Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • th darasi na 15 p. 18
  • Ka Yi Magana Ba Shakka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Magana Ba Shakka
  • Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi Magana da Kuzari
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Ka Yi Kamar Kuna Tattaunawa
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Mutane Su Koyi Darasi Daga Jawabin
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Kammalawa Mai Dadi
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
Dubi Ƙari
Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
th darasi na 15 p. 18

DARASI NA 15

Ka Yi Magana Ba Shakka

Nassin da aka rubuta

1 Tasalonikawa 1:5

ABIN DA ZA KA YI: Ka nuna cewa maganarka gaskiya ce kuma tana da muhimmanci sosai.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka yi shiri sosai. Ka yi nazarin batun da kake son ka tattauna har sai ka ga yadda Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa batun gaskiya ne. Ka bayyana muhimman batutuwan a hanya mai sauƙi. Ka mai da hankali ga yadda masu sauraronka za su amfana. Ka roƙi Allah ya ba ka ruhu mai tsarki.

    Shawara mai amfani

    Idan ka gama shirya jawabinka, ka furta shi da baki ba a zuciyarka ba. Hakan zai sa ka saba da batun, kuma jawabinka zai yi daɗi.

  • Ka yi amfani da kalmomin da za su nuna cewa ba ka shakkar abin da kake faɗa. Maimakon ka yi amfani da kalmomi yadda suke a rubuce a cikin littafi, ka yi magana daga zuciyarka. Ka yi amfani da kalmomin da suka nuna cewa ka tabbata da abin da kake cewa.

  • Ka nuna cewa ka yarda da abin da kake faɗa. Ka ɗaga muryarka daidai yadda masu sauraronka za su ji ka sosai. Ka riƙa kallon masu sauraronka idan ana hakan a yankin.

    Shawara mai amfani

    Yin magana da tabbaci ba ya nufin cusa wa mutane ra’ayoyinmu ko tilasta musu su yi abin da muka faɗa. Yayin da kake magana da tabbaci, ka nuna cewa kana ƙaunar masu sauraronka.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba