Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 6/15 pp. 7-11
  • Ka Kasance Da Himma Don Bautar Jehobah!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Kasance Da Himma Don Bautar Jehobah!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Gidan Allah a Dā da Kuma Yanzu
  • Hidima da Zuciya Ɗaya Tana Kawo Albarka
  • Ku Kula da Wuraren Taronmu da Kyau
  • Ka Yi Biyayya da Umurnin Allah
  • Ka Aikata Nan da Nan ga Umurni
  • Ka Bauta wa Jehobah da Dukan Zuciyarka!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Kana Amfani da Abubuwan da Aka Rubuta Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Ku Zama “Masu-himman Nagargarun Ayyuka”!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Kana Tambaya Kuwa, “Ina Ubangiji?”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 6/15 pp. 7-11

Ka Kasance Da Himma Don Bautar Jehobah!

“Himma domin gidanka za ta cinye ni.”—YOH. 2:17.

1, 2. Menene Yesu ya yi a cikin haikali a shekara ta 30 A.Z., kuma me ya sa?

KA YI tunanin abin da ya faru. Ana Idin Ƙetarewa a shekara ta 30 A.Z. Watanni shida da suka shige ne Yesu ya soma hidimarsa a duniya. Sai ya tafi Urushalima. A haikalin a Farfajiyar ’yan Al’ummai, Yesu ya sami “waɗanda su ke sayasda shanu da tumaki da kurciyoyi, kuma da masu-musanyan kuɗi, suna zaune.” Ya yi bulala da igiya, ya kori dukan dabbobin, kuma dillalan suka bi su. Yesu ya kuma watsar da tsabar kuɗin ’yan canjin, kuma ya birkice teburansu. Ya umurci waɗanda suke sayar da kurciyoyi su kwashi kayansu su tafi.—Yoh. 2:13-16.

2 Ayyukan Yesu sun nuna cewa ya damu da haikalin. Ya ce: “Kada ku maida gidan Ubana gidan ciniki.” Yayin da almajiran Yesu suka ga waɗannan abubuwa, suka tuna da kalmomi da mai zabura Dauda ya rubuta ƙarnuka da suka shige: “Himma domin gidanka za ta cinye ni.”—Yoh. 2:16, 17; Zab. 69:9.

3. (a) Mecece himma? (b) Wace tambaya ce za mu iya yi wa kanmu?

3 Damuwar da Yesu ya yi da gidan Allah, da kuma himmarsa ce ta motsa shi ya yi hakan. Himma tana nufin “ɗoki da kuma son biɗan wani abu.” A wannan ƙarni na 21, Kiristoci fiye da miliyan bakwai ne suke nuna himma don bautar Allah. Kowannenmu yana iya tambayar kansa, ‘Yaya zan iya ƙara himma don bautar Jehobah?’ Don a ba da wannan amsar, bari mu fara bincika ko menene bautar Allah a yau. Bayan haka, za mu tattauna misalan mutane masu aminci cikin Littafi Mai Tsarki da suka nuna himma don bautar. An rubuta misalansu “domin koyarwarmu” kuma zai iya motsa mu mu nuna himma sosai.—Rom. 15:4.

Gidan Allah a Dā da Kuma Yanzu

4. Menene amfanin haikalin da Sulemanu ya gina?

4 A Isra’ila ta dā, gidan Allah shi ne haikalin da ke Urushalima. Hakika, Jehobah ba ya zama a wurin a zahiri. Ya ce: “Sama kursiyina ce, duniya kuwa matashin sawuna ce; wane irin gida fa za ku gina mani? wane wuri kuma za ya zama wurin hutawata?” (Isha. 66:1) Duk da haka, haikalin da aka gina a lokacin sarautar Sulemanu shi ne ainihin wurin da ake bauta wa Jehobah, inda ake yin addu’a.—1 Sar. 8:27-30.

5. Mecece bauta a haikalin Sulemanu take wakilta a zamani?

5 A yau, gidan Jehobah ba gini ba ne a Urushalima ko kuma a wani waje. Maimakon haka, hanya ce ta kusantarsa don bauta bisa hadayar fansa ta Kristi. Dukan bayin Allah masu aminci a duniya sun haɗa kai don su bauta wa Jehobah a wannan haikali ta ruhaniya.—Isha. 60:4, 8, 13; A. M. 17:24; Ibran. 8:5; 9:24.

6. Waɗanne sarakuna na Yahudawa ne suka nuna himma na musamman don bauta ta gaskiya?

6 Bayan an raba Isra’ila zuwa mulkoki biyu a shekara ta 997 K.Z., sarakuna huɗu cikin goma sha tara da suka yi sarauta a Yahuda, wato, mulki na kudanci, sun nuna himma na musamman don bauta ta gaskiya. Sarakunan su ne Asa, Jehoshaphat, Hezekiya, da Josiah. Waɗanne darussa masu muhimmanci ne za mu iya koya daga misalansu?

Hidima da Zuciya Ɗaya Tana Kawo Albarka

7, 8. (a) Wace irin hidima ce Jehobah yake yi wa albarka? (b) Wane darassi ne za mu iya koya daga misalin Sarki Asa?

7 A lokacin sarautar Sarki Asa, Jehobah ya aika annabawa su yi wa al’ummarsa ja-gora don su bi tafarki na aminci. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Asa ya saurari annabi Azariah, ɗan Oded. (Karanta 2 Labarbaru 15:1-8.) Gyara da Asa ya yi ya haɗa kan mutanen Yahuda da kuma mutane da yawa daga mulkin Isra’ila da suka zo su haɗu su yi taro mai girma a Urushalima. Sun sanar da ƙudurinsu na bauta wa Jehobah da aminci tare. Nassi ya ce: “Suka rantse ma Ubangiji da murya mai-ƙarfi, da kuma ihu, da ƙafoni, da bushe bushe. Dukan Yahuda fa suka yi murna domin rantsuwar: gama suka rantse da dukan zuciyarsu, suka biɗe shi kuma da iyakacin niya; ya kuwa samu garesu: Ubangiji kuwa ya kewaye su da hutu koina.” (2 Laba. 15:9-15) Hakanan ma, Jehobah zai albarkace mu idan muka bauta masa da dukan zuciyarmu.—Mar. 12:30.

8 Abin baƙin ciki, daga baya Asa ya yi fushi sa’ad da Hanani mai gani ya yi masa gyara. (2 Laba. 16:7-10) Ya muke ji sa’ad da Jehobah ya ba mu shawara ko ja-gora ta wurin dattawa Kiristoci? Muna bin gargaɗinsu da ke bisa Nassi nan da nan kuma mu guji riƙe a zuciya?

9. Wace barazana ce Jehoshaphat da mutanen Yahuda suka fuskanta, kuma menene suka yi?

9 Jehoshaphat ya yi sarauta a Yahuda a ƙarni na goma K.Z. Shi da dukan Yahuda sun fuskanci barazanar rundunar haɗin gwiwa ta Ammon, Mowab da kuma mazauna dutsen Seir. Ko da yake yana jin tsoro, menene sarkin ya yi? Shi da mutanensa, tare da matansu da yara, sun taru a gidan Jehobah don su yi addu’a. (Karanta 2 Labarbaru 20:3-6.) Cikin jituwa da kalaman da Sulemanu ya furta da farko sa’ad da ake keɓe haikalin, Jehoshaphat ya roƙi Jehobah: “Ya Allahnmu, ba za ka shar’anta masu ba? gama mu ba mu da wani ƙarfi wurin wannan babban taron da ke zuwa yaƙi da mu; mun kuwa rasa yadda za mu yi: amma idanunmu suna gareka.” (2 Laba. 20:12, 13) Bayan Jehoshaphat ya yi addu’a, “a cikin tsakiyar jama’a,” ruhun Jehobah ya zo kan Jahaziel, Balawi, ya furta kalamai masu ƙarfafawa da suka sa mutanen suka kasance da ƙarfin zuciya.—Karanta 2 Labarbaru 20:14-17.

10. (a) Ta yaya Jehoshaphat da masarautar Yahuda suka sami ja-gora? (b) Ta yaya za mu nuna godiya ga umurnin da Jehobah yake ba mu a yau?

10 Hakika, a lokacin, Jehoshaphat da masarautan Yahuda sun samu ja-gora daga Jehobah ta bakin Jahaziel. A yau, muna samun ƙarfafa da ja-gora ta wurin rukunin bawan nan mai aminci mai hikima. Babu shakka, za mu so mu haɗa kai kuma mu nuna ladabi ga dattawa da aka naɗa, waɗanda suke aiki tuƙuru wajen kiwonmu da kuma cika umurnin “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.”—Mat. 24:45; 1 Tas. 5:12, 13.

11, 12. Wane darasi ne za mu iya koya daga abin da ya faru da Jehoshaphat da Yahuda?

11 Kamar yadda Jehoshaphat da mutanensa suka taru don su biɗi ja-gorar Jehobah, kada mu yi banza da halartan taron ikilisiya tare da ’yan’uwanmu a kai a kai. Idan wani lokaci muka samu kanmu cikin matsala mai tsanani, kuma ba mu san abin da za mu yi ba, bari mu bi misali mai kyau da Jehoshaphat da mutanen Yahuda suka kafa kuma mu yi addu’a ga Jehobah kuma mu dogara a gare shi sosai. (Mis. 3:5, 6; Filib. 4:6, 7) Ko da mun kasance mu kaɗai, addu’armu ga Jehobah na haɗa mu da ‘’yan’uwanmu da ke cikin duniya.’—1 Bit. 5:9.

12 Jehoshaphat da mutanensa sun bi ja-gorar da Allah ya ba su ta bakin Jahaziel. Menene sakamakon? Sun ci yaƙin kuma suka koma Urushalima “da murna” da “molaye da girayu da ƙafoni zuwa gidan Ubangiji.” (2 Laba. 20:27, 28) Mu ma muna bin ja-gora da Jehobah yake ba mu ta wurin waɗanda yake amfani da su kuma mu yabe shi tare da su.

Ku Kula da Wuraren Taronmu da Kyau

13. Wane aiki ne Hezekiah ya yi sa’ad da ya soma sarauta?

13 A watan farko ta sarautarsa, Hezekiah ya nuna himmarsa don bautar Jehobah ta wajen sake buɗe haikali da kuma gyara shi. Ya tsara firistoci da Lawiyawa su tsabtace gidan Allah. Sun yi hakan cikin kwanaki goma sha shida. (Karanta 2 Labarbaru 29:16-18.) Abin da ya yi ya tuna mana cewa aikin adana da kuma gyara wuraren taronmu na nuna himmarmu don bauta ta Jehobah. Babu shakka, ka ji labarai da suka nuna cewa himmar da ’yan’uwanmu suke nuna wa a irin wannan aikin yana burge mutane! Hakika, ƙoƙarce-ƙoƙarcensu na sa a yabi Jehobah sosai.

14, 15. Wane aiki ne a yau yake sa a yabi Jehobah sosai? Ka ba da misali.

14 A wani birni da ke arewancin Ingila, wani mutum ba ya son a gyara Majami’ar Mulki da ke dab da gidansa. ’Yan’uwan sun yi masa kirki. Da yake sun lura cewa bangon da ke tsakanin Majami’ar Mulkin da gidan maƙwabcin na bukatar gyara, sai suka yi masa gyaran kyauta. Sun yi aiki tuƙuru kuma sun sake gina yawancin bangon. Ayyukan waɗannan ’yan’uwan ya sa maƙwabcin ya canja halinsa. Yanzu yana kula da Majami’ar Mulkin.

15 Mutanen Jehobah suna saka hannu a aikin gine-ginen da ake yi a dukan duniya. Waɗanda suka ba da kansu da son rai tare da bayi masu hidima na ƙasashen waje suna gina Majami’un Mulki, da Majami’un Manyan Taro da gidajen Bethel. Sam injiniya ne da ya ƙware wajen gina wurin ɗumama ɗaki, inda iska mai daɗi za ta shiga ɗaki, da kuma saka iyakwandishan. Da shi da matarsa Ruth, sun je ƙasashe da yawa a Turai da Afirka don su ba da taimako a ayyukan gine-gine. Duk inda suka je, suna jin daɗin yin wa’azi tare da ikilisiyoyin da ke wajen. Sam ya bayyana abin da ya motsa shi ya sa hannu a irin waɗannan ayyuka na dukan ƙasashe: “Waɗanda suka yi hidima a gidajen Bethel dabam-dabam ne suka ƙarfafa mu. Ganin himmarsu da farin ciki ne ya motsa ni na so yin hidima a wannan hanyar.”

Ka Yi Biyayya da Umurnin Allah

16, 17. Wane aiki na musamman ne mutanen Allah suka yi da himma, da wane sakamako?

16 Ƙari ga gyara haikalin, Hezekiah ya dawo da Idin Ƙetarewa da Jehobah ya ba su umurni su riƙa yi kowace shekara. (Karanta 2 Labarbaru 30:1, 4, 5.) Hezekiah da mazauna Urushalima sun gayyaci dukan al’ummar har da waɗanda suke masarautan arewa su halarci idin. Manzanni sun tafi duk cikin ƙasar suna rarraba wasiƙun gayyata.—2 Laba. 30:6-9.

17 A shekaru na baya bayan nan, mun yi irin wannan gayyata. Mun yi amfani da takardun gayyata masu ban sha’awa don mu gayyaci mutane da ke yankunanmu su taru da mu wajen kiyaye Jibin Maraice na Ubangiji, cikin biyayya ga umurnin Yesu. (Luk 22:19, 20) Da yake an gaya mana yadda za mu yi hakan a Taronmu na Hidima, mun yi wannan aikin da himma. Kuma Jehobah ya albarkaci waɗannan ƙoƙarce-ƙoƙarcen! A shekarar da ta wuce, mutane miliyan bakwai sun rarraba takardun gayyata, kuma mutane 17,790,631 sun halarta!

18. Me ya sa kasancewa da himma don bauta ta gaskiya take da muhimmanci sosai a gareka?

18 An faɗa game da Hezekiah cewa: “Ya dogara ga Ubangiji, Allah na Isra’ila; har bayansa ba a yi wani kamassa a cikin sarakunan Yahuda duka, ko cikin waɗanda suka rigaye shi. Gama ya manne ma Ubangiji, ba ya rabu da binsa ba, amma ya kiyaye umurnansa waɗanda Ubangiji ya umurta ma Musa.” (2 Sar. 18:5, 6) Bari mu bi misalinsa. Himmarmu don gidan Allah zai taimake mu mu ‘ci gaba da manne wa Jehobah’ da begen samun rai madawwami.—K. Sha 30:16.

Ka Aikata Nan da Nan ga Umurni

19. Waɗanne ƙoƙarce-ƙoƙarce ne ake yi a lokacin Tuna Mutuwar Yesu?

19 Sa’ad da Josiah yake sarauta, shi ma ya yi shiri sosai don a riƙa yin Idin Ƙetarewa. (2 Sar. 23:21-23; 2 Laba. 35:1-19) Mu ma ya kamata mu riƙa shiri sosai don taron gunduma, taron da’ira, taro na musamman, da kuma Tuna Mutuwar Yesu. ’Yan’uwa a wasu ƙasashe suna sadaukar da rayukansu domin su taru su kiyaye mutuwar Kristi. Dattawa masu himma suna tabbata cewa ba a ƙyale kowa a cikin ikilisiya ba. Tsofaffi da naƙasassu sun sami taimako don su halarta.

20. (a) Menene ya faru a lokacin sarautar Josiah, kuma yaya ya aikata? (b) Wane darassi ya kamata mu riƙa tunawa?

20 A lokacin aikin sake gini da Sarki Josiah ya tsara, Babban Firist Hilkiah ya samu “litafin shari’ar Ubangiji, wanda Musa ya bayas.” Sai ya miƙa littafin ga Shaphan, wanda shi ne sakatare sarki, kuma ya soma karanta abin da ke ciki ga Josiah. (Karanta 2 Labarbaru 34:14-18.) Menene sakamakon? Nan da nan sarkin ya yayyage tufafinsa yana makoki kuma ya umurci mutanen su je su tuntuɓi Jehobah. Ta wurin annabiya Huldah, Allah ya ba da saƙo da ya la’anta wasu ayyukan addinai da ake yi a Yahuda. Duk da haka, an lura da ƙoƙarce-ƙoƙarcen Josiah na kawar da ayyukan bautar gumaka, kuma ya kasance cikin tagomashin Jehobah duk da masifu da aka annabta za su faɗa wa al’ummar gabaki ɗaya. (2 Laba. 34:19-28) Menene za mu iya koya daga wannan? Babu shakka muna da muradi irin na Josiah. Ya kamata mu bi ja-gorar Jehobah nan da nan, kuma mu yi tunanin abin da zai iya faruwa idan muka ƙyale ridda da rashin aminci su hana mu bauta wa Jehobah. Kuma za mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai amince da himmarmu don bauta ta gaskiya, kamar yadda ya yi da Josiah.

21, 22. (a) Me ya sa za mu nuna himma don bautar Jehobah? (b) Menene za a tattauna a talifi na gaba?

21 Waɗannan sarakuna huɗu na Yahuda, wato, Asa, Jehoshaphat, Hezekiah, da Josiah sun kafa mana misalai masu kyau wajen kasancewa da himma don gidan Allah da kuma bautarsa. Hakazalika, ya kamata himmarmu ta motsa mu mu dogara ga Jehobah kuma mu daɗa ƙoƙari don bautarsa. Hakika, tafarki na hikima ce da kuma hanyar samun farin ciki idan muka yi biyayya ga umurnin Allah kuma muka bi kulawa na ƙauna da gyara da muke samu a ikilisiya ta hanyar dattawa.

22 Talifi na gaba zai mai da hankalinmu ga himma don hidimar fage kuma zai ƙarfafa matasa su bauta wa Ubanmu da himma. Za mu kuma yi la’akari da yadda za mu guji ɗaya daga cikin rinjaya na lalata na Shaiɗan da ta fi muni. Yayin da muke yin biyayya ga dukan irin waɗannan tunasarwa daga Jehobah, za mu bi misalin Yesu, Ɗan Jehobah, wanda aka ce game da shi: “Himma domin gidanka ya cinye ni.”—Zab. 69:9; 119:111, 129; 1 Bit. 2:21.

Ka Tuna?

• Wace irin hidima ce Jehobah yake yi wa albarka, kuma me ya sa?

• Yaya za mu nuna mun dogara da Jehobah?

• Ta yaya himma za ta motsa mu mu yi biyayya ga umurnin Allah?

[Hotunan da ke shafi na 9]

Ta yaya Asa, Jehoshaphat, Hezekiah, da Josiah suka nuna himma don bautar Jehobah?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba