Littattafan da Aka Ɗauko Bayanai Daga Cikinsu a Littafin Taro don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu
4-10 GA YUNI
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MARKUS 15-16
“Yesu Ya Cika Annabcin Littafi Mai Tsarki”
(Markus 15:3-5) Sai manyan firistoci suka yi ta zarginsa a kan abubuwa da yawa. 4 Sai Bilatus ya sāke tambayarsa ya ce, “Ga shi fa, ana zarginka a kan abubuwa da yawa, ba za ka ba da amsa ba?” 5 Amma har yanzu, Yesu bai ƙara yi wata magana ba, har abin ya dami Bilatus.
(Markus 15:24) Sai suka giciye shi. Suka kuma rarraba rigunansa a tsakaninsu, suka yi ƙuri’a a kansu domin su ga abin da kowa zai samu.
(Markus 15:29, 30) Mutanen da suke wucewa suka yi ta yin maganganun reni, suna kaɗa kai, suna cewa, “Ahaf! Kai da za ka rushe Haikali, za ka kuma gina shi cikin kwana uku, 30 to, ka ceci kanka ka sauko mana!”
nwtsty na nazarin Mk 15:24, 29
rarraba rigunansa: Littafin Yoh 19:23, 24 ya ƙara wasu bayanai da Matiyu da Markus da kuma Luka ba su yi ba: Sojojin Romawan sun jefa ƙuri’a a kan tufafin Yesu guda biyu; sojojin sun raba tufafinsa na waje zuwa ‘kashi huɗu don kowanne soja ya ɗauki kashi ɗaya’; ba sa so su raba rigarsa na ciki, shi ya sa suka yi ƙuri’a a kan rigar: ƙuri’ar da suka yi ta cika annabcin da littafin Za 22:18 ya yi game da Almasihu. A lokacin, sojoji sun saba kwace tufafin mutanen da suka kashe. Don haka, ana cire rigar wanda ake so a rataye da kuma kayan mallakarsa kafin a kashe shi. Hakan ba ƙaramin cin mutunci ba ne.
suna kaɗa kai: Akan ambata wasu kalamai sa’ad da ake yin hakan kuma wannan kaɗa kai da suka yi na ba’a ne da reni. Waɗannan mutanen da suke wucewa sun cika annabcin da ke littafin Za 22:7.
(Markus 15:43) Sai wani mutum mai suna Yusuf daga Arimatiya ya zo. Shi ɗan majalisa ne, mai mutunci kuwa, wanda yake marmarin mulkin Allah ya zo. Ya yi ƙarfin hali ya tafi wurin Bilatus, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.
(Markus 15:46) Yusuf kuwa ya sayo yadin lilin, ya sauko da jikin Yesu, ya nannaɗe shi a yadin lilin, ya sa shi kabarin da aka haƙa a jikin dutse. Sa’an nan ya gangaro da wani dutse ya rufe bakin kabarin.
nwtsty na nazarin Mk 15:43
Yusuf: Yadda marubutan Linjila suka kwatanta Yusuf ya nuna mana bambancin da ke tsakanin kowannensu. Matiyu mai karɓan haraji ya ce Yusuf “mai arziki” ne; Markus, wanda ya yi rubutunsa yadda Romawa za su fahimta ya ce, Yusuf “ɗan majalisa ne, mai mutunci” wanda yake jiran Mulkin Allah ya zo; Luka, mai kula da marasa lafiya ya ce Yusuf “wani mutumin kirki ne, mai adalci” kuma bai yarda da abin da Majalisa suka yi shirin yi wa Yesu ba; Yohanna ne kaɗai ya ce Yusuf ‘almajirin Yesu ne, amma a ɓoye domin yana tsoron Yahudawa.’—Mt 27:57-60; Mk 15:43-46; Lu 23:50-53; Yoh 19:38-42.
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Markus 15:25) Da ƙarfe tara na safe ne suka [“rataye,” NW ] shi.
nwtsty na nazarin Mk 15:25
ƙarfe tara na safe: Akwai bambanci tsakanin ayar nan da littafin Yoh 19:14-16. Littafin Yohanna ya ce da wajen “tsakar rana” ko “wajen sa’a shida,” wato ƙarfe 12 na rana ne Bilatus ya ba da Yesu don a hukunta shi. Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai gaya mana dalilin da ya sa aka samu bambanci tsakanin lokacin da Markus ya ambata da na Yohanna ba, amma bari mu yi la’akari da wasu dalilan da suka sa wataƙila hakan ya faru: Sa’ad da suke ba da labarin abubuwan da suka faru a rana ta ƙarshe kafin a kashe Yesu, marubutan Linjila sun ambata lokuta iri ɗaya. Su huɗun sun rubuta cewa firistoci da malamai sun yi taro da sassafe, bayan haka suka kai Yesu wurin Gwamnan Romawa mai suna Bilatus Ba-Bunti. (Mt 27:1, 2; Mk 15:1; Lu 22:66–23:1; Yoh 18:28) Matiyu da Markus da Luka sun rubuta cewa sa’ad da Yesu yake kan gungumen, duhu ya rufe ko’ina a ƙasar “tun daga tsakar rana, . . . har zuwa wajen ƙarfe uku na yamma.” (Mt 27:45, 46; Mk 15:33, 34; Lu 23:44) Wataƙila dalilin da ya janyo wannan bambancin shi ne: Wasu sun ce dukān da ake yi wa mai laifi yana cikin hukuncin da aka yanke masa. A wasu lokuta, ana yi wa mai laifin dukā sosai har mutuwarsa. Amma da aka zo kan Yesu, sun yi masa dukā sosai kuma hakan ya sa bai iya ɗaukan gungumen ba har sai da wani ya ɗauka masa. (Lu 23:26; Yoh 19:17) Idan dukā yana cikin hukuncin da ake yi wa mutum kafin a kashe shi, babu shakka an ɗan bata lokaci kafin a rataye Yesu a kan gungumen. Shi ya sa littafin Mt 27:26 da Mk 15:15 suka ce an yi wa Yesu dukā kafin aka je aka rataye shi. Don haka, duka marubutan suna da ra’ayinsu game da lokacin da aka soma hukunta Yesu, shi ya sa suka ambata lokuta dabam-dabam. Wataƙila hakan ne ya sa Bilatus ya yi mamakin jin cewa Yesu ya mutu ba da daɗewa ba bayan an rataye shi. (Mk 15:44) Ƙari ga haka, marubutan Littafi Mai Tsarki sukan raba kwana ɗaya zuwa kashi huɗu kuma kowane kashi yana da sa’o’i uku-uku, wato daga ƙarfe 6 na safe zuwa kafe 9 na safe da ƙarfe 10 na safe zuwa ƙarfe 12 na rana da ƙarfe 1 na rana zuwa ƙarfe 3 na rana da kuma ƙarfe 4 zuwa ƙarfe 6 na yamma. Shi ya sa suke yawan ambata ƙarfe 9 na safe da 12 na rana da 3 na rana kuma suna fara ƙirgen daga ƙarfe 6 na safe ne. (Mt 20:1-5; Yoh 4:6; A. M. 2:15; 3:1; 10:3, 9, 30) Ban da haka ma, yadda mutane a lokacin suke ƙirga lokacinsu ba ɗaya ba ne, shi ya sa ake yawan amfani da kalmar nan “wajen,” kamar yadda muka gani a littafin Yoh 19:14. (Mt 27:46; Lu 23:44; Yoh 4:6; A. M. 10:3, 9) A taƙaice: Wataƙila dalilin da ya sa Markus ya ce ƙarfe 9, shi ne ya haɗa da lokacin da aka yi wa Yesu dukā zuwa lokacin da aka rataye shi. Yohanna kuma bai haɗa da lokacin da aka yi wa Yesu dukā ba, maimakon haka, ya ambaci lokacin da aka rataye Yesu kawai. Wataƙila Markus ya ambata sa’a ta ƙarshe a kashi na farko (wajen ƙarfe 9 na safe), Yohanna kuma ya ambata sa’a ta ƙarshe a kashi na biyu (wajen ƙarfe 12 na rana) kuma Yohanna bai faɗi ainihin lokacin ba, amma ya ce “wajen” ko kuma kusan. Waɗannan dalilan ne wataƙila suka sa marubutan Linjila ba su ambata lokacin da aka hukunta Yesu iri ɗaya ba. Markus ya kammala littafinsa shekaru da yawa kafin Yohanna ya yi na shi, kuma wannan bambancin da aka samu a rubutunsu ya nuna mana cewa Yohanna bai kofi abin da Markus ya rubuta ba.
(Markus 16:8) Matan kuwa suka fita da gudu, sun ruɗe suna rawar jiki. Ba su kuma ce wa kowa kome ba, domin suna jin tsoro.
nwtsty na nazarin Mk 16:8
domin suna jin tsoro: Bisa ga littattafai na farko na Linjilar Markus, an kammala Linjilar da abin da aka faɗa a aya takwas. Amma wasu sun ce ba zai yiwu a ce an kammala asalin Linjilar Markus da abin da ke aya ta takwas ba. Idan ka yi la’akari da yadda Markus ya yi rubutunsa, za ka gane cewa abin da suka faɗa ba gaskiya ba ne. Ban da haka ma, wasu masu binciken Littafi Mai Tsarki a ƙarni na huɗu masu suna Jerome da Eusebius sun nuna cewa an kammala asalin Linjilar Markus da furucin nan “domin suna jin tsoro.”
Akwai wasu rubuce-rubucen Helenanci da yawa da kuma wasu fassara zuwa yaruka dabam-dabam da aka ƙara gajeren bayani bayan aya takwas, wasu kuma suka yi dogon bayani. Ana samun dogon bayanin (wanda ya ƙunshi ayoyi 12 da aka ƙara) a wasu rubuce-rubucen Helenanci na dā kamar su Codex Alexandrinus da Codex Ephraemi Syri da kuma Codex Bezae Cantabrigiensis, dukansu sun wanzu daga ƙarni na biyar bayan haihuwar Yesu. Za a iya samun dogon bayanin a juyin Latin Vulgate da Curetonian Syriac da kuma juyin Syriac Peshitta. Amma wannan dogon bayanin bai bayyana a rubuce-rubucen Helenanci na farko a ƙarni na huɗu ba, wato, ba a ga bayanin a littattafan nan Codex Sinaiticus da Codex Vaticanus ko a littattafan nan Codex Sinaiticus Syriacus na ƙarni na huɗu da biyar ba. Ƙari ga haka, ba za ka ga dogon bayanin a littafin farko na Sahidic Coptic na rubutun Markus a ƙarni na biyar ba. Hakazalika, a littafin farko na Markus a yaren Armeniya da Jojiya, aya ta 8 ce ƙarshen Linjilar.
Wasu rubuce-rubucen Helenanci da kuma waɗanda aka fassara zuwa wasu yaruka bayan haka suna ɗauke da gajeren bayani (da ya ƙunshi wasu ’yan jimloli). Littafin Codex Regius na ƙarni na takwas bayan haihuwar Yesu yana da dogo da kuma gajeren bayanin amma ya fara ne da gajeren bayanin. Kuma kafin su yi kowane bayanin kammalawar, sun ce gajere da kuma dogon bayanin ba ya cikin asalin Littafi Mai Tsarki.
GAJEREN BAYANI
Gajeren bayanin da aka saka bayan Mk 16:8 ba ya cikin ainihin Nassosin Littafi Mai Tsarki. Bayanin yana kamar haka:
Kuma duka abubuwan da aka dokace su su yi sun gaya ma waɗanda suke tare da Bitrus. Bayan haka, sai Yesu da kansa ya aike su zuwa gabas da yamma domin su yi wa’azin ceto.
DOGON BAYANI
Dogon bayanin da aka saka bayan Mk 16:8 ba ya cikin ainihin Nassosin Littafi Mai Tsarki. Bayanin yana kamar haka:
9 Da Yesu ya tashi daga matattu da sassafe a rana ta farko ta mako, ya fara nuna kansa ga Maryamu daga Magadala, wato macen nan da Yesu ya fitar mata da aljannu bakwai. 10 Ita kuwa ta tafi ta faɗa wa mutanen da suke tare da shi tun dā, waɗanda suke baƙin ciki suna ta kuka. 11 Amma da suka ji cewa Yesu yana da rai, har ma ta gan shi, ba su ba da gaskiya ba. 12 Bayan haka Yesu ya canja kamanni ya nuna kansa ga waɗansu biyu daga cikin almajiran a lokacin da suke tafiya ƙauye. 13 Sai biyun nan suka koma suka faɗa wa sauran, amma har yanzu suka ƙi su yarda da labarin. 14 Daga baya Yesu ya nuna kansa ga sha ɗayan a daidai lokacin da suke cin abinci. Sai ya tsawata musu a kan rashin bangaskiyarsu da taurin kansu, don ba su gaskata da waɗanda suka gan shi bayan tashinsa ba. 15 Ya kuma ce musu, “Ku tafi ko’ina a dukan duniya, ku yi wa dukan ’yan Adam shelar labarin nan mai daɗi. 16 Duk wanda ya ba da gaskiya, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma duk wanda ya ƙi ba da gaskiya za a huƙunta shi. 17 Ga abubuwan da masu bina za su yi don shelar gaskiyarsu. A cikin sunana aljannu, za su kuma yi magana da sababbin harsuna. 18 Za su ɗauki macizai da hannuwansu. Idan kuma suka sha dafi, ba zai yi musu kome ba. Za su kuma sa hannuwansu a kan marasa lafiya, su warke.”
19 Bayan da Ubangiji Yesu ya yi musu wannan jawabi, sai aka ɗauke shi aka kai shi cikin sama, ya zauna a hannun dama na Allah. 20 Almajiran kuwa suka fita, suka yi ta wa’azi ko’ina. Ubangiji kuwa ya yi aiki tare da su, yana tabbatar da gaskiyar maganarsu ta wurin alamu masu ban mamakin da ya sa su suka yi tare da maganar.
Karatun Littafi Mai Tsarki
(Markus 15:1-15) Da sassafe manyan firistoci da shugabanni, da malaman Koyarwar Musa, da dukan sauran ’yan majalisa suka yi shawara. Sai suka ɗaure Yesu, suka tafi da shi, gaban Bilatus. 2 Bilatus kuwa ya tambaye shi ya ce, “Kai ne sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa masa ya ce, “Kai ne ka faɗa haka.” 3 Sai manyan firistoci suka yi ta zarginsa a kan abubuwa da yawa. 4 Sai Bilatus ya sāke tambayarsa ya ce, “Ga shi fa, ana zarginka a kan abubuwa da yawa, ba za ka ba da amsa ba?” 5 Amma har yanzu, Yesu bai ƙara yi wata magana ba, har abin ya dami Bilatus. 6 Abin da sarki ya saba yi a lokacin Bikin shi ne, yakan sakar musu ɗan kurkuku ɗaya wanda mutanen suka roƙa. 7 To, akwai wani mai suna Barnabas wanda yake a ɗaure a kurkuku, tare da ’yan tawaye da suka kashe mutum a lokacin da aka yi tawaye. 8 Sai taron jama’a suka zo suka fara roƙon Bilatus ya yi musu abin da ya saba yi. 9 Bilatus ya amsa musu ya ce, “Kuna so in sakar muku sarkin Yahudawa?” 10 Gama ya gane cewa saboda kishi ne ya sa manyan firistoci suka ba da Yesu a hannunsa. 11 Amma manyan firistoci suka zuga jama’a su ce ya saki Barabbas a maimakon Yesu. 12 Sai Bilatus ya tambaye su ya ce, “To, me zan yi da wanda kuke ce da shi sarkin Yahudawa?” 13 Suka tā da murya suka ce, “A gicciye shi!” 14 Bilatus kuwa ya ce musu, “Don me? Wane laifi ya yi?” Sai suka ƙara tā da murya suna cewa, “A gicciye shi!” 15 Da yake Bilatus yana so ya faranta wa jama’a zuciya, sai ya sakar musu Barabbas. Bayan da ya sa aka yi wa Yesu bulala, sai ya ba da shi domin a giccye shi.
11-17 GA YUNI
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | LUKA 1
“Mu Zama Masu Sauƙin Kai Kamar Maryamu”
(Luka 1:38) Maryamu ta ce, “To, ni baiwar Allah ce, bari ya zama mini kamar yadda ka faɗa.” Sai mala’ikan ya tafi.
(Luka 1:46-55) Maryamu ta ce, “Zuciyata tana yabon Ubangiji. 47 Raina yana murna saboda Allah mai cetona, 48 domin ya tuna da ni, ko da yake ni baiwarsa ce wadda ba kome ba! Daga yanzu dukan mutane za su ce da ni mai albarka, 49 gama Allah Mai Iko ya yi mini abubuwa da yawa! Sunansa mai tsarki ne! 50 Daga tsara zuwa tsara yana jin tausayin waɗanda suke tsoronsa. 51 Da hannunsa mai tsarki ya aikata manyan abubuwa! Ya watsar da masu ɗaga kai da dukan abin da suke takam da shi a zuciyarsu. 52 Ya sauko da sarakuna daga mulkinsu, ya ɗaukaka waɗanda ba kome ba. 53 Ya ba masu yunwa abubuwa masu kyau, ya sallami masu arziki hannu wofi. 54 Ya taimaki bawansa Isra’ila gama ya tuna ya nuna jinƙai ga mutanensa, 55 bisa ga alkawarinsa ga kakanninmu, ga Ibrahim da zuriyarsa har abada!”
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Luka 1:69) Ya ta da Mai Ceto mai iko dominmu daga gidan bawansa Dawuda,
nwtsty na nazarin Lu 1:69
mai Ceto mai iko: A juyin Littafi Mai Tsarki Cikin Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe, an fassara wannan furucin kamar haka: “Ƙahon ceto.” A cikin Littafi Mai Tsarki, akan yi amfani da ƙahon dabba don a ƙwatanta iko ko kuma nasara. (1Sam 2:1; Za 75:4, 5, 10; 148:14) Har ila, ana amfani da ƙaho a wakilci sarakunan da suke da kirki da marasa kirki kuma ana kwatanta nasarar da suka yi da yadda dabba take yin turi da ƙaho. (M.Sh 33:17; Da 7:24; 8:2-10, 20-24) A wannan ayar, furucin nan mai Ceto mai iko ko “ƙahon ceto” yana nufin Almasihu mai ceto wanda yake da ikon ba wa mutane ceto.
(Luka 1:76) Kai kuma ɗan yaron nan, za a ce da kai annabi na Allah Mafi Ɗaukaka. Za ka riga Ubangiji zuwa, domin ka shirya masa hanya,
nwtsty na nazarin Lu 1:76
za ka riga Ubangiji zuwa: Manufar wannan furucin cewa Yohanna zai “riga Ubangiji zuwa” shi ne, Yohanna ne zai zo ya yi shiri kafin zuwan Yesu, wanda zai zo a madadin Ubansa kuma zai zo a cikin sunan Jehobah.—Yoh 5:43; 8:29.
Karatun Littafi Mai Tsarki
(Luka 1:46-66) Maryamu ta ce, “Zuciyata tana yabon Ubangiji. 47 Raina yana murna saboda Allah mai cetona, 48 domin ya tuna da ni, ko da yake ni baiwarsa ce wadda ba kome ba! Daga yanzu dukan mutane za su ce da ni mai albarka, 49 gama Allah Mai Iko ya yi mini abubuwa da yawa! Sunansa mai tsarki ne! 50 Daga tsara zuwa tsara yana jin tausayin waɗanda suke tsoronsa. 51 Da hannunsa mai tsarki ya aikata manyan abubuwa! Ya watsar da masu ɗaga kai da dukan abin da suke takam da shi a zuciyarsu. 52 Ya sauko da sarakuna daga mulkinsu, ya ɗaukaka waɗanda ba kome ba. 53 Ya ba masu yunwa abubuwa masu kyau, ya sallami masu arziki hannu wofi. 54 Ya taimaki bawansa Isra’ila gama ya tuna ya nuna jinƙai ga mutanensa, 55 bisa ga alkawarinsa ga kakanninmu, ga Ibrahim da zuriyarsa har abada!” 56 Maryamu ta zauna da Alisabatu kamar wata uku, sa’an nan ta koma gida. 57 Da kwanakin haifuwarta suka cika, sai Alisabatu ta haifi ɗa. 58 Maƙwabtanta da ’yan’uwanta suka yi murna sosai da suka ji ta haifu, suka taya ta farin ciki saboda wannan albarkar da Ubangiji ya yi mata. 59 Da yaron ya cika kwana takwas, sai suka zo domin su yi masa kaciya. Dā ma sun so ne su sa masa sunan babansa, Zakariya, 60 amma mamar yaron ta ce, “A’a! Za a ce da shi Yohanna.” 61 Sai suka ce, “ ’Wane ne a danginku mai wannan suna?” 62 Sai suka tambayi baban yaron da hannu ya faɗa musu sunan da za a kira yaron da shi. 63 Sai ya sa a kawo masa allo, sai ya rubuta, “Sunansa Yohanna ne.” Sai dukan mutanen da suke wurin suka yi mamaki! 64 Nan take Zakariya ya sami bakin magana kuma, ya fara yabon Allah. 65 Tsoro ya kama dukan maƙwabtansu. Mutane suka ba da labarin abin da ya faru a ko’ina a yankin tuddan Yahudiya. 66 Duka wanda ya ji wannan labarin, sai ya yi ta tunani, yana cewa, “Me yaron nan zai zama?
18-24 GA YUNI
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | LUKA 2-3
“Matasa—Kuna Ƙarfafa Dangantakarku da Jehobah Kuwa?”
(Luka 2:41, 42) Kowace shekara iyayen Yesu sukan je Urushalima don Bikin Ƙetarewa. 42 Da Yesu ya cika shekara goma sha biyu da haifuwa, sai suka je bikin kamar yadda suka saba.
nwtsty na nazarin Lu 2:41
iyayen Yesu sukan je: Dokar ba ta bukaci mata su riƙa zuwa bikin Ƙetarewa ba. Amma Maryamu takan raka mijinta zuwa Urushalima domin wannan bikin. (Fit 23:17; 34:23) A kowace shekara, sukan yi tafiyar kusan kilomita 300 da iyalinsu.
(Luka 2:46, 47) A rana ta uku suka same shi yana zama a cikin Haikali tare da malamai. Yana jinsu, yana kuma yi musu tambayoyi. 47 Dukan waɗanda suka ji shi, suka riƙe baki, suna mamakin ganewarsa da yadda yake ba da amsoshi.
nwtsty na nazarin Lu 2:46, 47
yana kuma yi musu tambayoyi: Yadda masu sauraronsa suka yi mamaki ya nuna cewa tambayoyin da yake yi ya wuce irin tambayoyin da yara suke yi don su gamsu. (Lu 2:47) Kalmar Helenanci da aka fassara zuwa “yin . . . tambayoyi” a wasu mahalli tana iya nufin tambayoyi da ake amfani da su idan ana shari’a a kotu. (Mt 27:11; Mk 14:60, 61; 15:2, 4; A. M. 5:27) ’Yan tarihi sun ce wasu malaman addini sukan zauna a haikalin bayan an gama bikin don su riƙa koyar da mutane a wani ɓangaren haikalin. Mutane sukan zauna a gabansu suna sauraronsu da kuma yi musu tambayoyi.
suna mamaki: Kalmar aikatau ta Helenanci da aka yi amfani da ita don a fassara “mamaki” ta nuna cewa ba sau ɗaya ba ne kawai a ke mamakin amma ci gaba da yin mamakin.
(Luka 2:51, 52) Sai ya tashi ya bi su, suka koma Nazaret tare, inda ya ɗinga biyayya ga iyayensa. Mamarsa kuma ta riƙe dukan waɗannan abubuwa tana tunaninsu a zuciyarta. 52 Yesu ya yi ta ƙaruwa da hikima da tsayi, ya kuma sami farin jini a gaban Allah da kuma a gaban mutane.
nwtsty na nazarin Lu 2:51, 52
ya ɗinga biyayya: Ko kuma “ya ci gaba da biyayya.” Kalmar aikatau da aka yi amfani da ita ta nuna cewa bayan da Yesu ya ba malaman haikalin mamaki don ilimin Kalmar Allah da yake da shi, ya tafi gida tare da iyayensa kuma ya ci gaba da yi musu biyayya. Wannan biyayyar da Yesu ya yi ta fi wadda yara suke yi wa iyayensu. Ya yi hakan ne don Dokar da aka bayar ta hannun Musa ta ce yara su riƙa yin hakan.—Fit 20:12; Ga 4:4.
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Luka 2:14) “Ɗaukaka ga Allah a can cikin sama! A duniya bari salama ta kasance tare da waɗanda Allah yake jin daɗinsu!”
nwtsty na nazarin Lu 2:14
a duniya bari salama ta kasance tare da waɗanda Allah yake jin daɗinsu: Wasu rubuce-rubuce na dā sun fassara wurin cewa “salama a duniya, tagomashi kuma a wurin mutane,” kuma wasu fassarar Littafi Mai Tsarki ma sun faɗi hakan. Amma a yawancin rubuce-rubucen da aka yi a dā, an yi amfani da furucin da juyin New World Translation ya yi amfani da shi. Wannan furucin da mala’ika ya yi ba ya nufin cewa dukan mutane sun sami tagomashin Allah ko da yaya halinsu yake. A maimakon haka, yana nufin waɗanda za su sami tagomashin Allah domin sun ba da gaskiya sosai a gare shi kuma sun zama mabiyan Ɗansa.—Ka duba sakin layi na gaba.
waɗanda Allah yake jin daɗinsu: Za a iya fassara kalmar Helenancin nan eu·do·kiʹa zuwa “tagomashi ko murna ko kuma amincewa.” An yi amfani da makamancin aikatau na kalmar nan eu·do·keʹo a Mt 3:17; Mk 1:11; da kuma Lu 3:22 (ka duba na nazarin Mt 3:17; Mk 1:11), in da Allah ya yi magana game da Ɗansa a lokacin da ya yi baftisma. Kuma hakan yana nufin, “a amince ko a ji daɗi da ko a ɗauka da muhimmanci ko kuma a so.” Don haka, furucin da mala’ikan nan ya yi yana nufin tagomashin Allah ba ga dukan mutane ba, amma ga waɗanda suke biyayya da shi ta wurin bangaskiyarsu kuma sun zama mabiyan Ɗansa. Ko da yake kalmar Helenancin nan eu·do·kiʹa a wasu mahalli suna nufin tagomashin mutane, (Ro 10:1; Fib 1:15), an cika amfani da shi don a nuna tagomashin Allah ko abin da yake so ko kuma yadda yake son a yi wasu abubuwa (Mt 11:26; Lu 10:21; Afi 1:5, 9; Fib 2:13; 2Ta 1:11). A Za 51:18 [50:20, LXX] na juyin Septuagint, an yi amfani kalmar kuma tana nufin ‘yardan rai’ ko jin daɗi da, ko kuma tagomashin Allah.
(Luka 3:23) Lokacin da Yesu ya fara aikinsa na koyarwa, yana da shekara wajen talatin ne a duniya. Mutane sun ɗauke shi a kan shi ɗan Yusuf ne. Yusuf ɗan Heli,
Karatun Littafi Mai Tsarki
(Luka 2:1-20) A kwanakin nan, Kaisar Augustus ya ba da umurni a ƙirga dukan mutanen da suke a ƙarƙashin mulkin Roma. 2 Wannan shi ne ƙirge ta farko wadda aka yi lokacin da Kiriniyus yake mulkin ƙasar Suriya. 3 Dukan mutane suka koma garuruwansu domin a ƙirga su. 4 Yusuf ma ya bar garin Nazaret a cikin Galili ya je garin Betelehem a cikin yankin Yahudiya, wato garin da aka haifi sarki Dawuda ke nan. 5 Ya tafi da Maryamu da aka yi alkawari zai aura, domin a ƙirga su tare. Lokacin nan kuwa tana da ciki. 6 Da suna can Betelehem, sai kwanakin haihuwarta suka yi. 7 Ta haifi ɗanta na fari, ta rufe shi da zanen goyo, ta kuma kwantar da shi a abin da ake ba dabbobi abinci a ciki, domin ba su sami ɗaki a masauki ba. 8 A wannan gefen ƙasar kuwa, akwai waɗansu makiyaya suna kwana a fili, suna lura da dabbobinsu da dare. 9 Ba labari sai ga mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare su, kuma ɗaukakar Allah ta haskaka su. Sai suka ji tsoro sosai. 10 Amma mala’ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro! Gama na zo muku da labari mai daɗi, wanda zai sa dukan mutane su yi farin ciki sosai. 11 A yau ɗin nan, a cikin garin Dawuda, an haifa muku Mai Ceto, Almasihu Ubangiji! 12 Wannan ne zai zama muku alama, za ku samu an naɗe jariri da zane, an kuma kwantar da shi a abin da ake ba dabbobi abinci a ciki.” 13 Ba labari sai ga ƙungiyar mala’iku daga sama sun bayyana tare da mala’ika na farin, suna yabon Allah suna cewa, 14 “Ɗaukaka ga Allah a can cikin sama! A duniya bari salama ta kasance tare da waɗanda Allah yake jin daɗinsu!” 15 Da mala’ikun suka rabu da su suka koma sama, sai makiyayan suka ce wa junansu, “Bari mu je Betelehem mu ga abin nan da ya faru, da Ubangiji ya gaya mana.” 16 Sai suka tafi da sauri, suka ga Maryamu da Yusufu, suka kuma ga yaron yana kwance a abin da ake ba dabbobi abinci a ciki. 17 Da makiyayan suka gan shi sai suka ba da labarin abin da mala’ikan ya faɗa musu a kan yaron. 18 Dukan mutanen da suka ji wannan labari, sai suka yi ta riƙe baki suna mamakin abin da makyayan nan suka ce. 19 Maryamu kuwa ta riƙe dukan waɗannan abubuwa , tana tunaninsu a zuciyarta. 20 Makiyayan kuma suka koma, suna ta yin waƙoƙin yabon Allah, saboda dukan abin da suka ji, suka kuma gani. Kome ya faru kuwa kamar dai yadda mala’ikan ya faɗa musu.
25 GA YUNI–1 GA YULI
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | LUKA 4-5
“Kamar Yesu, Ka Guji Faɗawa Cikin Jarraba”
(Luka 4:1-4) Yesu ya dawo daga Kogin Yodan cike da Ruhu Mai Tsarki. Ruhu kuwa ya iza shi zuwa cikin daji,2 inda Shaiɗan ya gwada shi har kwana arba’in. A ƙarshen wannan lokacin sai yunwa ta kama shi, don bai ci kome ba. 3 Sai Shaiɗan ya ce masa, “Idan kai Ɗan Allah ne, ka umurci wannan dutse ya zama burodi. 4 Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake a cikin Maganar Allah cewa, ‘Ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba.’ ”
(Luka 4:5-8) Daga nan, Shaiɗan ya kai shi wani wuri mai tsayi sosai, ya nuna masa dukan mulkokin duniya a cikin ɗan lokaci. 6 Shaiɗan ya ce masa, “Zan ba ka iko a kan dukan waɗannan da duk ɗaukakarsu, gama dukan waɗannan an ba ni su. Kuma zan iya ba duk wanda nake so in ba shi. 7 Dukan wannan zai zama naka idan dai ka yi mini sujada.” 8 Yesu ya ce masa, “A rubuce yake cewa, “Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta masa!”
(Luka 4:9-12) Sai Shaiɗan ya ɗauke shi zuwa Urushalima, ya kai shi can bisa Haikali, ya ce masa, “Idan kai Ɗan Allah ne, ka yi tsalle daga nan ka faɗi ƙasa. 10 Gama a rubuce yake cikin Maganar Allah cewa, “Zai ba da umarni ga mala’ikunsa game da kai su tsare ka. 11 Za su kuma tare ka da hannuwansu domin kada ka buga ƙafarka a dutse.’ ” 12 Amma Yesu ya ce masa, “A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”
nwtsty hotuna da bidiyo
Saman Haikali
Mai yiwuwa a zahiri ne Shaiɗan ya kai Yesu “bisa [ko kuma “wuri mafi nisa”] a kan haikalin” kuma ya ce masa ya yi tsalle zuwa ƙasa. Amma, Littafi Mai Tsarki bai faɗi daidai wurin da Yesu ya tsaya ba. Tun da yake “haikali” ne kawai ayar ta ambata, zai iya nufin kowane wuri a saman haikalin. Saboda haka, mai yiwuwa Yesu ya tsaya a ta kudu maso gabashin (1) haikalin ne. Ko kuma ya tsaya a wani gefe dabam. Idan mutum ya faɗo daga wurin, ba zai taɓa rayuwa ba sai dai ko Jehobah ya taimaka masa.
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Luka 4:17) Sai ya miƙa masa littafin annabi Ishaya. Ya kwance littafin ya kuma sami wurin da aka rubuta cewa,
nwtsty na nazarin Lu 4:17
littafin annabi Ishaya: Littafin Ishaya da aka samu a tekun gishiri, an yi shi da fata guda 17 da aka haɗa su suka zama littafi ɗaya. Tsayinsa ya kai kafa 24 kuma yana da shafuffuka 54. Mai yiwuwa girman littafin Ishaya da ake amfani da shi a majami’ar Nazarat ya yi daidai da wannan littafin. Tun da yake littafin da ake amfani da shi a ƙarni na farko ba shi da sura da aya, Yesu yana bukatar ya nemi inda yake so ya karanta. Da yake ya iya samun wurin da annabi Ishaya ya yi annabcin, hakan ya nuna cewa yana karanta Kalmar Allah sosai.
(Luka 4:25) Amma gaskiya ina gaya muku, a zamanin annabi Iliya, akwai matan da mazansu suka mutu da yawa a Isra’ila, sa’ad da ruwan sama ya ƙi zuwa har shekara uku da wata shida, aka kuma yi muguwar yunwa ko’ina a ƙasar.
nwtsty na nazarin Lu 4:25
har shekara uku da wata shida: Littafin 1Sa 18:1 ya nuna cewa a “shekara ta uku” ne Iliya ya sanar cewa za a soma ruwan sama. Wasu sun ce abin da Yesu ya faɗa, bai yi daidai da abin da 1Sarakunan ya faɗa ba. Amma littafin 1Sarakunan bai nuna cewa an daina ruwan saman, na ƙasa da shekara uku ba. Furucin nan “a shekara ta uku,” da ayar ta ce yana nufin tun daga lokacin da Iliya ya sanar cewa ba za a sake yin ruwan sama ba. (1Sa 17:1) Kafin Iliya ya yi sanarwar, an yi wata shida ba a yi ruwan sama ba. Har ila, ba a soma yin ruwan sama nan take bayan Iliya ya sake zuwa wurin Ahab “a shekara ta uku ba,” amma sai bayan da aka yi gwaji tsakanin Iliya da annabawan Ba’al a Dutsen Karmel. (1Sa 18:18-45) Saboda haka, abin da Yesu ya faɗa a wannan ayar da wanda ɗan’uwansa ya faɗa a littafin Yaƙ 5:17, ya jitu da abin da ke littafin 1Sa 18:1.
Karatun Littafi Mai Tsarki
(Luka 4:31-44) Sai ya tafi Kafarnahum, wani gari a cikin Galili. A nan ya shiga majami’a a Ranar Hutu ta Mako yana koyar da su. 32 Suka yi ta mamakin koyarwarsa, domin maganarsa tana da iko 33 A cikin majami’ar, akwai wani mutum mai ƙazamin ruhu. Sai ya ta da murya da ƙarfi ya ce, 34 “Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu mutumin Nazaret? Ko ka zo ne ka halaka mu? Na san wane ne kai, kai ne Mai Tsarkin nan na Allah!” 35 Yesu ya tsawata wa aljanin ya ce, “Ka yi shiru, ka fita daga jikin mutumin nan!” Sai aljanin ya ɗaga mutumin ya buga shi a ƙasa a gabansu, sa’an nan ya fita, ya bar mutumin ba wani ciwo. 36 Sai dukan mutane suka kama baki kawai, suna ce wa junansu, “Wane irin abu ne haka? Da ƙarfi da iko wannan mutum ya umurci ƙazaman ruhohi har sun fita!” 37 Wannan abin da Yesu ya yi, ya sa an baza labarinsa ko’ina a ƙasar. 38 Yesu ya fita daga majami’ar ya tafi gidan Siman. Mamar matar Siman kuma ba ta da lafiya, zazzaɓi ya dame ta sosai. Suka roƙi Yesu ya warkar da ita. 39 Ya je ya tsaya kusa da gadonta ya umurci zazzaɓin ya bar ta. Nan take zazzaɓin ya bar ta, ta kuma tashi ta yi musu hidima. 40 Da rana ta faɗi, kowa da yake da aboki mai rashin lafiya da kowane irin ciwo, suka kawo su wurin Yesu. Shi kuma ya taɓa kowannensu da hannu ya warkar da su duka. 41 Aljannu kuma suka fita daga jikin mutane da yawa suna ihu suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne!” Amma Yesu ya tsawata musu, ya hana su magana, saboda sun san cewa shi ne Almasihu. 42 Da gari ya waye sai Yesu ya bar garin ya je inda ba kowa. Mutane suka yi ta nemansa har suka same shi. Suka yi ƙoƙari su hana shi zuwa wani wuri kuma. 43 amma ya ce musu, “Ya kamata in kai labari mai daɗi na mulkin Allah ga waɗansu garuruwa, gama saboda wannan dalilin ne aka aiko ni.”