ɗan Allah ne!”
16-22 GA AFRILU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MARKUS 1-2
“An Gafarta Maka Zunubanka”
(Markus 2:3-5) Ananan sai, aka kawo masa wani mutum, mai ciwon inna, mutane huɗu ke ɗauke da shi. 4 Sa’anda suka kāsa isa wurinsa saboda taro, suka buɗe rufin soro inda ya ke: bayan da suka buɗe soron sai suka saukar da shimfiɗar da mai ciwon inna yake kwanciya bisa. 5 Yesu kuwa da ya ga bangaskiyarsu ya ce wa mai ciwon innan, Ɗa, aka gafarta zunubanka.
jy 67 sakin layi na 3-5
“An Gafarta Maka Zunubanka”
Sa’ad da Yesu yake koyarwa a wani gida cike da mutane, sai wasu mutane guda huɗu suka kawo wani mutum da yake da ciwon inna a kan gado. Mutanen suna so Yesu ya warkar da abokinsu. Amma, saboda mutane sun cika gidan, sun ‘kāsa isa wurin da Yesu yake.’ (Markus 2:4) Babu shakka, ba su ji daɗi ba. Sai suka hau saman gidan kuma suka buɗe rufin, suka sauƙar da mutumin a daidai inda Yesu yake.
Yesu ya yi fushi domin mutanen sun dakatar da wa’azin da yake yi ne? A’a! Bangaskiyar mutanen ta burge Yesu sosai, sai ya ce wa mutumin: “An gafarta maka zunubanka.” (Matta 9:2, LMT) Amma Yesu yana da ikon gafarta zunubai kuwa? Abin da ya faɗa ya dami Farisiyawa da marubuta da ke wurin kuma suka soma tunani a cikin zuciyarsu suna cewa: “Don me mutumin nan yake faɗin haka? Yana saɓon Allah; wa ke da iko shi gafarta zunubai in ba Allah kadai ba?”—Markus 2:7.
Da Yesu ya gane tunanin da suke yi a zuciyarsu sai ya ce: ‘Don me kuke tunanin waɗannan abubuwa a cikin zukatanku? Wanne ne ya fi sauƙi, da a ce wa mai-ciwon inna, An gafarta zunubanka; ko kuma a ce masa, Tashi, ka ɗauki shimfiɗarka, ka yi tafiya?’ (Markus 2:8, 9) Hakika, da yake Yesu zai yi hadaya jim kaɗan, zai iya gafarta zunubin mutumin.
(Markus 2:6-12) Amma akwai waɗansu daga cikin marubuta suna nan zaune, suka yi tunani a cikin zuciyarsu. 7 Don me mutumin nan ya ke faɗin haka? yana saɓon Allah; wa ke da iko shi gafarta zunubai in ba Allah kadai ba? 8 Nan da nan kuwa Yesu, da ya gane cikin ruhunsa suna tunani haka a ransu, ya ce masu, Don me ku ke tunanin waɗannan abubuwa a cikin zukatanku? 9 Wannene ya fi sauƙi, da a ce wa mai-ciwon inna, Aka gafarta zunubanka; ko kuma a ce masa, Tashi, ka ɗauki shimfidarka, ka yi tafiya? 10 Amma domin ku sani Ɗan mutum yana da iko a duniya shi gafarta zunubi (Ya ce wa ciwon inna), 11 Ina ce maka, Ka tashi, ka dauki shimfidarka, ka tafi gidanka 12 Ya tashi, nan da nan ya dauki shimfidassa, ya fita a gabansu duka; har dukansu suka yi mamaki, suka girmama Allah, suka ce, Ba mu taba ganin irin wannan abu ba.
nwtsty na nazarin Mk 2:9
Wanne ne ya fi sauƙi: Yana da sauƙi mutum ya ce zai iya gafarta zunubi, domin ba zai yi wani abu a zahiri da zai tabbatar da cewa ya gafarta zunubin ba. Amma ce wa mai ciwon innar, Tashi . . . ka yi tafiya, dole ne Yesu ya yi wani abin al’ajibi wanda mutanen za su iya gani da idanunsu don su tabbata cewa yana da ikon gafarta zunubi. Wannan labarin da abin da ke littafin Ishaya 33:24 sun nuna cewa mukan yi ciwo don mu masu zunubi ne.
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Markus 1:11) murya kuwa ta fito daga sammai, kai ne Ɗana ƙaunatace, raina yana jin daɗin ka sosai.”
nwtsty na nazarin Mk 1:11
murya kuwa ta fito daga sammai: A cikin littattafan Linjila, Jehobah ya yi magana da ’yan Adam har sau uku, kuma wannan ne karo na farko da ya yi hakan.—Ka duba na nazarin Mk 9:7; Yoh 12:28.
Kai ne Ɗana: Yesu Ɗan Allah ne domin shi halittar ruhu ne. (Yoh 3:16) Daga lokacin da aka haife shi a duniya, Yesu ya zama “ɗan Allah” kamar yadda Adamu yake sa’ad da yake kamili. (Lu 1:35; 3:38) Amma da alama cewa abin da Allah ya faɗa yana nufin wani abu mai muhimmanci ba kawai yana son ya gaya mana wane ne Yesu ba. Abin da Allah ya faɗa da kuma yadda ya shafe Yesu da ruhu mai tsarki, sun nuna cewa Yesu haifaffen Ɗansa ne, da ya ‘sāke haifar sa’ da begen sake komawa sama don ya yi zama. Ƙari ga haka, ya shafe shi da ruhu mai tsarki don ya zama Sarki da Babban Firist da ya zaɓa.—Ka duba Yoh 3:3-6; 6:51; Lu 1:31-33; Ibr 2:17; 5:1, 4-10; 7:1-3.
raina yana jin daɗin ka sosai: Ko kuma, “Na amince da kai sosai.” An yi amfani da furucin daidai a Mt 12:18, kuma an yi ƙaulin ainihin ayar daga littafin Isa 42:1, wurin ya yi magana a kan Almasihu ko Kristi. Yadda Allah ya zuba ma Yesu Ruhu mai tsarki da kuma yadda ya ce Yesu Ɗansa ne, sun nuna cewa Yesu ne Almasihu da aka yi alkawarinsa.—Ka duba na nazarin Mt 3:17; 12:18.
(Markus 2:27, 28) Ya ce musu, aka yi ran assabaci domin mutum, ba a yi mutum domin ran assabbaci ba: 28 Domin haka nan Ɗan mutum ubangiji ne har na ran assabbaci.”
nwtsty na nazarin Mk 2:28
Ubangiji . . . na ran assabbaci: Yesu yana magana game da kansa ne sa’ad da ya yi wannan furucin. (Mt 12:8; Lu 6:5) Hakan yana nufin cewa Yesu yana da ikon yin aikin da Jehobah ya ba shi a ranar Assabaci. (Ka duba Yoh 5:19; 10:37, 38) Yesu ya yi mu’ujizai masu ban al’ajabi a ranar Assabaci, mu’ujizan sun haɗa da warkar da marasa lafiya. (Lu 13:10-13; Yoh 5:5-9; 9:1-14) Mu’ujizai da ya yi sun nuna irin albarkar da talakawan Mulkinsa za su samu kuma hakan zai zama kamar hutun da ake yi a ranar assabaci.—Ibr 10:1.
Karatun Littafi Mai Tsarki
(Markus 1:1-15) Farkon bishara ta Yesu Kristi, Ɗan Allah. 2 Kamar yadda aka rubuta cikin littafin annabi Ishaya, “Duba, na aika manzona a gabanka, wanda za ya shirya hanyarka;” 3 Ga Muryar mai kira a cikin jeji, ku shirya hanyar Ubangiji, ku daidaita tafarkunsa; 4 Lokacin da Yohanna ya zo sai ya fara baftisma a cikin jeji yana kuma wa’azi na baftismar tuba zuwa gafarar zunubai. 5 Sai dukan ƙasar Yahuda, da dukan mutanen Urushalima kuma, suka zo wurinsa; ya yi masu baftisma cikin kogin Urdun, suna shaida zunubansu. 6 Rigar Yohanna kuwa ta gashin rakumi ce, yana kuma da ɗamara na fata a gindinsa, abincinsa kuma fara ce da zuma ta jeji. 7 Sai ya yi wa’azi, ya ce akwai, Wani da ke zuwa daga bayana Wanda ya fi ni iko, ko maɓallin takalmansa ban isa in durƙusa in kwance ba. 8 Lallai na yi maku baftisma da ruwa; amma shi za ya yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki. 9 Ananan a cikin kwanakin nan, Yesu ya fito daga Nazarat ta Galili, Yohanna kuma ya yi masa baftisma cikin Urdun. 10 Sa’anda yana fitowa daga cikin ruwa, nan da nan ya ga sammai suka buɗe, ruhu kuwa da kamar kurciya yake saukowa a bisansa: 11 murya kuwa ta fito daga sammai, kai ne Ɗana ƙaunatacce, raina yana jin daɗin ka sosai. 12 Nan da nan kuwa sai Ruhu ya koro shi zuwa jeji. 13 Yana cikin jejin nan har kwana arba’in, Shaitan kuma na ta yi masa jaraba; daga shi sai namomin jeji; mala’iku kuma suka bauta masa. 14 Bayanda aka kulle Yohanna a cikin kurkuku, sai Yesu ya taho cikin Galili, yana wa’azin bishara ta Allah, 15 ya ce, Zamani ya cika, gashi lokacin bayyanar Mulkin Allah ya zo: ku tuba ku ba da gaskiya ga bisharar nan.
23-29 GA AFRILU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MARKUS 3-4
“Warkarwa a Ranar Assabaci”
(Markus 3:1, 2) Ya sake shiga majami’a; A nan fa akwai wani mutum wanda yake da shanyayyen hannu. 2 Suka zuba masa ido, su gani, ko za ya warkadda shi bisa ran asabarci; domin su tsare shi.
jy 78 sakin layi na 1-2
Mene ne Ya Kamata A Yi a Ranar Assabaci?
Yesu ya sake zuwa haikali wataƙila a Galili a ranar Assabaci. A wajen, ya haɗu da wani mutum da hannunsa na dama ya shanye. (Luka 6:6) Marubuta da Farisawa sun zuba wa Yesu ido. Me ya sa? Sun bayyana abin da ke zuciyarsu sa’ad da suka yi tambayar nan: “Ya halalta a yi warkaswa a kan ran assabbaci?”—Matta 12:10.
Malaman Yahuduwa sun ce bai kamata a warkar da marar lafiya a ranar Assabaci ba sai dai idan mutumin yana bakin mutuwa. Alal misali, idan mutum ya ji rauni a kashinsa a ranar Assabaci, sun ce bai kamata a yi jinyar sa ba. Don haka, tambayoyin da malamai da Farisawan suka yi wa Yesu ba ya nufin cewa sun damu da mutumin nan da yake cikin wahala. Amma sun yi hakan ne don suna neman hanyar da za su kama Yesu da laifi.
(Markus 3:3, 4) Ya ce wa mutumin nan mai-shanyayyen hannu, Ka tashi, ka fito nan a fili. 4 Ya ce masu kuma, Ya halatta a kan ran assabbaci a yi nagarta, ko kuwa a yi ɓarna? a ceci rai, ko kuwa a yi kisa? Amma suka yi shuru.
jy 78 sakin layi na 3
Mene ne Ya Kamata A Yi a Ranar Assabaci?
Amma Yesu ya gane munafuncin su. Ya fahimci cewa yadda suke ɗaukan abin da ya kamata a yi a ranar Assabaci da abin bai kamata a yi ba sun wuce gona da iri. (Fitowa 20:8-10) Kuma sun daɗe suna kushe ayyukansa masu kyau. Sai Yesu ya gaya wa mutumin da ke da shanyayyen hannu cewa: “Ka tashi, ka fito nan a fili.”—Markus 3:3.
(Markus 3:5) Yesu ya duddube su cikin fushi, yana kuma baƙin ciki domin taurin zuciyarsu. Sai ya ce wa mai shanyayyen hannun, “Ka miƙe hannunka.” Sai ya miƙe, hannunsa kuwa ya warke nan da nan.
nwtsty na nazarin Mk 3:5
cikin fushi, yana kuma baƙin ciki: Markus ne kawai ya rubuta yadda Yesu ya ji sa’ad da ya ga taurin zuciyar da malaman addinan suke da shi a wannan lokacin. (Mt 12:13; Lu 6:10) Tun da Bitrus mutum ne da ke son nuna yadda yake ji, wataƙila shi ne ya bayyana wa Markus yadda Yesu ya ji a lokacin.—Ka duba “Gabatarwar Littafin Markus.”
Neman Abubuwa Masu Tamani:
(Markus 3:29, Juyi Mai Fitar da Ma’ana) Amma fa, duk wanda ya yi maganar saɓo ga Allah game da Ruhu Mai Tsarki ba za a taɓa yafe masa ba har abada. Ya yi zunubi na har abada ke nan.
nwtsty na nazarin Mk 3:29
saɓo ga . . . ruhu mai tsarki: Yin saɓo yana nufin zagi ko yin maganganu marasa daɗi game da Allah ko ruhu mai tsarki. Tun da ruhu mai tsarki daga Allah ne, za mu yi wa Allah saɓo idan muka ƙi amincewa da ja-gorancin ruhu mai tsarki da gangan. Kamar yadda littafin Mt 12:24, 28 da kuma Mk 3:22 suka nuna, malaman Yahudawa sun ga cewa ruhun Allah yana tare da Yesu sa’ad da yake yin mu’ujizai, amma suka ce da ruhun Shaiɗan ne yake yin hakan.
zunubi na har abada: Wannan wajen na magana game da zunubin da mutum zai yi da gangan kuma sakamakon zunubin har abada ne; Babu hadayar da za ta iya fanshi mutum daga wannan zunubin.—Ka duba sakin layi na baya da ya yi bayani a kan saɓo ga . . . ruhu mai tsarki da kuma na nazarin Mt 12:31.
(Markus 4:26-29) Ya ce masu kuma, Mulkin Allah haka ya ke, watau kamar mutum ya watsa iri a ƙasa; 27 ya kwana ya tashi dare da rana, iri kuma ya tsira ya yi girma, shi kuwa ba ya san yadda ya ke yi ba. 28 Ƙasa tana ba da amfani don kanta, soshiya tukuna, kana zangarniya, bayan wannan zangarniya da ƙwaya nunanna a ciki. 29 Sa’anda amfani ya nuna, nan da nan sai ya sa magirbi, domin lokacin girbi ya yi.
Karatun Littafi Mai Tsarki:
(Markus 3:1-19a) Ya sake shiga majami’a; A nan fa akwai wani mutum wanda yake da shanyayyen hannu. 2 Suka zuba masa ido, su gani, ko za ya warkadda shi bisa ran asabarci; domin su tsare shi. 3 Ya ce wa mutumin nan mai-shanyayyen hannu, Ka tashi, ka fito nan a fili. 4 Ya ce masu kuma, Ya halatta a kan ran assabbaci a yi nagarta, ko kuwa a yi ɓarna? a ceci rai, ko kuwa a yi kisa? Amma suka yi shuru. 5 Sa’ad da ya duddube su da fushi, yana jin ciwon rai sabada taurin zuciyarsu, sai ya ce ma mutumen, miƙo hannunka. Ya miƙa shi; hannunsa ya komo lafiyayye. 6 Farisawa suka fita, kuma da su da mutanen Hirudus nan-da-nan suka kulla shawara a kansa, yadda za su hallaka shi. 7 Yesu kuwa ya koma tare da almajiransa zuwa bakin teku; Taro mai girma kuwa daga Galili suka bi shi; daga Yahuda, 8 da Urushalima, da Idumiya, da ƙetaren Urdun, kuma daga wajen Sur da Sida, taro mai yawa, da suka ji labarin al’amura masu girma da yake yi, suka zo wurinsa. 9 Ya fada wa almajiransa su kebe masa wani karamin jirgi saboda taro, domin kada su matse shi; 10 gama ya warkadda mutane dayawa; har iyakar waɗanda ke da cuta masu-azaba suka matse shi domin su tabe shi. 11 Ƙazaman ruhohi kuma, yayinda suka gan shi duka, suka faɗi a gabansa, suka yi ihu, suka ce, Kai ne Ɗan Allah. 12 Amma ya dokace su dayawa kada su bayyana shi. Amma ya dokace su dayawa kada su bayyana shi. 13 Ya hau bisa dutsen, ya kirawo waɗanda shi da kansa ya zaba: suka zo wurinsa. 14 Ya sanya goma sha biyu, domin su zauna tare da shi, domin kuma shi aike su garin su yi wa’azi, 15 su kuma sami ikon da za su fitarda aljanu; 16 Ya ba Siman suna Bitrus; 17 Yaƙub kuma ɗan Zabadi, da Yohanna ɗan’uwan Yaƙub; Ya ba su suna Buwanarjis, wato, ’ya’yan sawa ke nan: 18 da Andarawus, da Filibus, da Barthalamawus, da Matta, da Toma, da Yaƙub ɗan Halfa, da Taddawus, da Siman Bakana’na, 19 da Yahuda Iskariyoti, wanda ya ba da shi
30 GA AFRILU–6 GA MAYU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MARKUS 5-6
“Yesu Yana da Ikon Tayar da Ƙaunatattunmu da Suka Mutu”
(Markus 5:38) Suka zo gidan mahukuncin majami’a; Ya ga ana hayaniya, ana kuka, ana kururuwa dayawa.
(Markus 5:39-41) Sa’anda ya shiga, ya ce masu, Don me ku ke yin hayaniya, kuna kuka kuma? yarinya ba matacciya ba ce, amma barci ta ke yi. 40 Suka yi masa dariya da renako. Amma sa’anda ya fitar da dukan su waje, ya ɗauki uban yarinyar da uwatata da waɗanda ke tare da shi, ya shiga wurin da yarinyar take. 41 Ya kama hannun yarinya, ya ce mata, Talitha kumi; watau, Yarinya, ina ce maki, Ki tashi.
nwtsty na nazarin Mk 5:39
ba matacciya ba ce, amma barci take yi: A yawancin lokaci, akan kwatanta mutuwa da barci a cikin Littafi Mai Tsarki. (Za 13:3; Yoh 11:11-14; A. M. 7:60; 1Ko 7:39; 15:51; 1Ta 4:13) Wataƙila Yesu ya faɗi hakan domin yana son ya ta da yarinyar daga mutuwa ne. Kuma hakan zai nuna cewa kamar yadda za a iya tashi mutum daga barci, mutumin da ya mutu ma za a iya tashe shi. Jehobah Allah ‘wanda yake rayar da matattu, yana kiran abubuwan da ba su kasance ba, su kasance,’ shi ne ya ba wa Yesu iko ya ta da yarinyar daga mutuwa.—Ro 4:17.
(Markus 5:42) Nan da nan yarinya ta tashi, ta soma tafiya; gama shekarunta goma sha biyu ne. Suka yi mamaki nan da nan da mamaki mai-girma.
jy 118 sakin layi na 6
Wata Ƙaramar Yarinya Ta Tashi Daga Mutuwa!
Kafin wannan lokaci, Yesu ya gaya wa mutanen da ya warkar da su cewa ƙar su gaya wa kowa abin da faru, kuma abin da ya gaya wa iyayen wannan yarinyar ke nan. Amma da yake iyayen yarinyar da sauran danginsu sun yi farin ciki don abin da faru, sun ‘baza labarin cikin dukan ƙasar.’ (Matta 9:26) Babu shakka, idan ka ga ɗan’uwanka ko wani danginka ya tashi daga mutuwa, za ka yi farin cikin gaya wa mutane, ko ba haka ba? Wannan shi ne karo na biyu da aka rubuta cewa Yesu ya tayar da matacciya.
Neman Abubuwa Masu Tamani:
(Markus 5:19, 20) Ba ya bar shi ba, amma ya ce masa, Ka tafi gida, wurin abokanka kuma, ka ba su labarin al’amura masu girma da jinƙan da Ubangiji ya yi maka, 20 Ya yi tafiyassa, ya fara shela cikin Dikafolis al’amura masu-girma da Yesu ya yi masa: mutane duka suka yi mamaki.
nwtsty na nazarin Mk 5:19
ka ba su labarin: Wannan umurnin ya yi dabam da sauran umurnin da Yesu yake ba wa mutane (Mk 1:44; 3:12; 7:36), ya gaya wa mutumin nan ya gaya wa mutane abin da ya faru da shi. Wataƙila ya yi hakan ne don an kore shi daga yankin, kuma hakan zai sa ba zai iya yi wa mutanen yankin wa’azi ba; ƙari ga haka, zai hana maganganu marasa daɗi da mutane za su faɗa don mutuwar aladun.
(Markus 6:11) Dukan wurin da ba a karɓe ku ba, kuma ba su ji maganarku ba, sa’anda kuna fita ciki, ku karkaɗe kura da ke ƙarƙashin sawayenku domin shaida a kan su.
nwtsty na nazarin Mk 6:11
ku karkaɗe kura da ke ƙarƙashin sawayenku: Yesu yana nufin cewa duk hukuncin da Allah zai kawo ba zai faɗi a kansu ba. An yi amfani da wannan furucin a littafin Mt 10:14 da kuma Lu 9:5. Markus da Luka sun ƙara wani furuci a kai kuma furucin shi ne, domin shaida a kan su. Bulus da Barnaba sun bi wannan umurnin sa’ad da suke Pisidian ta Antakiya. (A. M. 13:51), kuma sa’ad da Bulus yake Koranti, ya karkaɗe rigarsa ya ce: ‘Alhakin jininku yana bisa kanku; ni dai ba ni da laifi.’ (A. M. 18:6) Wataƙila manzannin sun riga sun san da wannan umurnin domin idan Yahudawa masu ibada sosai suka je ƙasar mutanen da ba Yahudawa ba, suna karkaɗe takalmansu kafin su shiga biranen Yahuda don kada ƙasa marar tsarki ta shiga cikin birnin. Amma sa’ad da Yesu ya ba wa mabiyansa wannan umurnin, ba abin da yake nufin ba ke nan.
Karatun Littafi Mai Tsarki:
(Markus 6:1-13) Ya tashi daga nan ya koma garinsu, almajiransa kuwa suka bi shi. 2 Da Asabar ta yi, sai ya fara koyarwa a majami’a. Mutane da yawa da suka saurare shi, suka yi mamaki, suna cewa, “Ina mutumin nan ya sami wannan abu duka? Wace hikima ce aka ba shi haka? Dubi irin waɗannan mu’ujizan da aka aikatawa ta hannunsa! 3 Shin, wannan ba shi ne masassaƙin nan ba, ɗan Maryamu, ɗan’uwan su Yakubu, da Yusufu, da Yahuza, da kuma Saminu? ‘Yan’uwansa mata kuma ba ga su tare da mu ba?” Suka yi tuntuɓe sabili da shi. 4 Sai Yesu ya ce musu, “Ai, annabi ba ya rasa girma sai dai a garinsu, da cikin ’yan’uwansa, da kuma gidansu.” 5 Bai ko iya yin wata mu’ujiza a can ba, sai dai ya ɗora wa marasa lafiya kaɗan hannu ya warkar da su. 6 Ya yi mamakin rashin bangaskiyarsu. Sai ya zazzaga ƙauyuka yana koyarwa. 7 Sai ya kira sha biyun nan, ya fara aikensu biyu-biyu, ya kuma ba su iko a kan baƙaƙen aljannu. 8 Ya umarce su kada su ɗauki guzuri don tafiyar, ko gurasa, ko burgami, ko kuɗi ma a ɗamararsu, sai dai sanda kawai, 9 amma su sa takalmi, kada kuma su haɗa taguwa biyu. 10 Ya ce musu, “Duk gidan da kuka sauka, ku zauna a nan har ku tashi. 11 Duk inda aka ƙi yin na’am da ku, aka kuma ƙi sauraronku, in za ku tashi, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku don shaida a kansu.” 12 Haka fa, suka fita, suna wa’azi mutane su tuba. 13 Suka fitar da aljannu da yawa, suka kuma shafa wa marasa lafiya da yawa mai, suka warkar da su.