Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • th darasi na 10 p. 13
  • Muryar da Ta Dace

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Muryar da Ta Dace
  • Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi Magana da Kuzari
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Ka Yi Magana Ba Shakka
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Ka Yi Kamar Kuna Tattaunawa
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Maganarka ta Ratsa Zuciya
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
Dubi Ƙari
Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
th darasi na 10 p. 13

DARASI NA 10

Muryar da Ta Dace

Nassin da aka rubuta

Karin Magana 8:​4, 7

ABIN DA ZA KA YI: Don saƙon ya taɓa zuciyar masu sauraro, ka riƙa canja murya, kana iya ɗaga murya, rage murya, ƙara sauri ko rage sauri.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Muryarka ta yi daidai da abin da kake faɗa. Ka ɗaga muryarka sa’ad da kake nanata muhimman darussa ko ƙarfafa masu sauraro su yi wani abu. Ka yi hakan yayin da kake karanta hukuncin da ke Littafi Mai Tsarki. Ka sauƙe muryarka sa’ad da kake magana a kan abin ban tsoro ko damuwa.

    Shawara mai amfani

    Kada ka ɗaga murya a kai a kai don kar masu sauraronka su ɗauka kana yi musu faɗa. Kada yadda kake magana ya janye hankalin masu sauraronka daga abin da kake faɗa.

  • Ka riƙa canja murya. Yayin da kake magana a kan abu mai ban sha’awa ko kana so ka kwatanta girman wani abu ko kuma nisan wani wuri, ka ɗaga murya. Yayin da kuma kake bayyana abin baƙin ciki ko wata matsala, muryarka ta nuna hakan.

  • Ka yi magana da sauri ko kuma a hankali. Ka yi magana da sauri don ka nuna farin cikinka. Yayin da kuma kake bayyana muhimman darussa, ka yi hakan a hankali.

    Shawara mai amfani

    Don kada masu sauraronka su riƙice, kada ka riƙa canja muryarka cikin hanzari. Kada ka yi magana da sauri sosai don hakan zai hana su fahimtar abin da kake cewa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba