Ka Bauta Wa Allahn Da Ke Ba Da ’Yanci
“Ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba.” —1 YOH. 5:3.
MECE CE AMSARKA?
Ta yaya Shaiɗan yake sa mu ga kamar bin dokokin Allah yana da wuya?
Me ya sa muke bukata mu yi hattara game da irin abokai da muke yi?
Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da kasancewa da aminci ga Allah mai ’yanci?
1. Yaya Jehobah yake yin amfani da ’yancinsa, kuma wane ’yanci ne ya ba wa Adamu da Hauwa’u?
JEHOBAH ne kaɗai yake da cikakken ’yanci. Amma, yana amfani da ’yancinsa a hanyar da ta dace a kowane lokaci kuma ba ya sa ido a dukan abubuwan da bayinsa suke yi. A maimakon haka, ya ba su ’yancin yin zaɓin abin da suke so da kuma biyan dukan bukatunsu masu kyau. Alal misali, abu guda ne kawai Allah ya gaya wa Adamu da Hauwa’u kada su yi. Ya hana su cin “itace na sanin nagarta da mugunta.” (Far. 2:17) Saboda haka, za su iya yin nufin Mahaliccinsu su kuma kasance da ’yanci sosai!
2. Me ya sa iyayenmu na farko suka rasa ’yancin da Allah ya ba su?
2 Me ya sa Allah ya ba iyayenmu na farko ’yanci sosai? Domin Jehobah ya halicce su cikin siffarsa kuma ya ba su lamiri, ya kamata su yi abin da ya dace domin suna ƙaunarsa a matsayin Mahaliccinsu. (Far. 1:27; Rom. 2:15) Abin baƙin ciki, Adamu da Hauwa’u ba su nuna godiya ga Mahaliccinsu ba a yadda suka yi amfani da ’yancin da ya ba su. Maimakon haka, sun zaɓi su yi wa kansu ja-gora game da nagarta da mugunta. Maimakon samun ’yanci na gaske, iyayenmu na fari da ’ya’yansu sun zama bayi ga zunubi kuma sakamakon hakan shi ne wahala da kuma mutuwa.—Rom. 5:12.
3, 4. Wane irin ra’ayi ne Shaiɗan yake so mu kasance da shi game da ƙa’idodin Jehobah?
3 Idan Shaiɗan zai iya rinjayar mutane biyu kamiltattu da kuma mala’iku da yawa su bijire wa sarautar Allah, babu shakka zai iya rinjayar mu. Shaiɗan bai canja dabararsa ba. Yana so mu yi tunanin cewa kiyaye ƙa’idodin Allah yana da wuya ainun kuma yana hana mu samun sakewa da kuma jin daɗin rayuwa. (1 Yoh. 5:3) Yawancin mutane suna da wannan ra’ayin kuma idan muna tarayya da su kullum, ra’ayin nan zai shafe mu. Wata Kirista ’yar shekara 24 da ta taɓa yin lalata ta ce: “Yin tarayya da mutanen banza ya shafe ni sosai don ba na son ra’ayina ya bambanta da na abokaina.” Wataƙila kai ma ka taɓa shaida yadda halin abokai yake iya shafan mutum.
4 Wasu ma a cikin ikilisiyar Kirista za su iya rinjayar ka a hanyar da ba ta dace ba. Wani ɗan’uwa matashi ya ce: “Na yi abota da wasu ’yan’uwa da suke fita zance da waɗanda ba sa bauta wa Jehobah, tarayya da nake yi da su ya sa na fara nuna irin halayensu. Hakan ya sa na fara samun matsala a dangantakata da Jehobah. Ba na jin daɗin taro kuma, har na kusan in daina fita wa’azi. Sai na fahimci cewa ina bukatar in daina tarayya da waɗannan abokan, kuma abin da na yi ke nan!” Ka san cewa tarayya da abokai zai iya shafan halinka sosai? Bari mu yi la’akari da wani misali na Littafi Mai Tsarki da zai iya taimaka mana a yau.—Rom. 15:4.
YA RINJAYE SU
5, 6. Ta yaya Absalom ya yaudari mutane, ya yi nasara kuwa a dabararsa?
5 Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da misalai da yawa na miyagu da suka rinjayi wasu. Absalom ɗan Sarki Dauda, ɗaya ne daga cikinsu. Shi kyakkyawan mutum ne. Da shigewar lokaci, Absalom ya ƙyale haɗama ta shawo kansa kamar yadda Shaiɗan ya yi, sai ya fara tunanin yadda zai yi wa mahaifinsa juyin mulki, ko da yake ba shi da ikon yin hakan.a Don ya cim ma wannan mugun nufin, Absalom ya fara nuna kamar ya damu da mutane, kuma yana so ya taimake su. Hakan ya sa mutane tunanin cewa Sarki Dauda bai damu da su ba. Ƙari ga hakan, ya tabka ƙarya game da mahaifinsa kamar yadda Shaiɗan ya yi a gonar Adnin.—2 Sam. 15:1-5.
6 Absalom ya yi nasara ne a dabararsa? E to, ya ɗan yi nasara domin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Absalom ya sace zukatan mazaje na Isra’ila.” (2 Sam. 15:6) Absalom ya yaudari mutane da yawa, amma a ƙarshe, ya sha kashi. Ƙari ga haka, girman kansa ya yi sanadiyyar mutuwarsa da na dubban mutanen da suka bi shi.—2 Sam 18:7, 14-17.
7. Wane darasi ne za mu koya daga misalin Absalom? (Duba hoton da ke shafi na 14.)
7 Me ya sa ya yi wa Absalom sauƙi ya yaudare mutane? Wataƙila suna son su samu abubuwan da Absalom ya yi musu alkawarinsu. Wataƙila kuma kyaunsa ne ya sa suka yaudaru. Ko ma mene ne ya sa, abin da suka yi ya nuna cewa ba su da aminci ga Jehobah da kuma sarkin da ya naɗa. A yau, Shaiɗan yana amfani da mutane da suke kamar Absalom don ya rinjayi bayin Jehobah. Waɗannan mutanen za su iya ce ƙa’idodin Jehobah suna da wuyan kiyayewa, ko kuma su ce waɗanda ba sa bauta wa Jehobah ne suka fi jin daɗin rayuwa. Sa’ad da ka ji mutane suna irin waɗannan maganganun, za ka gane ne cewa ƙarya suke yi kuma ka ci gaba da kasancewa da aminci ga Jehobah? Za ka gane cewa cikakkiyar shari’a” ta Allah wato, shari’a ta Kristi kawai ce take ba da ’yanci? (Yaƙ. 1:25) Idan ka yi hakan, za ka nuna cewa kana ƙaunar shari’ar kuma ba ka son ka ɓata ’yancinka na Kirista.—Karanta 1 Bitrus 2:16.
8. Waɗanne misalai ne suke nuna cewa yin watsi da ƙa’idodin Jehobah ba ya kawo farin ciki?
8 Burin Shaiɗan musamman shi ne ya yaudari matasa. Wani ɗan’uwa, mai shekara 30 yanzu ya ce game da lokacin da yake matashi: “Ina ganin bin ƙa’idodin Jehobah game da ɗabi’a matsi ne, kamar ba ni da ’yanci ne.” Saboda haka, ya yi lalata. Amma, hakan bai sa shi farin ciki ba. “Na yi shekaru da yawa ina da-na-sani,” in ji shi. Wata ’yar’uwa da ta tuna abin da ta yi sa’ad da take matashiya ta rubuta cewa: “Idan kin yi lalata, sai mutuncinki gaba ɗaya ya zube kuma ba za ki ji daɗi ba. Bayan shekara 19 yanzu, idan na tuna, sai in riƙa baƙin ciki.” Wata ’yar’uwa ta ce: “Sanin cewa halina ya sa mutanen da nake ƙauna sosai baƙin ciki ya shafi tunanina da motsin raina da kuma dangantakata da Jehobah. Yin rayuwa ba tare da kāriyar Jehobah ba, bai da daɗi ko kaɗan.” Shaiɗan ba ya son ka yi tunanin sakamakon yin lalata.
9. (a) Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu game da Jehobah da dokokinsa da kuma ƙa’idodinsa? (b) Me ya sa yake da muhimmanci mu san Allah sosai?
9 Abin baƙin ciki ne cewa matasa da yawa da suke cikin gaskiya, har ma da wasu manya sun shaida cewa yin zunubi don annashuwa yana sa baƙin ciki da wahala ƙwarai! (Gal. 6:7, 8) Saboda haka, ka tambayi kanka: ‘Na gane irin dabarun da Shaiɗan yake amfani da su don ya yaudare ni? Na ɗauki Jehobah a matsayin aboki na kud da kud, kuma cewa yana gaya mini gaskiya a koyaushe don in amfana? Na amince cewa Jehobah ba zai taɓa hana ni abu mai kyau da zai sa in yi farin ciki na gaske ba?’ (Karanta Ishaya 48:17, 18.) Za ka iya ba da amsa kawai da dukan zuciyarka idan ka san Jehobah sosai. Kana bukatar ka san cewa dokoki da ƙa’idodin da ke Littafi Mai Tsarki suna bayyana cewa Jehobah yana ƙaunarka ne, ba wai Jehobah yana so ya rage maka jin daɗi ba.—Zab. 25:14.
KA ROƘI ALLAH YA BA KA ZUCIYA MAI HIKIMA DA KUMA MAI BIYAYYA
10. Me ya sa muke bukata mu yi koyi da Sulemanu?
10 Sa’ad da Sulemanu yake matashi, ya yi addu’a cikin tawali’u, ya ce: ‘Ni kuwa yaro ne ƙanƙani kaɗai; ban san ƙa’idar duniya ba.’ Sai ya roƙi Allah ya taimaka masa ya zama mai hikima da biyayya. (1 Sar. 3:7-9, 12) Jehobah ya amsa wannan addu’a da Sulemanu ya yi. Hakazalika, idan ka yi irin wannan addu’ar, Jehobah zai amsa maka, ko kai yaro ne ko babba. Ko da yake Jehobah ba zai sa ka zama mai hikima nan take ba, amma, zai ba ka hikima idan kana nazarin Kalmarsa da ƙwazo, kana addu’a ya ba ka ruhu mai tsarki kuma kana bin ja-gora da umurni da ake bayarwa a cikin ikilisiyar Kirista. (Yaƙ. 1:5) Hakika, ta haka Jehobah zai sa bawansa ya yi hikima fiye da dukan waɗanda suka yi watsi da umurninsa, da kuma “masu-hikima da masu-fahimi” na wannan duniyar.—Luk 10:21; karanta Zabura 119:98-100.
11-13. (a) Waɗanne muhimman darussa ne za mu iya koya daga Zabura 26:4 da Misalai 13:20 da kuma 1 Korintiyawa 15:33? (b) Ta yaya za ka yi amfani da waɗannan darussan a rayuwarka?
11 Bari mu tattauna wasu nassosi da za su nuna muhimmancin yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma yin bimbini. Kowane nassi yana koya mana ƙa’ida mai kyau game da irin abokai da muke yi. “Ban tara zama da mutanen banza ba; ba kuwa zan shiga tare da masu-makirci ba.” (Zab. 26:4) “Ka yi tafiya tare da masu-hikima, kai kuwa za ka yi hikima: amma abokin tafiyar wawaye za ya cutu dominsa.” (Mis. 13:20) “Kada ku yaudaru: zama da miyagu ta kan ɓata halaye na kirki.”—1 Kor. 15:33.
12 Waɗanne muhimman darussa ne za mu koya daga waɗannan nassosin? (1) Jehobah yana so ya mu yi hankali wajen zaɓan abokai. Yana so ya kāre dangantakarmu da shi kuma ya kāre mu daga muguwar ɗabi’a. (2) Halayen abokan da muka yi suna shafanmu a hanyar da ta dace ko kuma a hanyar da ba ta dace ba. Hakika, wannan gaskiya ce. Ta yaya? Ka lura cewa abubuwan da waɗannan ayoyin suka faɗa dahir ne, ayoyin ba su ce: “Kada ka yi kaza da kaza” ba. Amma abubuwan da ayoyin suka faɗa gaskiya ne wanda kowa ya sani. Kamar dai, Jehobah yana faɗa mana: ‘Ga zahirin gaskiya. Wane mataki ne za ka ɗauka? Mene ne ra’ayinka?’
13 A ƙarshe, da yake abubuwan da waɗannan ayoyin suke faɗa gaskiya ne wanda kowa ya sani, suna da amfani a yau kamar yadda suke a dā. Ka tambayi kanka: A wane yanayi ne zan iya haɗuwa da “masu-makirci”? Wane mataki ne zan ɗauka don kada in yi tarayya da su? (Mis. 3:32; 6:12) Su waye ne “masu-hikima” da Jehobah yake so in yi tarayya da su? Su waye ne “wawaye” da Jehobah ba ya so in yi harka da su? (Zab. 111:10; 112:1; Mis. 1:7) Waɗanne “halaye na kirki” ne zan ɓata idan na yi tarayya da mutanen banza? Ana iya samun abokan banza a cikin ikilisiya? (2 Bit. 2:1-3) Yaya za ka amsa waɗannan tambayoyin?
14. Me kuke bukata ku yi don ku kyautata Bautarku ta Iyali da yamma?
14 Hakazalika, kamar yadda ka bincika waɗannan ayoyin, za ka iya yin bincike a kan waɗansu ayoyin Littafi Mai Tsarki don ka fahimci ra’ayin Jehobah game da batutuwan da suka shafe ka da iyalinka.b Iyaye, za ku iya tattauna waɗannan batutuwan sa’ad da kuke Bauta ta Iyali da yamma. Sa’ad da kuke yin haka, ku tuna cewa dalilin shi ne ku taimaka wa kowa a iyalin ya fahimci cewa Allah ya ba mu ƙa’idodi da dokoki don yana ƙaunarmu ne. (Zab. 119:72) Idan kuka yi Bauta ta Iyalinku haka, za ku ƙarfafa ƙaunar da kuke yi wa juna da kuma dangantakarku da Jehobah.
15. Ta yaya za ka sani cewa ka fara yin hikima da kuma biyayya?
15 Ta yaya za ka sani cewa ka fara yin hikima da kuma biyayya? Wata hanya da za ka sani ita ce ta gwada ra’ayinka da na bayin Jehobah masu aminci na dā, kamar Sarki Dauda, wanda ya ce: ‘Murna na ke yi in yi nufinka, ya Allahna, hakika, shari’arka tana cikin zuciyata.’ (Zab. 40:8) Hakazalika, wanda ya rubuta Zabura 119 ya ce: ‘Ina ƙaunar shari’arka ba misali! Abin tunawa ne a gareni dukan yini.’ (Zab. 119:97) Kana bukatar ka yi aiki tuƙuru don ka kasance da irin wannan ƙaunar. Za ka samu irin wannan ƙaunar idan kana yin nazarin Littafi Mai Tsarki sosai da addu’a da kuma bimbini. Kuma idan ka shaida a rayuwarka cewa ana samun albarka da yawa don bin ƙa’idodin Jehobah.—Zab. 34:8.
KA YI KOKAWA DON KA SAMU ’YANCI NA KIRISTA
16. Mene ne za mu yi idan muna son mu yi nasara a kokawar da muke yi don mu samu ’yanci?
16 Al’ummai da yawa sun yi yaƙi sosai don su samu ’yancin kai. Kana da ƙwaƙƙwarar dalili fiye da su na manne wa ’yancin da kake da shi a matsayin Kirista! Ka tuna cewa maƙiyanka ba Shaiɗan da duniyarsa da kuma abin da ke tunzura mutane su yi abin da bai dace ba ne kawai. Kana bukatar ka yi kokawa da ajizancinka da kuma zuciyarka da za ta iya yaudararka. (Irm. 17:9; Afis. 2:3) Duk da haka, za ka iya yin nasara da taimakon Jehobah. Duk lokacin da ka yi abu mai kyau, kana cim ma abubuwa guda biyu. Na farko, kana faranta wa Jehobah rai. (Mis. 27:11) Na biyu, yayin da kake morar albarka da ake samu daga yin biyayya ga ‘cikakkiyar shari’a ta ’yanci’ ta Allah, za ka ƙudura aniyar kasancewa a ‘matsatsiyar hanya’ da za ta kai ga rai na har abada.—Yaƙ. 1:25; Mat. 7:13, 14.
17. Sa’ad da muka yi kuskure, me ya sa bai kamata mu yi sanyin gwiwa ba, kuma wane taimako ne Jehobah yake tanadarwa?
17 A wasu lokatai, muna yin kuskure. (M. Wa. 7:20) Amma idan hakan ya faru, kada ka yi sanyin gwiwa ko kuwa ka ɗauki kanka ba ka da daraja. Sa’ad da ka yi kuskure, ka ɗauki matakin da ya kamata don ka yi gyara, ko da yin hakan yana nufin neman taimakon dattawan ikilisiya. “Addu’ar bangaskiya [na dattawa] kuwa za ta ceci mai-ciwo, Ubangiji kuwa za ya tashe shi; idan kuma ya yi zunubai, za a gafarta masa.” (Yaƙ. 5:15) Kada ka manta cewa Jehobah, Allah ne mai jin ƙai na gaske kuma yana so ka kasance a cikin ikilisiya saboda ya ga cewa kana da zuciyar kirki. (Karanta Zabura 103:8, 9.) Jehobah zai taimaka maka muddin ka yi ƙoƙarin bauta masa da zuciya ɗaya.—1 Laba. 28:9.
18. Ta yaya za mu yi amfani da addu’ar da Yesu ya yi a Yohanna 17:15?
18 A daren da Yesu ya mutu, ya yi wannan addu’ar da ba za a taɓa mantawa ba a madadin almajiransa guda 11 masu aminci: “Ka tsare su daga Mugun.” (Yoh. 17:15) Kamar yadda Yesu ya damu da almajiransa, hakan ma yana damuwa da dukan mabiyansa a yau. Saboda haka, za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai amsa addu’ar da Yesu ya yi ta wajen kula da mu a waɗannan miyagun kwanaki. “Garkuwa ne shi [Jehobah] ga waɗanda ke tafiya cikin gaskiya . . . Shi kiyaye tafarkin tsarkakansa.” (Mis. 2:7, 8) Hakika, ba shi da sauƙi mu kiyaye dokokin Jehobah, amma waɗanda suka yi biyayya ne kawai za su samu rai na har abada da kuma ’yanci na gaske. (Rom. 8:21) Kada ka yarda wani ya yaudare ka cewa hakan ba gaskiya ba ne!
[Hasiya]
a A lokacin da Allah ya yi wa Dauda alkawarin ‘zuriya’ ko kuma ɗa da zai gāji sarautarsa, an riga an haifi Absalom. Saboda haka, ya kamata Absalom ya san cewa Jehobah bai zaɓe shi ya zama wanda zai gaji Dauda ba.—2 Sam. 3:3; 7:12.
b Ga misalai masu kyau na nassosi da kai da iyalinka za ku iya yin nazari a kai: 1 Korintiyawa 13:4-8 inda Bulus ya kwatanta yadda ƙauna take, da kuma Zabura 19:7-11 wadda ta lissafta albarka masu yawa da ake samu daga bin dokokin Jehobah.
[Hotona a shafi na 14]
Ta yaya za mu gane waɗanda suke kamar Absalom kuma mu guje su?