Shin Za Ka Iya Zama Kamar Finehas Sa’ad da Ka Fuskanci Ƙalubale?
YIN hidima a matsayin dattijo a cikin ikilisiya gata ne mai tamani. Amma, Kalmar Allah ta nuna cewa dattawa suna fuskantar ƙalubale. A wani lokaci, suna yin shari’o’i “domin Ubangiji” a kan laifuffukan da mutane suka aikata. (2 Laba. 19:6) Ko kuma mai kula zai samu aikin da yake ji bai cancanta ba, kamar yadda ya faru da Musa, wanda ya yi tambaya cikin tawali’u game da wani aikin da aka ba shi: “Wāne ni har da zan tafi wurin Fir’auna.”—Fit. 3:11.
Nassosi da aka rubuta ta wajen ruhu mai tsarki da ya naɗa dattawa, ya ba da misalan masu kula da suka yi nasara wajen bi da gwaje-gwaje. Finehas ɗan Eleazar ne da kuma jikan Haruna saboda haka yana cikin waɗanda za su zama babban firist. Abubuwa uku da suka faru a rayuwarsa sun nuna cewa dattawa a yau suna bukatar su fuskanci ƙalubale da gaba gaɗi da basira kuma su dogara ga Jehobah.
“Sai Ya Tashi”
Finehas matashi ne sa’ad da Isra’ilawa suka kafa sansanin a Filayen Mowab. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutane kuwa suka fara yin fasikanci da yan matan Moab, . . . jama’a kuwa suka ci, suka yi sujada ga allolinsu.” (Lit. Lis. 25:1, 2) Jehobah ya halaka masu laifin da annoba. Babu shakka wannan labari na aikata laifi da annoba ya damu Finehas sosai.
Labarin ya ci gaba: “Ga shi kuwa, wani mutumin Isra’ila ya zo ya kawo ma ’yan’uwansa wata mace Ba-midiya a ganin Musa, da na dukan taron jama’ar Isra’ila, tun suna cikin kuka a bakin ƙofar tent na taruwa.” (Lit. Lis. 25:6) Mene ne Finehas firist zai yi? Shi matashi ne, kuma Ba’isra’ila mai aikata laifin ɗan sarki ne wanda yake ja-gora a bauta tsakanin mutanen.—Lit. Lis. 25:14.
Amma Finehas yana jin tsoron Jehobah ba ’yan Adam ba. Sa’ad da ya ga su biyu, sai ya tashi nan da nan ya ɗauki mashi kuma ya bi su cikin tanti kuma ya sha zaran duka biyunsu. Yaya Jehobah ya ɗauki gaba gaɗi da kuma aniya da Finehas ya nuna? Nan da nan Jehobah ya tsayar da annobar kuma ya saka wa Finehas ta wajen yi masa alkawari cewa tsarin firistanci zai kasance a zuriyarsa “har abada.”—Lit. Lis. 25:7-13.
Hakika, dattawa a yau ba sa nuna ƙarfi. Amma kamar Finehas, ya kamata dattawa su kasance da aniya da kuma gaba gaɗi. Alal misali, Guilherme ya yi ’yan watanni kawai da zama dattijo sa’ad da aka gaya masa ya kasance cikin kwamitin shari’a. Batun ya shafi wani dattijo wanda ya taimaki Guilherme sa’ad da yake yaro. “Ban saki jiki ba a wannan matsayin,” in ji shi. “Ba na iya yin barci da dare. Na ci gaba da tunani yadda zan yi wannan shari’ar ba tare da barin yadda nake ji ya hana ni bi da yanayin bisa mizanan Jehobah ba. Na yi addu’a kwanaki da yawa kuma na yi bincike a cikin littattafai da ke bisa Littafi Mai Tsarki.” Wannan ya taimake shi ya kasance da gaba gaɗi da ake bukata don ya bi da wannan yanayi na musamman kuma ya taimaki wannan ɗan’uwansa da ya yi kuskure a ruhaniya.—1 Tim. 4:11, 12.
Dattawa za su zama misalan bangaskiya da aminci, ta wajen aikatawa da gaba gaɗi da kuma aniya idan yanayi da ke cikin ikilisiya ta bukaci hakan. Hakika, sauran Kiristoci ma suna bukatar aikatawa da gaba gaɗi, su kai ƙarar zunubi mai tsanani da suka sani. Haka nan ma, mutum yana bukatar ya zama mai aminci don ya daina tarayya da aboki ko dangi da aka yi wa yankan zumunci.—1 Kor. 5:11-13.
Basira Tana Sa a Kawar da Masifa
Finehas bai aikata da motsin rai kamar yadda wasu matasa sukan yi ba tare da yin tunani ba. Ka yi la’akari da yadda ya nuna basira, ya aikata da hikima da kuma fahimi sa’ad da ya ji wani labari. Ƙabilun Ra’ubainu da Gad da kuma rabin ƙabilar Manassa sun gina bagadi kusa da Kogin Urdun. Sauran Isra’ilawa sun kammala cewa sun gina shi don bauta ta ƙarya kuma suka yi shirin kai musu hari.—Josh. 22:11, 12.
Mene ne Finehas ya yi? Da hikima, Finehas tare da sarakuna Ba’isra’ila suka tattauna batun da waɗanda suka gina bagadin. Ƙabilu da ake zarginsu suka bayyana cewa sun gina bagadin ainihi don “bauta wa Ubangiji.” Ta hakan, aka daina rigimar.—Josh. 22:13-34.
Zai yi kyau Kirista ya yi koyi da Finehas idan ya ji zargi ko kuma labarin da ba shi da kyau game da ɗan’uwanmu mai bauta wa Jehobah! Basira tana hana mu yin fushi ko kuma faɗan abin da bai dace ba game da ’yan’uwanmu.—Mis. 19:11.
Ta yaya basira za ta taimaka wa dattawa su aikata yadda Finehas ya yi? Jaime, wanda dattijo ne fiye da shekara goma ya ce: “Sa’ad da mai shela ya soma magana game da matsalar da yake da wani, ina gaya wa Jehobah nan da nan ya taimaka mini kada na goyi bayansa amma na ba da umurni na Nassi. Akwai lokacin da wata ’yar’uwa ta gaya mini game da yadda wani ɗan’uwan mai gata a wata ikilisiya ya bi da ita. Tun da yake ɗan’uwan aboki na ne, zai kasance da sauƙi na yi masa magana. Maimakon hakan, ni da ’yar’uwar muka tattauna ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da yawa. Ta yarda ta yi magana tukuna da ɗan’uwan. (Mat. 5:23, 24) Ba su sasanta ba nan da nan. Sai na aririce ta ta yi la’akari da wasu ƙa’idodin Nassi. Ta shawarta ta sake yin addu’a game da yanayin kuma ta yi ƙoƙari ta gafarta.”
Mene ne sakamakon? Jaime ya tuna, “bayan watanni da yawa, ’yar’uwar ta same ni. Ta bayyana cewa, da shigewar lokaci, ɗan’uwan ya yi nadama game da abin da ya faɗa. Ya shirya ya fita hidimar fage tare da ita kuma ya yi mata godiya. Suka sasanta. Da hakan bai faru ba da a ce na goyi bayan wani kuma na sa baki cikin batun.” Littafi Mai Tsarki ya ba da gargaɗi: “Kada ka fita da garaje garin yin husuma.” (Mis. 25:8) Dattawa masu basira suna ƙarfafa Kiristoci da suke da matsala da wani su yi amfani da ƙa’idodin Nassi don su ɗaukaka da kuma kasance da salama.
Ya Tuntuɓi Jehobah
Finehas yana da gatar yin hidima a matsayin firist na mutanen da Allah ya zaɓa. Kamar yadda aka ambata, sa’ad da yake matashi yana da gaba gaɗi da basira da babu kamarsu. Amma, dogarar da ya yi ga Jehobah ya sa ya yi nasara wajen jimre da ƙalubale.
Bayan mutanen Gibeah, na ƙabilar Banyamin sun yi wa ƙwarƙwarar wani Balawi fyaɗe, sauran ƙabilu suka fita don su yi yaƙi da mutanen Banyamin. (Alƙa. 20:1-11) Sun yi addu’a su roƙi taimakon Jehobah kafin su soma yaƙin, amma an ci su sau biyu, kuma sun yi hasara sosai. (Alƙa. 20:14-25) Shin za su kammala cewa ba a amsa addu’o’insu ba? Shin Jehobah yana son ganin cewa sun aikata ga zunubin da aka yi?
Finehas da yanzu babban firist ne ya sake aikatawa da gaba gaɗi. Ya yi addu’a: “In sake fita domin in yi yaƙi har wa yau da ɗan’uwana Banyamin, ko kuwa in bari?” Jehobah ya sa suka ci nasara a kan mutanen Banyamin, kuma aka ƙone Gibeah kurmus.—Alƙa. 20:27-48.
Wane darassi ne za mu iya koya daga wannan? Wasu matsaloli suna ci gaba da kasancewa a cikin ikilisiya ko da yake dattawa suna ƙoƙartawa sosai kuma suna addu’a don taimakon Allah. Idan hakan ya faru, yana da kyau dattawa su tuna da kalaman Yesu: “Ku roƙa [ko yi addu’a], za a ba ku; ku nema, za ku samu; ku ƙwanƙwasa, za a buɗe muku.” (Luk 11:9) Ko idan kamar amsa ga wata addu’a tana jinkiri, ya kamata masu kula su tabbata cewa Jehobah zai amsa a lokacin da ya ga ya dace.
Alal misali, wata ikilisiya a ƙasar Ireland tana bukatar Majami’ar Mulki sosai amma mai ba da fili a yankin ba ya son ’yan’uwan. Ya ƙi ba da dukan wuraren da ’yan’uwan suke son su yi gini. Amma dai kamar wanda zai iya ba da wurin gini shi ne wani wanda ke da hakkin ba da fili a ƙasar baki ɗaya. Shin yin addu’a zai taimaka kamar yadda ya kasance a zamanin Finehas?
Wani dattijo ya ce: “Bayan mun yi addu’a sosai, muka yi tafiya zuwa ainihin ofishin da ake tsara gini. An gaya mini cewa zai ɗauki makonni kafin mu ga ainihin shugaban masu ba da filin. Amma, mun haɗu da shi na tsawon minti biyar. Bayan ya ga zanen ginin, nan da nan ya ba mu izini mu yi ginin, kuma tun daga lokacin mai ba da fili a yankin ya ƙoƙarta ya taimaka mana. Abin da ya faru ya nuna mana cewa addu’a tana da iko.” Hakika, Jehobah zai amsa addu’o’i na dattawa da suka dogara a gare shi.
Finehas yana da hakki mai girma a Isra’ila ta dā, amma da gaba gaɗi da basira da kuma dogara ga Allah, ya yi nasara duk da yanayi mai wuya. Kuma Jehobah ya amince da yadda Finehas ya kula da ikilisiyar Allah da ƙwazo. Bayan shekaru 1,000, an hure Ezra ya rubuta: Finehas “ɗan Eleazar shi ne mai-mulkinsu a kwanakin dā, Ubangiji kuwa yana tare da shi.” (1 Laba. 9:20) Bari ya kasance hakan ga dukan waɗanda suke shugabanci tsakanin mutanen Allah a yau, hakika, ga dukan Kiristoci da suke bauta masa da aminci.