WAƘA TA 86
Muna Bukatar Jehobah Ya Koyar da Mu
Hoto
(Ishaya 50:4; 54:13)
1. Mu zo da murna mu bauta wa Jehobah.
Allah ya ce: ‘Mu zo mu sami rai.’
Jehobah Allah, na koyar da mu
Domin dukanmu mu san gaskiya.
2. Zuwa taro na da muhimmanci sosai,
Allah na koya mana gaskiya.
Ruhun Jehobah na taimakon mu,
’Yan’uwanmu ma na ƙarfafa mu.
3. Rera yabo ga Allahnmu na da daɗi!
Furucin bayin Allah na da kyau!
Za mu kasance da bayin Allah!
E, mu riƙa kasancewa da su!
(Ka kuma duba Ibran. 10:24, 25; R. Yoh. 22:17.)