Littattafan da Aka Ɗauko Bayanai Daga Cikinsu a Littafin Taro don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu
3-9 GA MAYU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | LITTAFIN ƘIDAYA 27-29
“Ku Yi Koyi da Halin Rashin Son Kai na Jehobah”
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
it-2 528 sakin layi na 5
Hadaya
Hadaya ta abin sha. Ana ba da hadaya ta abin sha tare da sauran hadayun da ake bayarwa, musamman ma bayan da Isra’ilawa suka soma zama a Ƙasar Alkawari. (L.Ƙi 15:2, 5, 8-10) Hadayar ta ƙunshi ruwan inabi (abin sha mai sa buguwa) da ake zubawa a kan bagadi. (L.Ƙi 28:7, 14; ka kuma duba Fit 30:9; L.Ƙi 15:10.) Manzo Bulus ya rubuta wa Kiristoci da ke Filibi cewa: “Ko da an zub da ni kamar hadaya ta abin sha a hidima mai tsarki wadda kuke yi saboda bangaskiyarku, na yi murna.” A ayar nan, ya yi kwatanci da abin sha don ya nuna yadda ya ba da kansa a madadin Kiristoci. (Fib 2:17, New World Translation) Jim kaɗan kafin ya mutu, ya rubuta wa Timoti cewa: “An riga an fara zubar da raina kamar hadaya ta abin sha a bagade, kuma lokacin da zan bar wannan rayuwa ya yi.”—2Ti 4:6.
10-16 GA MAYU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | LITTAFIN ƘIDAYA 30-31
“Ku Cika Alkawarin da Kuka Yi”
it-2 1162
Wa’adi
Da Yardan Rai, Amma da Zarar An Yi Sai An Cika Shi. Mutum yakan yi alkawarin yin wani abu da yardan ransa. Amma dokar Allah ta ce da zarar mutum ya ɗauki alkawarin yin wani abu, dole sai ya cika alkawarin. Idan mutum ya yi alkawarin yin wani abu, kamar ya ‘ɗaure’ kansa ne. Kuma idan ya kāsa cika alkawarin, hakan zai iya shafan ransa. (L.Ƙi 30:2; ka kuma duba Ro 1:31, 32.) Da yake yin alkawari zai iya shafan ran mutum, shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya shawarce mu mu yi tunani sosai a kan haɗarurrukan da ke tattare da rashin cika alkawari kafin mu ɗau alkawari. Dokar ta ce: “Idan fa kuka yi wa Yahweh Allahnku rantsuwa, . . . Yahweh Allahnku lallai zai neme shi daga gare ku. Rashin cikawa zai jawo muku zunubi. Amma idan ba ku yi wata rantsuwa ba, ba zai jawo muku zunubi ba.”—M.Sh 23:21, 22.
it-2 1162
Wa’adi
Alkawari ne da muke yi wa Allah cewa za mu yi wani abu ko yi hadaya ko ba da wata kyauta ko yin wata hidima ko kuma guje ma wasu abubuwa da doka ba ta haramta su ba. Da yardan rai akan yi wa’adi ko alkawarin yin wani abu. Wa’adi babban alkawari ne da ake haɗawa da rantsuwa, shi ya sa a wasu lokuta Littafi Mai Tsarki yake amfani da waɗannan furuci biyun wajen kwatanta abu ɗaya. (L.Ƙi 30:2; Mt 5:33) Wa’adi alkawarin yin wani abu ne da akan yi, “rantsuwa” kuma akan yi ta ne ga masu iko don a goyi bayan wani batu ko kuma a tabbatar da cewa wani batu gaskiya ne. Sau da yawa akan yi rantsuwa don a tabbatar da wata yarjejeniya da aka yi.—Fa 26:28; 31:44, 53.
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
it-2 28 sakin layi na 1
Yefta
Akan iya ba da mutane su yi hidima a mazaunin Jehobah muddin rayuwarsu. Iyaye ma suna da ikon ba da ’ya’yansu. Abin da ya faru da Sama’ila ke nan. Mahaifiyarsa ta yi alkawarin cewa idan ta haife shi, zai yi hidima a haikali muddin rayuwarsa. Kuma maigidanta Elkanah ya goyi bayan alkawarin da ta yi. Shi ya sa a lokacin da Hannatu ta yaye Sama’ila, ta kai shi ya yi hidima a mazauni. Kuma ta kai abubuwan da za ta yi hadaya da su. (1Sam 1:11, 22-28; 2:11) Haka ma ya faru da Samson, an keɓe shi ya yi hidimar Ba-nazari.—Alƙ 13:2-5, 11-14; ka kuma duba ikon da uba yake da shi a kan ’yarsa kamar yadda aka nuna a L.Ƙi 30:3-5, 16.
17-23 GA MAYU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | LITTAFIN ƘIDAYA 32-33
“Ku Kori Dukan Mazaunan Ƙasar”
Ka Sani?
Mene ne “kan tuddai” da ake yawan ambatawa a Nassosin Ibrananci?
Sa’ad da Isra’ilawa suke gab da shiga Ƙasar Alkawari, Jehobah ya gaya musu cewa su kawar da dukan wuraren bauta na Kan’aniyawa da suke zama a wurin. Allah ya gaya musu cewa: “Ku rurrushe duwatsunsu waɗanda suka sassaƙa, da siffofin zunubinsu, da wuraren sujadarsu a kan tuddai.” (Littafin Ƙidaya 33:52) Mai yiwuwa wuraren bautar allolin ƙarya nan suna kan duwatsu ko kuma wani waje da aka gina a ƙarƙashin bishiyoyi ko birane. (1 Sarakuna 14:23; 2 Sarakuna 17:29; Ezekiyel 6:3) A wurin, akwai bagadai da duwatsun ibada da gumaka da bagaden turare da dai sauran abubuwan bautar ƙarya.
it-1 404 sakin layi na 2
Kan’ana
Joshua da basira bai ƙi gaya wa Isra’ilawa “dukan abin da Yahweh ya umarci Musa” game da halakar mutanen Kan’ana ba. (Yos 11:15) Amma Isra’ilawan sun ƙi bin ja-gorancinsa kuma suka ƙi halaka abubuwan da ke lalata ƙasar. Ko da yake sun bar Kan’aniyawan su kasance a tsakaninsu, mutanen sun ɓata halayen Isra’ilawan kuma da shigewar lokaci, Isra’ilawa da yawa sun rasa rayukansu (ban da yawan ta’addanci da lalata da kuma bautar gumaka). Rashin biyayya da Isra’ilawan suka yi, ya sa da yawa daga cikinsu sun rasa rayukansu fiye da yawan Kan’aniyawa da aka ce su kawar. (L.Ƙi 33:55, 56; Alƙ 2:1-3, 11-23; Za 106:34-43) Jehobah ya gaya wa Isra’ilawan cewa ba zai yi son kai a shari’arsa da kuma hukuncinsa ba. Kuma idan Isra’ilawan suka soma cuɗanya da Kan’aniyawan da aurayya da su da bauta ma allolinsu da bin al’adun addininsu da kuma yin wasu munanan abubuwa, hakan zai sa su jawo wa kansu irin halakar da za a yi wa Kan’aniyawan kuma ‘ƙasar za ta amayar da su.’—Fit 23:32, 33; 34:12-17; L.Fi 18:26-30; M.Sh 7:2-5, 25, 26.
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
it-1 359 sakin layi na 2
Iyaka
Bayan ƙuri’ar ta nuna filin da za a ba ma wata ƙabila, sai a bincika a ga ko filin ya yi babba ko kuma ƙarami. Littafi Mai Tsarki ya ce, “Za ku rarraba wa kanku gādon ƙasar bisa ga dangi-dangi ta hanyar jefa ƙuri’a. Za ku ba babban dangi babban rabo, ƙaramin dangi kuma ku ba ta ƙaramin rabo. Duk inda ƙuri’a ta yanka wa mutum, wurin ne zai zama gādonsa.” (L.Ƙi 33:54) Ba za a canja inda ƙuri’ar ta ce filin zai kasance ba, amma za a iya ƙara ko rage girman filin bisa ga yawan ƙabilar. Shi ya sa sa’ad da aka lura cewa filin da aka ba wa zuriyar Yahuda yana da girma sosai, an yanka wani gefe kuma aka ba wa zuriyar Simeyon.—Yos 19:9.
24-30 GA MAYU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | LITTAFIN ƘIDAYA 34-36
“Ku Mai da Jehobah Mafakarku”
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
w91 2/15 13 sakin layi na 13
Fansa Daidaitaciya Domin Mutane Duka
13 Adamu da Hauwa’u ba za su amfana daga fansar ba. A Dokar da aka ba da ta hannun Musa, an faɗi cewa: “Kada ku karɓi abin fansa domin rai na mai kisan kai, wanda kuma an riga an yanka masa hukuncin mutuwa.” (Littafin Ƙidaya 35:31) Tun da ba a yaudari Adamu ba, zunubin da ya yi, ya yi shi ne da saninsa kuma da gangan. (1 Timoti 2:14) Hakan ya sa ’ya’yansa mutuwa domin sun gāji zunubinsa kuma suka zama bayi ga mutuwa. Babu shakka, Adamu ya cancanci ya mutu domin shi kamiltaccen mutum ne amma ya zaɓi ya yi wa Allah rashin biyayya. Idan Allah ya bar Adamu ya amfana daga tanadin fansar, hakan zai saɓa wa ƙa’idodinsa masu adalci. Idan ana so a ba da fansa don zunubin Adamu, wajibi ne a tanadar da wadda za ta iya kawar da sakamakon mutuwa da zunubin Adamu ya jawo wa ’ya’yansa. (Romawa 5:16) Ta wajen fansa da Jehobah ya tanadar, Jehobah ya kawar da munanan sakamakon zunubi daga tushensa. Wajibi ne wanda zai ba da fansar ‘ya mutu saboda kowane’ mutum kuma ya ɗauki sakamakon zunubi wanda dukan ’ya’yan Adamu suke da shi.—Ibraniyawa 2:9; 2 Korintiyawa 5:21; 1 Bitrus 2:24.
31 GA MAYU–6 GA YUNI
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MAIMAITAWAR SHARI’A 1-2
“Shari’a ta Allah Ce”
w96 3/15 23 sakin layi na 1
Jehobah Yana Son Adalci da Gaskiya
An bukaci dattawa da aka naɗa a ikilisiya su shar’anta waɗanda suka yi zunubi mai tsanani. (1 Korintiyawa 5:12, 13) Sa’ad da suke yin hakan, su tuna cewa a duk lokacin da Allah yake yanke hukunci, yakan nuna jin kai idan da bukata. Amma waɗanda suka yi zunubi kuma suka ƙi tuba, ba a bukata a nuna musu jin kai. Kuma bai kamata dattawa su yi wa mutum yankan zumunci cikin fushi ko don ramako ba. Me ya sa? Domin begensu shi ne mai zunubin ya dawo hankalinsa kuma ya soma bauta wa Jehobah. (Ka kuma duba Ezekiyel 18:23.) Da yake dattawa suna bin ja-gorancin shugabansu Yesu Kristi, suna yin adalci kuma hakan ya ƙunshi zama kamar wurin “mafaka daga iska.” (Ishaya 32:1, 2) Saboda haka, bai kamata su yi son kai ba, amma su nuna sanin ya kamata.—Maimaitawar Shari’a 1:16, 17.
7-13 GA YUNI
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MAIMAITAWAR SHARI’A 3-4
“Dokokin Jehobah Masu Adalci Ne Kuma Akwai Hikima a Cikinsu”
it-2 1140 sakin layi na 5
Fahimi
Idan mutum yana ƙwazo a nazarin Kalmar Allah kuma yana yin amfani da abin da yake koya, hakan zai sa shi ya fi malamansa ilimi kuma ya zama da fahimi fiye da waɗanda suka fi shi shekaru. (Za 119:99, 100, 130; ka kuma duba Lu 2:46, 47.) Dalilin kuma shi ne hikima da fahimi suna cikin Kalmar Allah. Kuma idan Isra’ilawa sun bi dokar Allah sau da kafa, al’ummai da suke kewaye da su za su san cewa su “mutane ne masu hikima da ganewa!” (M.Sh 4:5-8; Za 111:7, 8, 10; ka kuma duba 1Sar 2:3.) Mutum mai fahimi ya san cewa Kalmar Allah ba ta cutar da mutum kuma yana ƙoƙari ya ga yadda Kalmar Allah ta shafe shi sa’an nan ya yi addu’a ga Allah ya taimaka masa ya yi amfani da abin da ya karanta. (Za 119:169) Yana barin Kalmar Allah ta shiga zuciyarsa (Mt 13:19-23), ya kuma rubuta ta a allon zuciyarsa (K. Ma 3:3-6; 7:1-4), bayan haka, sai ya “ƙi kowace hanyar rashin gaskiya” (Za 119:104). Sa’ad da Ɗan Allah yake duniya, ya nuna irin wannan fahimin kuma ya ƙi ya guji mutuwa don ya san cewa idan bai mutu a wannan hanyar ba, annabcin da aka yi ba zai cika ba.—Mt 26:51-54.
w99 11/1 20 sakin layi na 6-7
Amfanin Nuna Karimci
Sarauniyar Sheba ta yi mamaki sosai da abin da ta gani da kuma ji, sai ta ce: “Lallai mutanenka da masu yi maka hidima sun yi sa’a, saboda ta dalilin aikinsu a nan kullum suna jin hikimarka!” (1 Sarakuna 10:4-8) Sarauniyar ba ta ce bayin Sulemanu sun yi sa’a don wadatar da ta kewaye su ba, amma ta ce sun yi sa’a don a kullum suna jin hikimar Allah ta bakin Sulemanu. Sarauniyar ta nuna hali mai kyau da bayin Jehobah za su iya koya na bincika hikimar Mahalicci da kuma na Ɗansa Yesu Kristi!
Ban da haka ma, sarauniyar ta sake gaya wa Sulemanu cewa: “Albarka ta tabbata ga Yahweh Allahnka.” (1 Sarakuna 10:9) Babu shakka, ta gane cewa Allah ne ya ba Sulemanu hikima da wadata. Hakan ya jitu da abin da Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa da farko cewa: “Ku kiyaye ku kuma aikata [maganata], gama yin haka zai nuna hikimarku da ganewarku ga sauran kabilu, waɗanda in sun ji game da dukan waɗannan ƙa’idodi, za su ce, ‘Lailai, wannan babbar al’ummar mutane ne masu hikima da ganewa!’ ”—Maimaitawar Shari’a 4:5-7.
14-20 GA YUNI
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MAIMAITAWAR SHARI’A 5-6
“Ku Koyar da Yaranku Yadda Za Su Ƙaunaci Jehobah”
w07 5/15 15-16
Ta Yaya Zan Koyar da Yarana Su Kasance da Ilimin Gaske?
Abubuwan da kake faɗa da kuma yi sukan nuna muradinka da ra’ayi da kuma abubuwan da kake so. (Romawa 2:21, 22) Yara suna lura da abubuwan da iyayensu suke yi kuma su koye su tun suna jarirai. Idan suka lura da abubuwan da suka fi kwanta ma iyayensu a rai, su ma idan suka girma abubuwan ne za su riƙa kwanta musu a rai. Idan iyaye suna ƙaunar Jehobah da gaske, yaran za su gane hakan. Alal misali, idan suka lura cewa kana karanta Littafi Mai Tsarki kullum kuma kana bincike, za su fahimci cewa kana saka Mulkin Allah farko a rayuwarka. (Matiyu 6:33) Ban da haka ma, idan suka lura cewa kana halartan taro kuma kana zuwa wa’azi a kullum, hakan zai nuna musu cewa ibada ce ta fi maka muhimmanci a rayuwa.—Matiyu 28:19, 20; Ibraniyawa 10:24, 25.
28 GA YUNI–4 GA YULI
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MAIMAITAWAR SHARI’A 9-10
“Mene ne Yahweh Allahnku Yake So a Gare Ku?”
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
it-1 103
‘Ya’yan Anak
Wata kabilar kattan mutane ne da suke zama a Kan’ana da kuma wasu wurare a kudancin ƙasar. Akwai wani lokaci da ’ya’yan Anak masu suna Ahiman da Sheshai da kuma Talmai suka yi zama a Hebron. (L.Ƙi 13:22) A wurin ne ’yan leƙen asirin nan guda 12 suka fara ganin su kuma goma daga cikinsu suka ba da rahoto na ban tsoro game da su cewa, su kattai ne kamar Nephilim da suka yi rayuwa kafin ambaliyar ruwa da ta hallaka zamanin Nuhu. Kuma sun ƙara da cewa Isra’ilawa za su zama kamar “fara” ne kawai a gabansu. (L.Ƙi 13:28-33; M.Sh 1:28) Ana amfani da su wajen kwatanta kattan mutanen Emim da Raphaim don yadda jikinsu yake. Irin ƙarfin da suke da shi ne ya sa ake ƙarin maganar nan: “Wane ne zai iya tsayawa ya fuskanci ’ya’yan Anak?”—M.Sh 2:10, 11, 20, 21; 9:1-3.