Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lffi darasi na 1
  • Ta Yaya Littafi Mai Tsarki Zai Inganta Rayuwarka?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta Yaya Littafi Mai Tsarki Zai Inganta Rayuwarka?
  • Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Gabatarwar Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA YI BINCIKE SOSAI
  • TAƘAITAWA
  • KA BINCIKA
  • Ta Yaya Littafi Mai Tsarki Zai Inganta Rayuwarka?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Gabatarwar Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Yadda Za Ka Amfana Daga Karanta Littafi Mai Tsarki
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Me Zai Taimaka Maka Ka Ci Gaba da Nazarin Kalmar Allah?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Littafi Mai Tsarki Ya Ce Za Mu Ji Dadin Rayuwa
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Gabatarwar Nazarin Littafi Mai Tsarki
lffi darasi na 1
Darasi na 1. Littafi Mai Tsarki da ke a bude.

DARASI NA 01

Ta Yaya Littafi Mai Tsarki Zai Inganta Rayuwarka?

Hoto
Hoto
Hoto

Kusan dukanmu muna son mu san dalilin da ya sa aka halicce mu da dalilin da ya sa muke wahala da mutuwa da kuma abin da zai faru a nan gaba. Muna kuma damuwa game da yadda za mu biya bukatunmu da yadda iyalinmu za ta zauna lafiya. Littafi Mai Tsarki ya taimaka wa mutane da yawa su sami amsoshin muhimman tambayoyi game da rayuwa. Yana kuma ɗauke da shawarwari masu kyau game da harkokinmu na yau da kullum. Kana ganin Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka wa dukanmu kuwa?

1. Waɗanne tambayoyi ne za mu iya samun amsoshinsu a Littafi Mai Tsarki?

Za mu iya samun amsoshin muhimman tambayoyin nan a Littafi Mai Tsarki: Ta yaya muka soma wanzuwa? Me ya sa aka halicce mu? Me ya sa mutane suke shan wahala? Me ke faruwa da mutum sa’ad da ya mutu? Idan kowa yana son zaman lafiya, me ya sa ake yaƙe-yaƙe a ko’ina? Me zai faru da duniya a nan gaba? Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu nemi amsoshin tambayoyin nan, kuma miliyoyin mutane sun sami amsoshi masu gamsarwa.

2. Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu ji daɗin rayuwa kullum?

Muna samun shawarwari masu kyau a Littafi Mai Tsarki. Alal misali, yadda iyalinmu za ta riƙa farin ciki da yadda za mu magance matsaloli da kuma yadda za mu ji daɗin aikinmu. Yayin da muke tattauna littafin nan tare, za ka ga abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Kuma za ka ga cewa dukan Nassosi, wato dukan abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki, yana “da amfani.”​—2 Timoti 3:16.

Wannan littafin bai sauya Littafi Mai Tsarki ba. Maimakon haka, zai taimaka maka ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kanka. Saboda haka, muna ƙarfafa ka ka karanta nassosin da ke kowane darasi kuma ka ga ko sun yi daidai da abubuwan da kake koya.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yadda Littafi Mai Tsarki ya taimaka wa mutane da yadda za ka ji daɗin karanta shi da kuma abin da ya sa ya dace ka nemi taimako don ka fahimce shi.

3. Littafi Mai Tsarki zai iya yi mana ja-goranci

Littafi Mai Tsarki yana kama da fitila mai haske sosai. Zai iya taimaka mana mu ga yadda za mu yanke shawarwari masu kyau kuma mu san abin da zai faru a nan gaba.

Ku karanta Zabura 119:​105, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Mene ne ra’ayin marubucin wannan zabura game da Littafi Mai Tsarki?

  • Mene ne ra’ayinka game da Littafi Mai Tsarki?

Wani mutum yana tafiya a bakin kogi da dare kuma yana rike da tocila.

4. Za mu iya samun amsoshin tambayoyinmu a cikin Littafi Mai Tsarki

Wata mata ta sami amsoshin tambayoyin da ta yi shekaru tana tunani a kai. Ta sami amsoshin a cikin Littafi Mai Tsarki. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

BIDIYO: Kar Ka Gaji da Jira! (1:48)

  • Waɗanne tambayoyi ne matar ta yi a bidiyon?

  • Ta yaya yin nazarin Littafi Mai Tsarki ya taimaka mata?

Littafi Mai Tsarki ya ce mu riƙa yin tambayoyi. Ku karanta Matiyu 7:​7, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Waɗanne tambayoyi ne za ka iya samun amsoshinsu a cikin Littafi Mai Tsarki?

5. Za ka ji daɗin karanta Littafi Mai Tsarki

Mutane da yawa suna jin daɗin karanta Littafi Mai Tsarki kuma suna amfana daga abin da suke karantawa. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

BIDIYO: Karatun Littafi Mai Tsarki (2:05)

  • Kamar yadda aka nuna a bidiyon, mene ne matasan suka ce game da yin karatu?

  • Me ya sa suke son karanta Littafi Mai Tsarki?

A cikin Littafi Mai Tsarki, za mu iya samun umurnin da zai ƙarfafa begenmu a kan abubuwa da za su faru a nan gaba. Ku karanta Romawa 15:​4, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Za ka so ka sami ƙarin bayani game da alkawarin da ke ayar nan?

6. Za a iya taimaka mana mu fahimci Littafi Mai Tsarki

Zai dace mu riƙa karanta Littafi Mai Tsarki da kanmu. Ƙari ga haka, mutane da yawa sun lura cewa tattauna shi da wasu yana da ban-taimako. Ku karanta Ayyukan Manzanni 8:​26-31, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Mene ne zai taimaka mana mu fahimci Littafi Mai Tsarki?​—Ka duba ayoyi 30 da 31.

Hotuna: 1. Filibus yana bayyana wa Bahabashen Nassosi. 2. Wata Mashaidiya tana tattauna Littafi Mai Tsarki da wata mata da kuma yaranta biyu.

Bahabashen ya nemi taimako don ya fahimci Nassosi. Mutane da yawa a yau suna amfana idan wani ya tattauna Littafi Mai Tsarki da su

WASU SUN CE: “Karanta Littafi Mai Tsarki ɓata lokaci ne.”

  • Mene ne ra’ayinka? Me ya sa?

TAƘAITAWA

A cikin Littafi Mai Tsarki, za mu iya samun ƙarfafawa da amsoshin tambayoyi masu muhimmanci da kuma shawarwari masu kyau da za su taimaka mana kullum. Kuma za mu iya sanin abubuwa masu kyau da za su faru a nan gaba.

Bita

  • Waɗanne shawarwari ne za mu iya samu a Littafi Mai Tsarki?

  • Waɗanne tambayoyi ne za mu iya samun amsoshinsu a cikin Littafi Mai Tsarki?

  • Mene ne za ka so ka koya a Littafi Mai Tsarki?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku koyi yadda Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana a yau.

“Koyarwar Littafi Mai Tsarki Tana da Amfani a Koyaushe” (Hasumiyar Tsaro Na 1 2018)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda Littafi Mai Tsarki ya taimaka wa wani mutum wanda ya yi fama tun yana yaro.

Yadda Na Soma Yin Farin Ciki a Rayuwa (2:53)

Ku karanta talifin nan don ku ga wasu shawarwari masu kyau da Littafi Mai Tsarki yake ɗauke da su don iyalai.

“Abubuwa 12 da Za Su Sa Iyalai Zaman Lafiya” (Awake! Na 2 2018)

Ku kalli bidiyon nan don ku koyi gaskiya da ke cikin Littafi Mai Tsarki game da ainihin wanda yake mulkin duniya.

Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki?​—Cikakken Bidiyon (3:14)

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba