Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 8/15 pp. 6-10
  • Mene ne Matsayin Mata a Tsarin Jehobah?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mene ne Matsayin Mata a Tsarin Jehobah?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • SAKAMAKON TAWAYE
  • WASU MATA DA JEHOBAH YA GOYA MUSU BAYA
  • MATA MASU TSORON ALLAH A ƘARNI NA FARKO
  • ‘BABBAR RUNDUNAR’ MATA
  • ALLAH ZAI ALBARKACI MATA MASU TSORONSA
  • Shin Allah Ya Damu da Mata Kuwa da Gaske?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Mata Suna da Mutunci A Gaban Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Mata, Me Ya Sa Za Ku Miƙa Kai Ga Shugabanci?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Mata Da Suka Faranta Wa Jehovah Rai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 8/15 pp. 6-10

Mene ne Matsayin Mata a Tsarin Jehobah?

‘Mata masu-shelar bisharar kuwa babbar runduna ne.’—ZAB. 68:11.

MECE CE AMSARKA?

  • Wane sakamako ne tawayen da aka yi a lambun Adnin ya jawo wa maza da mata?

  • Ta yaya mata suka bauta wa Jehobah a zamanin dā?

  • Mene ne mata suke yi yau don a yaɗa bishara?

1, 2. (a) Wace kyauta ce Allah ya ba Adamu? (b) Me ya sa Allah ya ba wa Adamu mata? (Ka duba hoton da ke shafi na 6.)

AKWAI dalilin da ya sa Jehobah ya halicci duniya. “Ya halicce ta . . . domin wurin zama.” (Isha. 45:18) Adamu ne mutumin da Allah ya fara halitta kuma shi kamiltacce ne. Jehobah ya saka shi cikin lambun Adnin, wato wani kyakkyawan lambu mai itatuwa da yawa da dabbobi masu kyau. Amma akwai wani abu mai muhimmanci sosai da Adamu bai da shi. Jehobah ya san da hakan shi ya sa ya ce: “Ba ya yi kyau ba mutum shi kasance shi ɗaya; sai in yi masa mataimaki mai-dacewa da shi.” Allah ya sa barci mai nauyi ya kwashi Adamu, sai ya cire haƙarƙarinsa ɗaya kuma ya “maishe shi mace.” Sa’ad da Adamu ya tashi daga barci, ya yi farin ciki da ya ga matarsa kuma ya ce: “Wannan yanzu ƙashi ne daga ƙasusuwana, nama ne daga namana: za a ce da ita Mace, domin daga cikin Namiji aka ciro ta.”—Far. 2:18-23.

2 Mace kyauta ta musamman ce da Allah ya ba Adamu don ita mai taimako ce da ta dace da shi. Ƙari ga haka, Allah ya ba ta gatan haifan ’ya’ya, shi ya sa Adamu ya ‘kira sunan matatasa Hawwa’u; domin ita ce uwar masu-rai duka.’ (Far. 3:20) Hakika, babban gata ne Allah ya ba Adamu da Hawwa’u! Wannan gatan zai ba su damar haifan yara kamiltattu. Ta hakan, duniya za ta zama aljanna da za ta cika da kamiltattun mutane da za su kula da sauran halittun da ke cikinta.—Far. 1:27, 28.

3. (a) Mene ne Adamu da Hawwa’u suke bukata su yi don Allah ya albarkace su, amma mene ne ya faru? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

3 Adamu da Hawwa’u suna bukata su bi umurnin Jehobah kuma su amince da sarautarsa don ya albarkace su. (Far. 2:15-17) Za su iya cika nufin Allah a gare su ne kawai idan suka kasance da aminci ga Allah. Abin baƙin ciki, wani “babban maciji,” wato Shaiɗan ya rinjaye su kuma suka yi zunubi. (R. Yoh. 12:9; Far. 3:1-6) Ta yaya wannan tawayen ya shafi mata? Mene ne mata masu tsoron Allah suka cim ma a dā? Me ya sa za mu iya ce Kiristoci mata na zamaninmu ‘babbar runduna’ ce?—Zab. 68:11.

SAKAMAKON TAWAYE

4. Wane ne ke da alhakin zunubin da Adamu da Hawwa’u suka yi?

4 Sa’ad da Jehobah ya tambayi Adamu dalilin da ya sa ya yi tawaye, ya ba da hujja da ba ta taka kara ta ƙarya ba. Ya ce: “Macen da ka ba ni domin ta zauna tare da ni, ita ta ba ni daga itacen, ni kuwa na ci.” (Far. 3:12) Adamu bai yarda cewa zunubin da ya yi laifinsa ba ne, maimakon haka, ya yi ƙoƙarin ɗora wa matarsa da kuma Jehobah laifi. Adamu da Hawwa’u sun yi zunubi, amma Adamu ne ke da alhakin zunubin da suka yi. Shi ya sa manzo Bulus ya ce: ‘Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya [Adamu], mutuwa kuwa ta wurin zunubi.’—Rom. 5:12.

5. Mene ne sakamakon sarautar ’yan Adam?

5 Shaiɗan ya yaudari ma’aurata na farko kuma suka ɗauka cewa ba sa bukatar sarautar Jehobah. Hakan ya ta da wata muhimmiyar tambaya: Wane ne ya dace ya yi sarauta bisa ’yan Adam? Jehobah ya bari ’yan Adam su mulki kansu na ɗan lokaci domin hakan zai ba da amsa da za ta gamshi kowa. Mene ne sakamakon haka? Ƙarnukan da suka shige sun nuna cewa mulkin ’yan Adam ya haddasa matsaloli dabam-dabam. A ƙarnin da ya wuce kaɗai, mutane wajen miliyan ɗari sun rasa rayukansu sanadiyyar yaƙe-yaƙe. Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutum kuwa ba shi da iko shi shirya tafiyarsa.” (Irm. 10:23) Shi ya sa Kiristoci na gaske sun amince Jehobah ya yi sarauta a kansu.—Karanta Misalai 3:5, 6.

6. Yaya ake ɗaukan mata a ƙasashe da yawa?

6 Maza da mata suna shan wulaƙanci a wannan duniyar da ke ƙarƙashin ikon Shaiɗan. (M. Wa. 8:9; 1 Yoh. 5:19) Duk da haka, an fi wulaƙanta mata. Mata sama da biliyan 1 a faɗin duniya sun fuskanci wulaƙanci daga mazajensu ko kuma samarinsu. A wasu wurare, an fi son ’ya’ya maza fiye da ’ya’ya mata don an ɗauka cewa su ne za su kula da iyayensu da kakanninsu sa’ad da suka tsufa kuma za su ci gaba da kāre zuriyarsu. Ƙari ga haka, ba a ɗaukan ’ya’ya mata da muhimmanci a wasu ƙasashe kuma an fi zub da cikin ’ya’ya mata fiye da ’ya’ya maza.

7. Wane irin yanayi ne Allah ya shirya wa Adamu da Hawwa’u?

7 Jehobah ba ya jin daɗin wulaƙancin da ake wa mata ko kaɗan. Ba ya nuna bambanci ga mata kuma suna da mutunci a gabansa. Sa’ad da Allah ya halicci Hawwa’u, bai so ta zama baiwa ga Adamu ba, amma ya halicce ta da halaye masu kyau da za su sa ta kasance abokiyar zama da ta dace da Adamu. Shi ya sa bayan Allah ya gama halittar abubuwa, ya “duba kowane abin da ya yi, ga shi kuwa, yana da kyau ƙwarai.” (Far. 1:31) Hakika, “kowane abin” da Allah ya halitta yana da “kyau ƙwarai.” Allah ya tsara dukan abubuwa domin Adamu da Hawwa’u su ji daɗin rayuwa!

WASU MATA DA JEHOBAH YA GOYA MUSU BAYA

8. (a) Yaya halin yawancin mutane yake? (b) Waɗanne mutane ne Allah ya yi wa albarka kamar yadda tarihi ya nuna?

8 Bayan tawayen da aka yi a lambun Adnin, maza da mata sun ci gaba da rashin biyayya ga Jehobah kuma a ƙarnin da ya wuce, halin ’yan Adam ya ƙara muni. Babu shakka, muna rayuwa ne a zamanin da Littafi Mai Tsarki ya kira “kwanaki na ƙarshe.” (2 Tim. 3:1-5) Duk da haka, abubuwan da suka faru a tarihi ya nuna cewa Jehobah ya albarkaci waɗanda suka bi umurninsa, suka dogara da shi kuma suka amince da shi a matsayin maɗaukakin Sarki.—Karanta Zabura 71:5.

9. Mutane nawa ne suka tsira daga Rigyawar, kuma me ya sa?

9 Sa’ad da Allah ya halaka miyagun mutane a zamanin Nuhu da Rigyawa, mutane kaɗan ne suka tsira. Idan ’yan’uwan Nuhu suna da rai a lokacin, su ma sun halaka a Rigyawar. (Far. 5:30) Amma adadin mata da suka tsira daga Rigyawar ɗaya ne da na mazan. Nuhu da matarsa da ’ya’yansa guda uku da matansu ne suka tsira. Su masu tsoron Allah ne kuma sun yi nufinsa, shi ya sa ya cece su. Biliyoyin mutanen da suke raye a yau sun fito daga waɗannan mutane takwas da Jehobah ya kāre.—Far. 7:7; 1 Bit. 3:20.

10. Me ya sa Allah ya albarkaci amintattun matan ubannin iyali?

10 Shekaru da yawa bayan haka, matan Ubannin iyali masu aminci sun amfana daga kāriya da kuma taimakon Allah. Ba su yi gunaguni ba kuma hakan ya sa Jehobah ya albarkace su. (Yahu. 16) Saratu ɗaya ce daga cikin su. Sa’ad da suka bar birnin Ur kuma suka zama baƙi masu zama a tanti a wata ƙasa, ba ta yi gunaguni ba. A maimakon haka, “Saratu ta bi maganar Ibrahim, tana ce da shi ubangiji.” (1 Bit. 3:6) Ka kuma yi la’akari da Rifkatu, wadda mace ce mai albarka da Allah ya ba wa Ishaƙu. Littafi Mai Tsarki ya ce Ishaƙu ya “ƙaunace ta . . . kuma ya ta’azantu bayan mutuwar uwatasa.” (Far. 24:67) A yau, mutanen Jehobah suna farin ciki cewa Allah ya albarkace su da mata masu tsoronsa kamar Saratu da Rifkatu!

11. Ta yaya ungozoma biyu na Ibraniyawa suka nuna gaba gaɗi?

11 Sa’ad da Isra’ilawa suke bauta a ƙasar Masar, adadinsu ya ƙaru sosai kuma suka bunƙasa. Saboda haka, Fir’auna ya ba da umurni cewa a kashe dukan ’ya’ya maza sa’ad da aka haife su. Amma ungozoma biyu na Ibraniyawa masu suna Shiphrah da Puah sun nuna gaba gaɗi kuma sun ƙi bin umurnin Fir’auna don su masu tsoron Jehobah ne. Saboda haka, Jehobah ya albarkace su ta wajen sa su samu nasu iyali.—Fit. 1:15-21.

12. Wane fitaccen abu ne Deborah da Jael suka yi?

12 A zamanin da alƙalawa suke ja-gorar Isra’ilawa, Allah ya naɗa wata mace mai suna Deborah a matsayin annabiya. Deborah ta ƙarfafa Alƙali Barak kuma ta yi rawar gani wajen ceton Isra’ilawa daga zalunci, amma ta annabta cewa ba shi ba ne zai sami ɗaukakar nasarar da Isra’ilawa za su yi bisa Kan’aniyawa ba. A maimakon haka, ta “hannun mace” ce Allah zai ba su nasara bisa rundunar Sisera. Abin da ya faru ke nan domin Jael, wata mata da ba Ba’isra’iliya ba ce ta kashe Shugaban rundunar Sisera.—Alƙa. 4:4-9, 17-22.

13. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da Abigail?

13 Abigail wata mace da ta yi rayuwa a ƙarni na 11 kafin zamaninmu ma ta taka rawar gani. Abigail mace ce mai fahimi, amma mijinta Nabal mugu ne, wawa kuma mara hankali. (1 Sam. 25:2, 3, 25) Akwai wani lokacin da Dauda da mutanensa suka kāre dukiyar Nabal, amma sa’ad da Dauda ya aika mutanensa zuwa wajen Nabal don ya tanadar musu da abinci, sai ya “zazzage su” kuma bai ba su kome ba. Hakan ya ɓata wa Dauda rai sosai har ya shirya su kashe Nabal. Sa’ad da Abigail ta ji hakan, sai ta ɗauki abinci da abin sha, ta kai wa Dauda da mutanensa kuma saboda abin da ta yi, Dauda bai kashe Nabal ba. (1 Sam. 25:8-18) Daga baya, Dauda ya ce mata: “Mai-albarka ne Ubangiji Allah na Isra’ila, wanda ya aiko ki yau garin ki tarbe ni.” (1 Sam. 25:32) Bayan mutuwar Nabal, Dauda ya auri Abigail.—1 Sam. 25:37-42.

14. Wane aiki ne ’ya’ya mata na Shallum suka yi, kuma ta yaya mata Kiristoci suke yin irin wannan aikin a yau?

14 Sa’ad da aka halaka Urushalima da haikalin da ke cikinsa a shekara ta 607 kafin zamaninmu, an kashe maza da mata da kuma yara da yawa. A shekara ta 455 kafin zamaninmu, aka sake gina ganuwar birnin kuma Nehemiya ne ya ja-goranci aikin. ’Ya’ya mata na wani yarima mai suna Shallum da ke mulkin rabin yankin Urushalima, suna cikin waɗanda suka saka hannu a gyarar. (Neh. 3:12) Sun yi aiki da son rai. Muna godiya ga mata Kiristoci da yawa da suke saka hannu a aikin gine-gine na ƙungiyar Jehobah da son rai a yau, kuma suna yin haka a hanyoyi dabam-dabam!

MATA MASU TSORON ALLAH A ƘARNI NA FARKO

15. Wane gata ne Allah ya ba Maryamu?

15 Jehobah ya ba wasu mata gata kafin ƙarni na farko da kuma a ƙarni na farko. Budurwa Maryamu tana cikin waɗannan matan. A lokacin da suka yi alkawarin aure da Yusufu, ruhu mai tsarki ya sa ta yi juna biyu. Me ya sa Allah ya zaɓe ta don ta zama mahaifiyar Yesu? Babu shakka, domin tana da halaye masu kyau kuma hakan zai sa ta yi rainon Yesu har ya girma. Hakika, babban gata ne kasancewa mahaifiyar mutum mafi girma da ya taɓa wanzuwa a duniya!—Mat. 1:18-25.

16. Ka ba da misalin da ya nuna yadda Yesu ya bi da mata.

16 Yesu ya yi wa mata alheri sosai. Alal misali, ka yi la’akari da wata mace da ta yi shekara 12 tana zub da jini. Ta raɓo ta bayan Yesu ta taɓa taguwarsa. Yesu bai tsauta mata ba, maimakon haka, ya ce mata: “Ɗiya, bangaskiyarki ta warkar da ke; ki tafi lafiya, ki rabu da azabarki.”—Mar. 5:25-34.

17. Wane abin ban al’ajibi ne ya faru a Fentakos 33 kafin zamaninmu?

17 Wasu mata almajiran Yesu sun yi wa Yesu da manzanninsa hidima. (Luk 8:1-3) Ƙari ga haka, a ranar Fentakos ta 33 kafin zamaninmu, wajen maza da mata 120 ne Allah ya ba ruhu mai tsarki a wata hanya mai ban al’ajabi. (Karanta Ayyukan Manzanni 2:1-4.) Shekaru da yawa kafin lokacin, Jehobah ya ce: “Zan zuba ruhuna a bisa dukan masu-rai; ’ya’yanku maza da mata za su yi annabci, . . . kuma a bisa bayina maza da mata zan zuba ruhuna.” (Joel 2:28, 29) Allah ya nuna ta wannan abin al’ajabi da ya faru a ranar Fentakos cewa ya daina sha’ani da Al’ummar Isra’ila kuma ya sauya ta da “Isra’ila na Allah” da ta ƙunshi maza da mata. (Gal. 3:28; 6:15, 16) ’Ya’yan Filibus mai bishara suna cikin mata Kiristoci da suka yi hidima a ƙarni na farko.—A. M. 21:8, 9.

‘BABBAR RUNDUNAR’ MATA

18, 19. (a) Wane gata ne Allah ya ba maza da mata? (b) Ta yaya marubucin zabura ya kwatanta mata masu shelar bishara?

18 A shekarun ƙarshe na ƙarni na 19, wasu maza da mata sun yi marmarin sanin ibada ta gaskiya. Su ne waɗanda suka share hanya wa waɗanda suke cika annabcin Yesu da ya ce: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.”—Mat. 24:14.

19 Wannan ƙaramin rukuni na Ɗaliban Littafi Mai Tsarki ya ƙaru zuwa wajen Shaidun Jehobah guda 8,000,000 a yau. Mutane sama da 11,000,000 ne suka halarci taron tuna mutuwar Yesu kuma hakan ya nuna cewa suna son gaskiyar Littafi Mai Tsarki da kuma wa’azin da muke yi. A yawancin ƙasashe, galibin mutanen da suka halarci wannan taron mata ne. Ƙari ga haka, akwai masu hidima ta cikakken lokaci fiye da 1,000,000 a faɗin duniya kuma mata ne suka fi yawa. Babu shakka, Allah ya ba mata gatan cika wannan annabcin da marubucin zabura ya yi: ‘Ubangiji ya bada saƙo: Mata masu-shelar bisharan kuwa babbar runduna ne.’—Zab. 68:11.

ALLAH ZAI ALBARKACI MATA MASU TSORONSA

20. Waɗanne batutuwa ne za mu iya tattaunawa sa’ad da muke nazari?

20 Ba zai yiwu mu ba da labarin dukan mata masu aminci da Littafi Mai Tsarki ya yi maganarsu a nan ba. Amma za mu iya karanta game da su a cikin Kalmar Allah da kuma talifofin da ake wallafawa a cikin littattafanmu. Alal misali, za mu iya yin bimbini a kan amincin da Ruth ta nuna. (Ruth 1:16, 17) Ƙari ga haka, idan muka karanta littafin Esther da kuma talifofin da aka rubuta game da ita, za mu ƙarfafa bangaskiyarmu. Za mu iya yin nazari game da waɗannan matan sa’ad da muke Ibada ta Iyali da yamma. Idan kuma ba mu da iyali, za mu iya karanta irin waɗannan batutuwan sa’ad da muke nazari mu kaɗai.

21. Ta yaya mata masu tsoron Allah suka nuna amincinsu ga Jehobah a mawuyacin lokaci?

21 A bayyane yake cewa Jehobah yana albarkar wa’azin da Kiristoci mata suke yi kuma yana taimaka musu a lokacin da suke fuskantar mawuyacin hali. Alal misali, ya taimaka wa mata masu tsoronsa su kasance da aminci a lokacin mulkin Nazi da kuma Kwaminisanci. Da yawa cikin matan sun sha azaba har ma wasu sun rasa rayukansu don sun kasance da aminci ga Allah. (A. M. 5:29) Kiristoci mata ma a yau, tare da sauran masu bi sun zaɓi Allah a matsayin Sarkinsu. Jehobah ya yi musu alkawari kamar yadda ya yi wa Isra’ilawa na dā cewa: “Kada ku ji tsoro, ni zan taimake ku.”—Isha. 41:10-13, Littafi Mai Tsarki.

22. Waɗanne gata ne za mu iya samu a nan gaba?

22 Nan ba da daɗewa ba, maza da mata masu tsoron Allah za su mai da duniya ta zama aljanna kuma za su koya wa miliyoyin mutane da za a ta da daga matattu nufin Jehobah. Kafin wannan lokacin, bari dukanmu maza da mata mu daraja gatan bauta wa Jehobah da “zuciya ɗaya.”—Zaf. 3:9.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba