Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • th darasi na 4 p. 7
  • Ka Gabatar da Nassi Yadda Ya Dace

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Gabatar da Nassi Yadda Ya Dace
  • Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Bayyana Nassin da Ka Karanta
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Gabatarwa Mai Dadi
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Maganarka ta Ratsa Zuciya
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Mutane Su Koyi Darasi Daga Jawabin
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
Dubi Ƙari
Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
th darasi na 4 p. 7

DARASI NA 4

Ka Gabatar da Nassi Yadda Ya Dace

Nassin da aka rubuta

Matiyu 22:​41-45

ABIN DA ZA KA YI: Ka sa masu sauraronka su yi marmarin nassin da kake so ka karanta kafin ka karanta shi.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka yi tunani a kan dalilin da ya sa kake so ka karanta nassin. Ka gabatar da nassin a hanyar da za ta sa masu sauraronka su ga bayanin da kake so ka fitar daga nassin.

    Shawara mai amfani

    Ka san labarin da kyau. Idan ka ambata wani nassi ko kuma sunan wanda yake magana ko wanda ya rubuta littafin, ka tabbata cewa abin da ka faɗa daidai ne.

  • Ka yi amfani da Littafi Mai Tsarki. Idan kana magana da mutanen da suka yi imani da Allah, ka nuna musu cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ce. Ta hakan, kana nuna cewa abin da kake koyarwa ba naka ba ne, amma na Allah ne.

  • Ka ja hankalin masu sauraronka ga nassin. Ka yi wata tambayar da za a sami amsar a nassin, ka ambata wata matsala da nassin zai bayyana yadda za a warware ta ko kuma ka faɗi wata ƙa’idar da ke nassin.

    Shawara mai amfani

    Ka yi la’akari da abin da masu sauraronka suka sani game da batun da kuma nassin. Ka gabatar da batun da masu sauraronka suka riga suka sani a hanya mai kyau don su fahimce shi a wata hanya dabam.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba