Ba Wanda Zai Iya Bauta wa Iyayengiji Biyu
“Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu . . . Ba dama ku bauta wa Allah da dukiya gaba ɗaya.”—MAT. 6:24, Littafi Mai Tsarki.
1-3. (a) Wace irin matsalar kuɗi ce mutane da yawa suke fuskanta a yau, kuma ta yaya wasu suke ƙoƙarin magance ta? (Ka duba hoton da ke wannan shafin.) (b) Wace matsala ce iyaye suke samu game da renon yaransu sa’ad da suke so su je ƙasar waje neman aiki?
WATA ’yar’uwa mai suna Marya ta ce: “Mijina James yakan dawo daga aiki a gajiye kowace rana, amma albashinsa ba ya biyan bukatunmu na yau da kullum. Na so in rage ɗawainiyar kuma in saya wa ɗanmu wasu abubuwa masu kyau da abokan makarantarsa suke da shi.” Har ila, Mary ta so ta taimaka wa danginta kuma ta yi tanadi don nan gaba. Abokanta da yawa sun tafi ƙasashen waje don neman kuɗi. Amma sa’ad da ta yi tunanin zuwa ƙasar waje, sai ta rasa na yi. Me ya sa?
2 Mary ta san cewa idan ta tafi ƙasar waje, hakan zai shafi iyalinta da take ƙauna da kuma ibadar da suke yi a kai a kai. Duk da haka, sai ta yi tunani cewa ai akwai waɗanda suka je ƙasar waje, kuma kamar iyalansu ba su daina bauta wa Jehobah ba. Amma ta sake yin tunanin yadda za ta yi rainon ɗanta Jimmy daga ƙasar waje. Shin za ta iya rainon ɗanta “cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa” ta wajen amfani da intane?—Afis. 6:4.
3 Mary ta nemi shawara daga wurin mutane. Mijinta ba ya so ta tafi, amma ya ce ba zai hana ta ba. Dattawa da kuma wasu a cikin ikilisiya sun ba ta shawara cewa kada ta tafi, amma wasu ’yan’uwa mata sun ce ta tafi kawai, sun daɗa da cewa: “Idan kina ƙaunar iyalinki, ya kamata ki je, ai za ki iya bauta wa Jehobah a can.” Mary ta yi shakkar ɗaukar wannan matakin, duk da haka, ta yi ban kwana da mijinta da kuma ɗanta sai ta tafi ƙasar waje neman aiki. Ta tabbatar musu cewa ba za ta daɗe ba.
HAKKIN KULA DA IYALI DA KUMA ƘA’IDODIN LITTAFI MAI TSARKI
4. Me ya sa mutane da yawa suke ƙaura, kuma wane ne yake kula da ’ya’yansu sa’ad da suka yi hakan?
4 Jehobah ba ya so bayinsa su kasance a cikin matuƙar talauci. Tun zamanin dā, bayin Jehobah sun ƙaura zuwa wasu wurare don su rabu da talauci. (Zab. 37:25; Mis. 30:8) Yakubu ya aiki ’ya’yansa zuwa ƙasar Masar su sayi abinci don kada su mutu da yunwa.b (Far. 42:1, 2) A yau ba rashin abinci ba ne yake sa mutane da yawa suke ƙaura. To, me ya sa? Bashi ne yakan sa mutane da yawa su yi haka. Wasu suna zama a inda samun abin biyan bukatar iyali na da wuya kuma suna so su kyautata rayuwar iyalinsu. Shi ya sa suke barin iyalinsu zuwa wani gari ko wata ƙasa neman aiki da ake biyan kuɗi mai tsoka. A yawancin lokaci, sukan bar wa iyayensu ko ’yan’uwansu ko kakanninsu ko kuma abokansu ’ya’yansu ƙanana don su kula musu da su. Ko da yake ba sa jin daɗin yin hakan, amma da yawa daga cikinsu suna ganin ba su da zaɓi.
5, 6. (a) Mene ne Yesu ya koya wa mutane game da samun farin ciki da kwanciyar rai? (b) Mene ne Yesu ya ce mabiyansa su yi addu’a a kai? (c) Ta yaya Jehobah yake yi mana albarka?
5 A zamanin Yesu, mutane da yawa talakawa ne. Wataƙila sun yi tunani cewa da sun kasance da farin ciki da kwanciya rai sosai da a ce suna da wadata. (Mar. 14:7) Amma Yesu bai so su dogara ga abubuwan da ba za su dawwama ba. Ya so su dogara ga Jehobah don shi ke tanadar da dukiya da za ta dawwama. A huɗubar da Yesu ya ba da bisa dutse, ya bayyana cewa dangantakarmu da Jehobah ce ke kawo farin ciki na gaske ba abin duniya ba.
6 A addu’ar da Yesu ya koya wa mabiyansa, ya ce mu yi addu’a don ‘abincin yini,’wato bukatunmu na yau da kullum, ba don wadata ba. Ya gaya wa waɗanda suke sauraronsa cewa: “Kada ku tara wa kanku dukiya a duniya, . . . amma ku tara wa kanku dukiya cikin sama.” (Mat. 6:9, 11, 19, 20) Ya kamata mu tabbata cewa Jehobah zai albarkace mu kamar yadda ya yi alkawari. Allah zai yi mana albarka ta wajen amincewa da mu da kuma tanadar mana da abubuwan da muke bukata. Hakika, ta wajen dogara ga Ubanmu Jehobah ne kawai za mu iya samun farin ciki, ba ta neman kuɗi ba.—Karanta Matta 6:24, 25, 31-34.
7. (a) Su waye ne Allah ya ɗanka wa hakkin kula da yara? (b) Me ya sa ya kamata uba da uwa su kasance tare don su yi rainon yaransu?
7 Biɗan adalcin Allah ya ƙunshi kula da iyalanmu kamar yadda Jehobah ya umurta. Alal misali, dokar da Allah ya ba da ta hannun Musa ta umurci iyaye su tarbiyyar da ’ya’yansu don su bauta wa Jehobah. Ya kamata Kiristoci da suke son su faranta wa Allah rai su yi hakan. (Karanta Kubawar Shari’a 6:6.) Iyaye ne Allah ya ba wa wannan hakkin ba kakanni ko kuma wasu ba. Sarki Sulemanu ya ce: ‘Ɗana, ka ji koyarwar ubanka, dokar uwarka kuma kada ka yar da ita.’ (Mis. 1:8) Jehobah yana so iyalai su kasance tare don hakan zai sa iyayen su koyar da ’ya’yansu kuma su ja-gorance su. (Mis. 31:10, 27, 28) Idan yara suna ganin yadda iyayensu suke magana game da Jehobah da kuma bauta masa, za su iya yin koyi da su.
SAKAMAKO DA BA A SO BA
8, 9. (a) Waɗanne canje-canje ne ake samu idan iyalai ba sa zama tare? (b) Wane mugun sakamako ne irin wannan yanayin yake jawowa?
8 Mutane da yawa da suke barin iyalinsu sun san cewa hakan zai haifar da wasu matsaloli. Amma ba sa sanin ainihi yadda wannan matakin zai shafi iyalinsu. (Mis. 22:3)c Da zarar Mary ta bar gida, sai ta soma kewar iyalinta. Mijinta da kuma ɗanta ma sun soma kewar ta. Yaronta mai suna Jimmy yakan yi mata wannan tambayar, “Me ya sa kika bar ni?” Mary ta ce za ta yi ’yan watanni ne kawai, amma ta yi shekaru kuma sai ta fahimci cewa wasu canje-canje suna faruwa a cikin iyalinta kuma ba ta ji daɗin haka ba. Ɗanta ba ya son faɗin ra’ayinsa kuma ya daina gaya mata abin da yake damunsa. Marylin ta ce, “Ya daina ƙauna ta.”
9 Idan iyaye da yara ba sa zama tare a matsayin iyali, hakan zai shafi halinsu da kuma ra’ayoyinsu game da nagarta da mugunta.d Idan yaran ƙanana ne kuma rabuwar na tsawon lokaci ne, hakan zai ƙara yi wa yaran lahani. Mary ta gaya wa ɗanta Jimmy cewa ta tafi neman kuɗi ne don ta taimake shi. Amma a ganin Jimmy, mahaifiyarsa ta yi watsi da shi. Da farko, ya yi kewar ta amma daga baya, idan ta ziyarce su ba ya son ganinta. Kamar yadda yake faruwa da yaran da iyaye suka bar su, Jimmy ya ji kamar ba ta cancanci ya yi mata biyayya kuma ya ƙaunace ta ba.—Karanta Misalai 29:15.
10. (a) Me zai faru idan iyaye suka riƙa ba wa ’ya’yansu kyauta maimakon su kasance tare da su? (b) Mene ne iyalai sukan rasa idan ba sa tare da yaransu?
10 Da yake wurin da Mary take zama yana da nisa daga inda Jimmy yake, ta nemi ta sa shi farin ciki ta wajen aika masa kuɗi da kuma wasu abubuwa. Amma ta fahimci cewa hakan yana ƙara raba tsakaninta da ɗanta da kuma koya masa ya riƙa ɗaukan abin duniya da muhimmanci fiye da iyali da kuma Jehobah. (Mis. 22:6) Jimmy yakan gaya mata “Kada ki dawo, ki riƙa aiko da abubuwa.” A nan ne ta ankara cewa ba za ta iya rainon ɗanta ta wajen aika wasiƙu ko magana ta waya ko kuma intane ba. Ta ce: “Ba za ka iya rungumar ɗanka ko kuma yi masa sumba ta Intane ba.”
11. (a) Idan mata da miji ba sa zama tare, ta yaya hakan yake shafan aurensu? (b) Ta yaya wata ’yar’uwa ta fahimci cewa tana bukata ta koma wajen iyalinta?
11 Dangantakar Mary da Jehobah ta raunana. Hakan ma ya faru da dangantakarta da mijinta da kuma ɗanta. Tana zuwa taro da kuma wa’azi yini guda ko kuma ƙasa da hakan a mako. Abin ya sa shugabanta a aiki ya so ya yi jima’i da ita amma ba ta yarda ba. Da yake Mary da mijinta ba sa kusa da juna kuma ba za su iya su bayyana wa juna matsalolin da suke fuskanta ba, sun kusan yin zina. Ko da yake ba su yi zina ba, amma Mary ta fahimci cewa ba za su iya biya wa juna bukata ta motsin rai da jima’i kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce ma’aurata su yi ba. Me ya sa? Domin ba sa zama tare. Ba za su iya keɓe lokaci don tattaunawa ko kuma yin wasu abubuwa tare kamar mata da miji ba. Ba za su iya nuna ‘ƙauna’ ko kuma biya wa juna hakkinsu na aure ba. (W. Waƙ. 1:2; 1 Kor. 7:3, 5) Ƙari ga haka, ba za su iya bauta wa Jehobah tare da ɗansu ba. Mary ta ce: “Sa’ad da na koya a wani taron gunduma cewa ibada ta iyali tana da muhimmanci idan muna so mu tsira a babban ranar Jehobah, sai na gane cewa ina bukata in koma wajen iyalina. Wajibi ne in soma kyautata dangantakata da Jehobah da kuma iyalina.”
SHAWARA MAI KYAU DA MARAR KYAU
12. Wace shawarar Littafi Mai Tsarki ce za a iya ba wa waɗanda ba sa zama tare da iyalansu?
12 Sa’ad da Mary ta yi shawarar komawa gida, wasu sun ba ta shawara mai kyau, wasu kuma marar kyau. Dattawan ikilisiyarta sun yaba mata don ta nuna bangaskiya da kuma gaba gaɗi. Amma wasu mutane sun gaya mata cewa kada ta koma gida don ba za ta sami aiki mai kyau ba. Sun ce mata: “Ai nan ba da daɗewa ba za ki dawo.” Bai kamata Kiristoci su yi irin wannan magana ba. Maimakon haka, ya kamata su shawarci ‘mata domin su yi ƙaunar mazajensu, su yi ƙaunar ’ya’yansu, su zama . . . masu-aiki a gidajensu,’ wato gidan mazajensu don “kada a saɓa maganar Allah.”—Karanta Titus 2:3-5.
13, 14. Me ya sa muna bukatar bangaskiya don mu guji bin ra’ayin danginmu? Ka ba da misali.
13 Mutane da yawa da suka bar iyalan don yin aiki a wani wuri sun girma da wannan al’adar cewa zumunci tsakanin dangi ya fi kome muhimmanci. Ya kamata Kirista ya kasance da bangaskiya sosai don ya guji bin irin al’adar nan da ba ta faranta wa Jehobah rai.
14 Ka yi la’akari da labarin Carin, ta ce: “Sa’ad da na haifi ɗanmu mai suna Don, ni da maigidana muna aiki a ƙasar waje kuma na soma nazarin Littafi Mai Tsarki. ’Yan danginmu suna zaton cewa zan tura Don garinmu don iyayena su yi rainonsa har lokacin da muka yi wadata.” Sa’ad da Carin ta nace cewa za ta yi rainon ɗanta Don da kanta, sai danginta da mijinta suka ce ita raguwa ce kuma suka yi mata ba’a. Carin ta ci gaba da cewa: “A gaskiya, a lokacin na yi tunani cewa ba laifi ba ne idan na tura Don wajen iyayena don su yi rainonsa na ’yan shekaru. Amma na fahimci cewa Jehobah ya ba mu hakkin rainon ɗanmu da yake mu iyayensa ne.” Sa’ad da Carin ta sake yin juna biyu kuma, sai mijinta da ba Mashaidi ba ya ce ta zubar da cikin. Da yake Carin ta yanke shawara mai kyau da farko, hakan ya ƙarfafa bangaskiyarta kuma ta sake yanke shawara da ya faranta wa Jehobah rai. Yanzu ita da mijinta da ’ya’yansu suna farin ciki cewa suna zama tare. Da a ce Carin ta tura yaranta garinsu don wasu su yi rainonsu, da ba haka sakamakon zai kasance ba.
15, 16. (a) Yaya aka yi rainon Vicky sa’ad da take ƙarama? (b) Me ya sa ba ta yarda iyayenta su yi rainon ’yarta ba?
15 Wata Mashaidiya mai suna Vicky ta ce: “Kakata ce ta yi raino na cikin ’yan shekaru yayin da ƙanwata ta zauna tare da iyayenmu. A lokacin da na koma zama da iyayenmu, ƙaunata a gare su ta ragu. Ƙanwata ba ta jinkirin bayyana musu ra’ayinta, tana rungumarsu kuma tana jin daɗin zumuncin da ke tsakaninsu. Amma ban kusaci iyayena ba kuma sa’ad da na girma ba na iya bayyana musu ra’ayina. Ni da ƙanwata mun yi musu alkawari cewa za mu kula da su sa’ad da suka tsufa. Amma zan fi yin haka don hakkina ne, ƙanwata kuma za ta fi yin haka ne don tana ƙaunarsu.
16 Vicky ta ce: “Yanzu mahaifiyata tana so in tura ’yata don ta yi rainon ta kamar yadda kakata ta yi raino na. Cikin ladabi na ƙi amincewa. Ina so ni da mijina mu yi rainon ’yarmu don ta ƙaunaci Jehobah. Ƙari ga haka, ba na son in ɓata dangantakata da ’yata a nan gaba.” Vicky ta koyi cewa yin nasara ya dangana ne kawai ga yin biyayya ga Jehobah da kuma ƙa’idodinsa fiye da abin duniya ko kuma ra’ayin danginmu. Yesu ya bayyana a fili cewa: “Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu,” wato bauta wa Allah da dukiya ba.—Mat. 6:24, LMT; Fit. 23:2.
JEHOBAH ZAI ALBARKACE MU IDAN MUKA DĀGE
17, 18. (a) Wane zaɓi ne Kiristoci suke da shi a koyaushe? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu amsa a talifi na gaba?
17 Ubanmu Jehobah ya yi mana alkawari cewa zai ba mu dukan abubuwan da muke bukata idan muka mai da Mulkin da kuma adalcinsa farko a rayuwarmu. (Mat. 6:33) Saboda wannan alkawarin, Kiristoci na gaskiya suna da zaɓi a koyaushe. Ko da muna fuskantar matsaloli masu wuya ne, Jehobah zai tanadar da “hanyar tsira” da ba zai bukaci saɓa wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba. (Karanta 1 Korintiyawa 10:13.) Idan muna ‘sauraron’ Jehobah kuma muna “dogara gare shi” ta wajen roƙonsa ya tanadar mana da hikima da ja-gora da kuma ta bin dokokinsa da ƙa’idodinsa, zai taimake mu. (Zab. 37:5, 7) Zai ga ƙoƙarin da muke yi kuma ya biya mana ainihin bukatunmu. Ƙari ga haka, zai yi mana “albarka.”—Ka duba Farawa 39:3.
18 Mene ne za mu iya yi don magance matsalar da rashin zama tare yake haifarwa? Waɗanne matakai ne za mu iya ɗauka don mu ciyar da iyalinmu ba tare da mun bar su ba? Kuma ta yaya za mu iya ƙarfafa wasu su yanke shawara mai kyau game da hakan? Talifi na gaba zai ba da amsoshin waɗannan tambayoyin.
a An canja wasu sunaye.
b ’Ya’yan Yakubu sun bar iyalansu na tsawon mako uku ko ƙasa da hakan ne kawai a kowace tafiyarsu Masar. Sa’ad da Yakubu da ’ya’yansa suka ƙaura zuwa Masar daga baya, sun yi hakan ne tare da matansu da kuma ’ya’yansu.—Far. 46:6, 7.
c Ka duba talifin nan “Immigration—Dreams and Realities” da ke mujallar Awake! ta February 2013 na Turanci.
d Rahotanni daga ƙasashe da yawa sun nuna cewa barin iyali zuwa ƙasar waje don aiki yana cikin abubuwan da ke haddasa matsaloli masu tsanani. Waɗannan sun haɗa da zina da luwaɗi da kuma jima’i tsakanin dangi. Ƙari ga haka, yara sukan sami matsaloli a makaranta kuma su riƙa saurin fushi da tsoro da baƙin ciki da son yin kisan kai.