Littattafan da Aka Ɗauko Bayanai Daga Cikinsu a Littafin Taro don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu
© 2023 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
6-12 GA NUWAMBA
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | AYUBA 13-14
“Idan Mutum Ya Mutu, Zai Sāke Rayuwa Kuwa?”
Yaƙin da ꞌYan Adam Suke Yi da Mutuwa
Sarakunan ƙasar Sin ma sun yaƙi mutuwa, amma sun yi hakan ta wajen amfani da magungunan da suke ganin za su iya hana mutuwa. Wani sarki mai suna Qin Shi Huang, ya sa masu harhaɗa masa magani su yi masa haɗin da zai iya raba shi da mutuwa. Amma, haɗe-haɗensu da dama sun ƙunshi gubar ƙarfe, kuma wataƙila ɗaya daga cikin haɗe-haɗen ne ya zama sanadin mutuwarsa.
A shekara ta 1513, Juan Ponce de León, wani ɗan Sifen mai bincike, ya yi tafiya a faɗin tsibirai da ke kudancin Amirka yana neman maɓulɓular da ke mai da mutum matashi. Yayin da yake wannan tafiyar, ya gano wata jiha da ake kira Florida a Amirka, amma bayan wasu ꞌyan shekaru, ya mutu sanadiyyar yaƙin da ya ɓarke tsakanin shi da mutanen jihar. Har wa yau, ba a gano maɓulɓula da ke mai da mutum matashi ba.
Idan Aka Sare Bishiya, Tana Iya Sake Tohuwa Kuwa?
CEDAR wato, bishiyar alꞌul ta ƙasar Lebanon, bishiya ce mai girma sosai da kuma ban shaꞌawa. Akasin haka, bishiyar zaitun ba ta girma sosai kuma ba ta kai bishiyar alꞌul kyau ba. Amma an san bishiyar zaitun da dauriya a yanayi dabam-dabam. Wasu suna kai wajen shekara 1,000. Bishiyar zaitun tana da jijiyoyi masu shiga ƙasa sosai kuma hakan yakan sa ta sake tohuwa bayan an datse bishiyar. Muddin jijiyoyin ba su mutu ba, za su sake tohuwa.
Uban iyali Ayuba ya tabbata cewa idan ya mutu, zai sake rayuwa. (Ayu. 14:13-15) Ya yi amfani da bishiya, wataƙila bishiyar zaitun wajen nuna tabbaci da yake da shi cewa Allah zai ta da shi bayan ya mutu. Ayuba ya ce: ‘Ana sa zuciya gareshi [itace] ya sake tohuwa.’ ‘Gama icen da an datse . . . zai sake tohuwa.’ Idan aka yi ruwan sama bayan fāri mai tsawo, kututturen bishiyar zaitun zai iya sake tohuwa kuma ya yi rassa.—Ayu. 14:7-9.
“Za Ka Yi Marmari”
Kalmomin Ayuba sun koya mana cewa Jehobah mai ƙauna ne: Kamar yadda Ayuba ya yi, Jehobah yana ƙaunar waɗanda suka miƙa kansu ga hannunsa, waɗanda suke ƙyale shi ya mulmula su su zama mutane masu daraja a idanunsa. (Ishaya 64:8) Jehobah yana ɗaukan bayinsa masu aminci da tamani. Ga masu aminci da suka mutu, yana da “marmari.” Kalmar Ibrananci da aka fassara “babu shakka tana ɗaya daga cikin kalmomi mafi ƙarfi sosai da ake amfani da su wajen nuna ɗoki,” in ji wani masani. Hakika, Jehobah yana tunawa da masu bauta masa kuma yana ɗokin ta da su daga matattu.
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
it-2-E 905
SHADOW
The way in which a shadow changes in size and finally is no more as a result of the sun’s progress is used as a simile of man’s being short-lived or transient. (1Ch 29:15; Job 8:9; 14:1, 2; Ps 102:11; 144:4; Ec 6:12; 8:13) For an individual’s days to be “like a shadow that has declined” signifies that his death is near. (Ps 102:11; 109:23) Whereas shadows cast by the sun are always changing in size and direction as the earth rotates, Jehovah is unchangeable. As the disciple James wrote: “With him there is not a variation of the turning of the shadow.”—Jas 1:17.
13-19 GA NUWAMBA
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | AYUBA 15-17
“Kada Ku Yi Koyi da Elifaz Saꞌad da Kuke Taꞌazantar da Mutane”
Ka Ci Gaba da Ƙarfafa Begenka
10 Begenmu zai taimaka mana mu guji yin tunani cewa ba za mu iya faranta wa Allah rai ba. Alal misali, wasu za su iya cewa: ‘Ba zan iya samun rai na har abada ba domin ban cancanta ba. Ba zan taɓa iya yin abubuwan da Allah ya ce in yi ba.’ Ka tuna cewa abin da abokin Ayuba na ƙarya, wato Eliphaz ya gaya wa Ayuba ke nan. Eliphaz ya ce: “Wane ɗan Adam ne zai iya kasance marar laifi?” Ya kuma ce game da Jehobah: “Allah bai ma amince da halittunsa masu tsarki ba, ko sammai ma ba su kasance marasa laifi a gabansa ba.” (Ayu. 15:14, 15) Wannan ƙarya ne ba kaɗan ba! Ka tuna cewa Shaiɗan ne yake so ka yi tunani kamar haka. Ya san cewa idan ka ci gaba da yin tunani kamar haka, za ka rasa begenka. A maimakon haka, ka guji irin ƙaryar nan kuma ka mai da hankali ga alkawuran da Allah ya yi. Kada ka yi shakkar cewa yana so ka yi rayuwa har abada kuma zai taimaka maka ka iya yin hakan.—1 Tim. 2:3, 4.
Ka Kasance da Tawaliꞌu da Tausayi Kamar Yesu
16 Mu yi magana mai daɗin ji. Idan muna tausayin mutane, za mu “ƙarfafa masu-raunanan zukata.” (1 Tas. 5:14) Mene ne za mu faɗa don mu ƙarfafa irin waɗannan masu baƙin ciki? Za mu iya ƙarfafa su ta wajen nuna cewa mun damu da su da gaske. Za mu iya yaba musu don mu taimaka musu su ga halayensu masu kyau. Za mu iya tuna musu cewa Jehobah ya jawo su zuwa wajen Ɗansa, saboda haka, suna da mutunci a gabansa. (Yoh. 6:44) Za mu iya tabbatar musu cewa Jehobah yana ƙaunar bayinsa “masu-karyayyar zuciya” ko kuma “ruhu mai-tuba.” (Zab. 34:18) Kalamanmu masu daɗin ji zai iya ƙarfafa masu baƙin ciki.—Mis. 16:24.
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
Darussa Daga Littafin Ayuba
7:9, 10; 10:21; 16:22—Waɗannan furcin na nuna cewa Ayuba bai gaskata da tashin matattu ba ne? Ayuba ya yi waɗannan kalamai game da mutuwarsa ne. To, menene yake nufi? Wataƙila yana nufin cewa idan ya mutu, zuriyarsa ba za su gan shi kuma ba. A raꞌayinsu, ba zai dawo gidansa ba ko kuma a san da shi har sai lokacin da Allah ya kaꞌide. Mai yiwuwa Ayuba yana nufin cewa babu wanda zai iya dawowa daga Sheol da kansa. Ayuba 14:13-15 sun nuna sarai cewa Ayuba yana da begen tashin matattu na nan gaba.
20-26 GA NUWAMBA
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | AYUBA 18-19
“Kada Ku Yi Watsi da Waɗanda Kuke Ibada Tare”
Darussan da Za Mu Iya Koya Daga Hawayen Yesu
9 Za ka iya taimaka ma waɗanda suke baƙin ciki. Yesu bai yi kuka kawai tare da Marta da Maryamu ba, amma ya saurare su kuma ya ƙarfafa su. Mu ma za mu iya yin hakan ga waɗanda suke baƙin ciki. Wani dattijo mai suna Dan a Ostareliya ya ce: “Bayan rasuwar matata, na bukaci taimako sosai. ꞌYanꞌuwa maꞌaurata da yawa sun kasance tare da ni dare da rana don su saurare ni. Sun bar ni in faɗi yadda nake ji kuma ba su ji kunya saꞌad da nake kuka ba. Sun kuma taimaka mini a hanyoyi dabam-dabam, kamar taya ni wanke motata da taya ni cefane, da kuma dafa abinci a lokutan da na kasa yin hakan. Ƙari ga haka, sukan yi adduꞌa tare da ni. Sun nuna mini cewa su abokaina ne na ƙwarai, da ꞌyanꞌuwa da ke ba da ‘taimako a kwanakin masifa.’”—K. Mag. 17:17.
Abin da Za Ka Yi Idan Wani a Iyalinku Ya Bar Jehobah
16 Ka ci gaba da taimaka wa iyalin waɗanda aka yi wa yankan zumunci da suke bauta wa Jehobah da aminci. A yanzu ne suka fi bukatar ka nuna kana ƙaunar su kuma ka ƙarfafa su. (Ibran. 10:24, 25) A wasu lokuta, ꞌyanꞌuwan waɗanda aka yi wa yankan zumunci sun lura cewa, wasu ꞌyanꞌuwa a ikilisiya sun daina cuɗanya da su sai ka ce su ma an yi musu yankan zumunci. Ba zai dace mu sa su ji hakan ba! Matasa musamman waɗanda iyayensu suka daina bauta wa Jehobah suna bukatar a riƙa yaba musu da kuma ƙarfafa su. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Maria da aka yi wa mijinta yankan zumunci kuma ya bar ta da yaransu, ta ce: “Wasu a cikin abokaina sun zo gidanmu, suka dafa mana abinci kuma suka yi nazari da yarana. Sun nuna sun damu da ni kuma sun yi kuka tare da ni. Sun kāre ni saꞌad da mutane suka soma faɗan abubuwan da ba gaskiya ba game da ni. Hakika, sun ƙarfafa ni sosai!”—Rom. 12:13, 15.
w90-E 9/1 22 sakin layi na 20
Are You Reaching Out?
20 A body of elders should realize that deletion may cause stress for a former overseer or ministerial servant, even if he voluntarily gives up the privilege. If he is not disfellowshipped, but the elders see that the brother is depressed, they ought to provide loving spiritual assistance. (1 Thessalonians 5:14) They should help him to realize that he is needed in the congregation. Even if counsel has been required, it may not be such a long time before a humble and grateful man again receives added privileges of service in the congregation.
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
w94-E 10/1 32
The Power of a Kind Word
However, when Job himself needed encouragement, Eliphaz and his companions did not utter kind words. They blamed Job for his adversity, implying that he must have had some secret fault. (Job 4:8) The Interpreter’s Bible comments: “What Job needs is the compassion of a human heart. What he gets is a series of absolutely ‘true’ and absolutely beautiful religious clichés and moral platitudes.” So distraught was Job at hearing the speech of Eliphaz and his companions that he was compelled to cry out: “How long will you men keep irritating my soul and keep crushing me with words?”—Job 19:2.
Never should we cause a fellow servant of God to cry out in distress because of our thoughtless, unkind words. (Compare Deuteronomy 24:15.) A Bible proverb warns: “What you say can preserve life or destroy it; so you must accept the consequences of your words.”—Proverbs 18:21, TEV.
27 GA NUWAMBA–3 GA DISAMBA
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | AYUBA 20-21
“Ba Arziki Ne Ke Nuna Amincin Mutum Ba”
Kai ‘Mawadaci Ne Ga Allah’?
12 A furcin Yesu, an bambanta zama mawadaci ga Allah da mutum ya tara wa kansa dukiya, ko kuma ya zama mai arziki. Da haka, Yesu yana cewa ne bai kamata tara dukiya ko kuma jin daɗin abin da muka tara ya zama ainihin damuwarmu a rayuwa ba. Maimakon haka, ya kamata mu yi amfani da dukiyarmu mu kyautata ko kuma mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah. Yin hakan zai sa mu zama mawadaci ga Allah. Me ya sa? Domin zai sa mu sami albarka da yawa daga wajensa. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Albarkar Ubangiji ta kan kawo wadata, ba ya kan haɗa ta da baƙinciki ba.”—Misalai 10:22.
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
w95 1/1 20 sakin layi na 19
Yin Nasara Bisa Shaitan Da Ayukansa
19 Abin marmari ne cewa bawan Allah Ayuba ya jure da “tunanin” da Shaitan ya gabatar ta wurin Eliphaz da Zophar. (Ayuba 4:13-18; 20:2, 3) Ayuba ya ji ‘zafin rai,’ wadda ya kai shiga “magana da rashin hankali” game da “razana” da ke damun zuciyarsa. (Ayuba 6:2-4; 30:15, 16) Elihu ya saurara sarai ga Ayuba kuma taimake shi ya ga raꞌayin Jehovah mafi-hikima na alꞌamura. Hakanan ma yau, dattiɓai masu-ganewa za su nuna kulawarsu ga waɗanda suke shan wahala ta wurin ƙin daɗa ga “nauyi” na waɗannan. Maimako fa, kamar Elihu, za su saurara da hanƙuri garesu kuma yi amfani da mai mai-dacewa na Kalmar Allah. (Ayuba 33:1-3, 7; Yaƙub 5:13-15) Don haka duk wanda ciwon zuci ya taɓe jiye-jiyensa, na gaske ne ko kuwa mafalkin zaune, ko wanda ya “firgita . . . da mafalkai, . . . da ruꞌyai” kamar Ayuba, zai iya samun taꞌaziya na Nassi cikin ikklisiya.—Ayuba 7:14; Yaƙub 4:7.
4-10 GA DISAMBA
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | AYUBA 22-24
“Zai ‘Yiwu Mutum Ya Zama da Amfani ga Allah?’”
Yadda Za Mu Kasance da Raꞌayi Mai Kyau
2 Duk da dukan waɗannan albarkar da Jehobah ya yi mana, wasu bayin Jehobah suna baƙin ciki. Suna iya ji cewa Jehobah ba ya daraja su da kuma hidimarsu. Mutanen da suke da irin wannan raꞌayin za su iya ji cewa more “shekaru da yawa” wasiƙar jaki ce. Sun ji cewa babu wani batun jin daɗi a rayuwa.—M. Wa. 11:8.
3 Rashin lafiya ko taƙaici ko kuma tsufa zai iya sa wasu ꞌyanꞌuwa baƙin ciki. (Zab. 71:9; Mis. 13:12; M. Wa. 7:7) Bugu da ƙari, dole ne kowane Kirista ya fahimci cewa zuciya tana da rikici kuma tana iya sa mu ji cewa ba ma faranta wa Jehobah rai ko da muna yin abu mai kyau. (Irm. 17:9; 1 Yoh. 3:20) Shaiɗan yana yaɗa ƙarya game da bayin Allah kuma waɗanda suke koyi da Shaiɗan za su iya sa mu kasance da irin raꞌayin Eliphaz marar bangaskiya wanda ya ce ba mu da daraja a gaban Jehobah. Hakan ƙarya ce a zamanin Ayuba da kuma a yau.—Ayu. 4:18, 19.
4 Jehobah ya bayyana a cikin Kalmarsa dalla-dalla cewa zai kasance tare da waɗanda suke fama da baƙin ciki. (Zab. 23:4) Wata hanya da yake kasance tare da mu ita ce ta Kalmarsa. Littafi Mai Tsarki yana da iko daga ‘Allah don rushe makamai masu ƙarfi.’ Hakan yana nufin cewa zai iya canja raꞌayi marar kyau da muke da shi game da kanmu. (2 Kor. 10:4, 5, Littafi Mai Tsarki) Yanzu, bari mu tattauna yadda Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu kasance da raꞌayi mai kyau. Za ka iya amfana daga hakan kuma zai iya sa ka ƙarfafa wasu.
ijwia talifi na 4 sakin layi na 16
“Ba Zan Daina Tsare Mutuncina Ba!”
Bayan mutanen nan sun ce Ayuba bai da aminci da gaske, sun yi daꞌawar cewa kasancewa da aminci a gaban Allah bai da amfani. Da Elifaz ya fara maganarsa, ya ce ya gamu da wani ruhu. Wannan aljanin ya sa Elifaz ya kasance da raꞌayin nan cewa Allah ‘bai amince da bayinsa ba, yana kuma samun malaꞌikunsa da laifi.’ Idan hakan gaskiya ne, ꞌyan Adam ba za su taba iya faranta wa Allah rai ba. Wannan raꞌayin yana da illa sosai domin zai iya sa mutum ya daina kasancewa da bangaskiya. Daga baya, Bildad ya ce Allah bai damu da amincin Ayuba ba, kamar yadda ba zai kula da amincin tsutsa ba.—Ayuba 4:12-18; 15:15; 22:2, 3; 25:4-6.
w03 5/1 5-6 sakin layi na 10-12
Matasa Da Suke Faranta Wa Jehovah Zuciya
10 Yadda yake a bayyane cikin labarin Littafi Mai Tsarki, Shaiɗan ya tuhumi ba kawai amincin Ayuba ba amma kuma na dukan wasu da suke bauta wa Allah—har da kai. Hakika, da yake magana game da galibin mutane, Shaiɗan ya ce wa Jehovah: “Dukan abin da mutum [ko waye, ba Ayuba kawai ba] ya ke da shi, ya bayar a bakin ransa.” (Ayuba 2:4) Ka ga matsayinka a wannan batu mai muhimmanci? Yadda aka nuna a Misalai 27:11, Jehovah yana cewa ne da akwai abin da za ka ba shi—dalili da zai sa ya sami amsa wa mai zargi, Shaiɗan. Ka duba—Mamallakin Dukan Halitta yana kiranka ka sa hannu a ba da amsa ga wannan batu mafi girma gabaki ɗaya. Dubi yadda wannan yake hakki mai girma kuma gatar taka ce! Za ka iya cika abin da Jehovah yake biɗa a gare ka? Ayuba ya yi hakan. (Ayuba 2:9, 10) Haka ma Yesu da wasu da yawa cikin tarihi suka yi, har da matasa da yawa. (Filibbiyawa 2:8; Ruꞌya ta Yohanna 6:9) Za ka iya yin haka nan. Kada ka yi kuskure, babu tsaka-tsaki cikin wannan batun. Ta wurin halayenka, za ka nuna ko kana goyon bayan zargin Shaiɗan ko kuma amsar Jehovah. Wanene za ka zaɓa ka bi?
Jehovah Yana Kula da Kai!
11 Jehovah yana damuwa ne game da zaɓen da kake yi? Mutane da yawa ba sun riga sun riƙe amincinsu gare shi domin ya iya ba da amsa ga Shaiɗan ba ne? Hakika, Iblis ya yi daꞌawar cewa babu wanda yake bauta wa Jehovah domin ƙauna amma an ƙaryata wannan zargin. Duk da haka, Jehovah yana son ka kasance a gefensa na batun ikon mallaka domin yana kula da kai ainihinka. Yesu ya ce: “Ba nufin Ubanku wanda ke cikin sama ba ne, guda ɗaya daga cikin waɗannan ƙanƙanana shi lalace.”—Matta 18:14.
12 A bayyane yake cewa Jehovah yana damuwa da tafarkin da ka zaɓa. Fiye da haka ma, yana shafansa. Littafi Mai Tsarki ya bayyana sarai cewa Jehovah yana da juyayi ƙwarai a kan halayen kirki ko kuma na mugunta da mutane suke yi. Alal misali, da Israꞌilawa suka riƙa tawaye, sun ‘ɓata’ wa Jehovah rai. (Zabura 78:40, 41) Kafin Rigyawan zamanin Nuhu, yayin da “muguntar mutum ta yi yawa,” ya ‘ɓata’ wa Jehovah rai. (Farawa 6:5, 6) Ka yi tunanin abin da wannan yake nufi. Idan ka bi mummunar tafarki, kana iya ɓata wa Mahaliccinka rai. Wannan ba ya nufin cewa Allah kumami ne ko kuma wanda motsin rai ke rinjayarsa. Maimakon haka, yana ƙaunarka ne kuma ya damu da lafiyarka. A wata sassa kuma, idan ka yi abin da ke daidai, Jehovah yana farin ciki. Yana farin ciki ba domin ya sake samun wata amsa ga Shaiɗan ba amma kuma domin zai iya zama Mai Saka maka. Abin da yake son ya yi ke nan. (Ibraniyawa 11:6) Hakika Uba mai ƙauna kake da shi, Jehovah Allah!
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
w04-E 7/15 sakin layi na 21-22
Use Spiritual Goals to Glorify Your Creator
Consider how Jehovah accomplished the creation of the universe. With the words “there came to be evening and there came to be morning,” Jehovah marked off the successive periods of creation. (Genesis 1:5, 8, 13, 19, 23, 31) At the beginning of each creative time period, he well knew his goal, or objective, for that day. And God carried out his purpose to create things. (Revelation 4:11) “[Jehovah’s] own soul has a desire, and he will do it,” said the patriarch Job. (Job 23:13) How satisfying it must have been for Jehovah to see “everything he had made” and declare it “very good”!—Genesis 1:31.
For our goals to become a reality, we too must have a strong desire to achieve them. What will help us develop such an intense desire? Even while the earth was formless and waste, Jehovah could foresee the end result—a beautiful jewel in space, bringing him glory and honor. Similarly, our desire to accomplish what we set out to do can be cultivated by meditating on the results and benefits of achieving the goal. That was the experience of 19-year-old Tony. He never forgot his first impression of a visit to a branch office of Jehovah’s Witnesses in Western Europe. From then on, the question that occupied Tony’s mind was, ‘What would it be like to live and serve in a place like that?’ Tony never stopped thinking about the possibility, and he continued to reach out for it. How happy he was when several years later his application to serve at the branch was approved!
11-17 GA DISAMBA
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | AYUBA 25-27
“Kasancewa da Aminci Ba Ya Nufin Mutum Zai Zama Kamili”
w09 4/15 3-4 sakin layi na 3-7
Ayuba Ya Ɗaukaka Sunan Jehobah
3 Ayuba mutum ne mai wadata kuma mai tasiri, uban iyali mai halaye masu kyau. Babu shakka shi mai kula da mabukata ne. Mafi muhimmanci, Ayuba yana tsoron Allah. An kwatanta Ayuba a matsayin mutumi “kamili . . . mai-adilci, yana tsoron Allah, yana kuwa bada baya ga mugunta.” Ba wadatar Ayuba da ikonsa ba ne ya sa ya zama abin farmaki ga Shaiɗan Iblis, amma ibadarsa ga Allah ce ta sa.—Ayu. 1:1; 29:7-16; 31:1.
4 Littafin Ayuba ya fara ne da ba da bayani game da taron da aka yi a sama saꞌad da malaꞌiku suka tsaya a gaban Jehobah. Shaiɗan ma ya halarci taron, kuma a nan ne ya zargi Ayuba. (Karanta Ayuba 1:6-11.) Ko da yake Shaiɗan ya ambata wadatar Ayuba, ya mai da hankalinsa ne ga ƙalubalantar amincinsa. Kalmar nan “aminci” tana nufin mutunci, marar aibi, adali, da kuma marar kuskure. Kamar yadda yake a cikin Littafi Mai Tsarki, amincin ꞌyan adam yana nufin bauta wa Jehobah da dukan zuciya.
5 Shaiɗan ya yi daꞌawar cewa Ayuba yana bauta wa Allah saboda son kai, ba don nagarta ba. Shaiɗan ya yi zargi cewa Ayuba zai kasance da aminci ga Jehobah ne kawai idan Allah ya ci gaba da ba shi arziki da kāriya. Don amsa zargin da Shaiɗan ya yi, Jehobah ya ƙyale Shaiɗan ya jarraba wannan mutumi mai aminci. A sakamakon hakan, cikin kwana ɗaya, Ayuba ya sami labari cewa an sace ko kuma kashe dabbobinsa, an kashe yawancin bayinsa, kuma yaransa guda goma sun rasa rayukansu. (Ayu. 1:13-19) Wannan hari na Shaiɗan ya sa Ayuba sanyin gwiwa ne? Hurarren labarin ya kwatanta abin da Ayuba ya ce game da balaꞌin: “Ubangiji ya bayas, Ubangiji ya karɓa, albarka ga sunan Ubangiji.”—Ayu. 1:21.
6 Daga baya, an sake yin wani taro a sama. Shaiɗan ya sake jefa wasu zargi game da Ayuba, ya ce: “Ai, fata a bakin fata, hakika dukan abin da mutum ya ke da shi, ya bayar a bakin ransa. Miƙa hannunka yanzu kaɗai, ka taɓa ƙashinsa da namansa, sai shi laꞌanta ka a fuskarka.” Ka lura cewa Shaiɗan ya faɗaɗa zarginsa. Ta cewa, ‘Dukan abin da mutum yake da shi, ya bayar a bakin ransa,’ Iblis ya ƙalubalanci amincin duk ‘mutumin’ da ke bauta wa Jehobah ba Ayuba kaɗai ba. Bayan hakan, Jehobah ya ƙyale Shaiɗan ya bugi Ayuba da ciwo. (Ayu. 2:1-8) Amma gwajin da Ayuba ya fuskanta bai tsaya a nan ba.
7 A farkon gwajin, matar Ayuba ta fuskanci irin wahalar da mijinta ya fuskanta. Rashin ꞌyaꞌyanta da kuma wadatarsu ya sa ta baƙin ciki sosai. Ta yi baƙin cikin ganin mijinta yana shan wahala domin ciwo mai tsanani. Ta yi wa Ayuba kuka: “Har yanzu kana riƙe da gaskiyarka? Ka laꞌanta Allah, ka mutu.” Bayan haka, Eliphaz, Bildad, da Zophar suka iso wurinsa, da sunan yi masa taꞌaziyya. Maimakon haka, sun yi amfani da tunanin ruɗu kuma suka zama “masu-taꞌaziya na ban takaici.” Alal misali, Bildad ya faɗi cewa ꞌyaꞌyan Ayuba sun yi zunubi ne shi ya sa suka mutu. Eliphaz kuma ya ce wahalar da Ayuba yake sha horo ne na zunuban da ya yi a dā. Har cewa ya yi wai waɗanda suke da aminci ba su da daraja a gaban Allah! (Ayu. 2:9, 11; 4:8; 8:4; 16:2; 22:2, 3) Duk da irin wannan mugun matsin, Ayuba ya kasance da aminci. Hakika, bai yi daidai ba saꞌad da ya ce “ya fi Allah gaskiya.” (Ayu. 32:2) Duk da haka, ya kasance da aminci har ƙarshe.
17 Menene ya taimaka wa Ayuba ya riƙe amincinsa? Babu Shakka, kafin balaꞌin ya faɗa masa, ya riga ya ƙulla dangantaka na kud da kud da Jehobah. Ko da yake ba mu da shaidar da ta nuna cewa ya san cewa Shaiɗan ya ƙalubalanci Jehobah, Ayuba ya ƙudurta kasancewa da aminci. Ya ce: “Har in mutu ba ni rabuwa da gaskiyata.” (Ayu. 27:5) Yaya Ayuba ya ƙulla wannan dangantaka na kud da kud? Babu shakka, ya daraja abubuwan da ya ji game da yadda Allah ya bi da Ibrahim, Ishaƙu, da Yakubu, waɗanda danginsa ne na nesa. Kuma ta wajen lura da halitta, Ayuba ya fahimci halayen Jehobah da yawa.—Karanta Ayuba 12:7-9, 13, 16.
Ka Riƙe Amincinka!
3 Ta yaya bayin Allah suke nuna aminci? Suna yin hakan ta wurin ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarsu, kuma hakan yana sa su yi abin da yake faranta masa rai. Ka yi laꞌakari da yadda ake amfani da kalmar nan a cikin Littafi Mai Tsarki. Kalmar nan aminci tana nufin cikakkiya ko marar aibi ko kuma abin da aka ba da gabaki ɗaya. Alal misali, Israꞌilawa sun miƙa hadayun dabobbi ga Jehobah kuma a Dokar, an ce ya kamata dabbar ta kasance cikakkiya ko lafiyayya. (L. Fir. 22:21, 22) Ba a karɓan dabbar da ta gurgunce ko ta makance ko kuma ba ta da kunne ɗaya. Kuma ba a yin hadaya da dabba mai rashin lafiya. Jehobah yana bukatar dabbar ta zama cikakkiya ko lafiyayya ko kuma marar aibi. (Mal. 1:6-9) Hakan ya sa mun fahimci abin da ya sa Jehobah yake son mu miƙa cikakkiyar hadaya. Idan muna so mu sayi wani abu, wataƙila ꞌyaꞌyan itatuwa ko littafi ko kuma wani kayan aiki, mukan sayi mai kyau ba mai huji ba ko kuma wanda ya rasa wasu sassa ba. Muna son abu cikakke ko lafiyayye ko kuma marar aibi. Hakazalika, Jehobah yana so mu riƙa ƙaunar sa da dukan zuciyarmu ko kuma mu riƙe amincinmu a gare shi. Wajibi ne hadayarmu ta zama cikakkiya ko marar aibi.
4 Ya kamata ne mu yi tunani cewa wajibi ne mu zama kamiltattu kafin mu riƙe aminci? Muna iya ganin cewa muna yin kuskure da yawa. Amma, ka yi laꞌakari da dalilai biyu da ya sa ba ma bukatar mu riƙa jin tsoro. Na farko, Jehobah ba ya mai da hankali ga kurakuranmu. Kalmarsa ta ce: “Ya Ubangiji, idan kana lissafa laifofi, wa zai tsaya?” (Zab. 130:3) Jehobah ya san cewa mu ajizai ne kuma mu masu zunubi ne, saboda haka yakan gafarta mana zunubanmu. (Zab. 86:5) Na biyu, Jehobah ya san kasawarmu, kuma ba ya sa mu yi abin da ya fi ƙarfinmu. (Karanta Zabura 103:12-14.) Saboda haka, ta yaya za mu zama cikakku ko marar aibi a gaban Jehobah?
5 Abin da zai taimaka wa bayin Jehobah su riƙe aminci shi ne nuna ƙauna. Wajibi ne mu riƙa ƙaunar Allah da bauta masa da aminci da dukan zuciyarmu. Mu masu aminci ne idan muna ƙaunar Allah sosai har a lokacin da muke fuskantar gwaji. (1 Tar. 28:9; Mat. 22:37) Ka sake yin laꞌakari da Shaidu uku da aka ambata ɗazu. Me ya sa suka kasance da aminci? Shin yarinyar ba ta son shaƙatawa ne a makaranta ko kuma matashin yana son a riƙa masa baꞌa ne? Mutumin nan kuma fa, yana so ya rasa aikinsa ne? Aꞌa. Maimakon haka, sun san cewa Jehobah ya kafa ƙaꞌidodi masu kyau, kuma sun mai da hankali ga yin abin da yake faranta masa rai. Domin suna ƙaunar sa, sukan sa shi farko a duk shawarwarin da suke yi. Ta hakan suna nuna cewa su masu aminci ne.
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
Abin da Ke Sa Mu Bauta wa Allah Cikin Tsari
3 Abubuwan da Allah ya halitta sun nuna cewa shi Mai tsari ne sosai. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji bisa ga hikima ya kafa duniya: Bisa ga fahimi kuma ya ƙarfafa sammai.” (Mis. 3:19) Abubuwan da muka sani “kaɗan ne kawai daga cikin alꞌamuran [Allah]. Ɗan ƙis kaɗai muke ji a kansa.” (Ayu. 26:14, Littafi Mai Tsarki) Duk da haka, wannan ɗan ilimin da muke da shi a kan duniyoyi da kuma damin-damin taurarin da ke sama sun nuna mana cewa halittun Allah suna da tsari ba kaɗan ba. (Zab. 8:3, 4) Kowane damin taurari yana ɗauke da miliyoyin taurarin da suke tafiya bisa ga tsari. Duniyoyin da suke kewaye rana suna bin tsarin da aka kafa musu kamar dai suna biyayya ne ga dokokin hanya! Hakika, yadda aka tsara sama da ƙasa ya nuna cewa Jehobah, wanda ya yi duniya da kuma “sammai bisa ga fahimi” ya cancanci mu ba shi yabo da ɗaukaka da girma.—Zab. 136:1, 5-9.
18-24 GA DISAMBA
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | AYUBA 28-29
“Kana da Hali Irin na Ayuba?”
Ka Nuna Ƙauna Ta Alheri Ga Waɗanda Suke Da Bukata
19 Labaran Littafi Mai Tsarki da muka tattauna sun nuna cewa ƙauna ta alheri ya kamata a nuna ta ga waɗanda suke da bukatar da ba za su iya biyanta ba da kansu. Domin ya ci gaba da zuriyarsa, Ibrahim yana bukatar haɗin kan Bethuel. Domin a kai gawarsa Kanꞌana, Yakubu yana bukatar taimakon Yusufu. Kuma domin ta samu magaji, Naomi tana bukatar taimakon Ruth. Babu wanda zai iya cika waɗannan bukatar ba tare da taimako ba tsakanin Ibrahim, Yakubu da kuma Naomi. Hakanan a yau, ƙauna ta alheri ya kamata a nuna ta, musamman ga waɗanda suke da bukata. (Misalai 19:17) Muna bukatar mu yi koyi da uban iyali Ayuba, wanda yake mai da hankalinsa ga “talakan da ya yi kuka, maraya kuma wanda ba shi da mai-taimakonsa” har da wanda “ya ke bakin mutuwa.” Ayuba kuma ya ‘faranta wa gwauruwa rai’ kuma ya zama ‘ido ga makaho sawu kuma ga gurgu.’—Ayuba 29:12-15.
it-1-E 655 sakin layi na 10
Dress
Many other symbolic references are made to clothing. Just as a uniform or special attire identifies one as belonging to a certain organization or supporting a certain movement, so clothing, as used symbolically in the Bible, indicates the identification of a person by the stand he takes and his activities in harmony with it, as in the case of Jesus’ illustration of the marriage garment. (Mt 22:11, 12; see HEADDRESS; SANDAL.) At Revelation 16:14, 15, the Lord Jesus Christ warns against falling asleep spiritually and being stripped of one’s identity as a faithful witness of the true God. This could be disastrous on the eve of “the war of the great day of God the Almighty.”
Muhimmancin Suna?
Ba mu da wani iko bisa suka da aka raɗa mana saꞌada muke jarirai. Amma, mu za mu iya bai kanmu irin sunan da muka yi. (Misalai 20:11) Me ya sa ba za ka tambayi kanka ba: ‘Da a ce Yesu ko kuma manzani sun sami zarafi, wane suna za su ba ka? Wane suna zai dace da irin halina?’
Wannan tambayar tana bukatar a mai da hankali a kanta sosai. Me ya sa? “Suna mai-kyau abin zaɓa ne gaba da wadata mai-yawa,” Sarki Sulemanu ya rubuta.” (Misalai 22:1) Hakika, idan muka yi suna mai kyau, a inda muke hakika muna da arziki. Mafi muhimmanci ma, idan muka kasance da suna mai kyau a gaban Allah, za mu sami dukiya madawwamiya. Ta yaya? Allah ya yi alkawari cewa zai rubuta a cikin “littafin tunawa” sunayen waɗanda.—Malachi 3:16; Ruꞌya ta Yohanna 3:5; 20:12-15.
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
g00-E 7/8 11 sakin layi na 3
Smile—It’s Good for You!
Does smiling really make a difference? Well, do you remember when someone’s smile brought you a sense of relief or made you feel relaxed? Or when the absence of a smile made you feel nervous or even rejected? Yes, a smile does make a difference. It affects both the one who is smiling and the one smiled at. The Bible character Job said of his adversaries: “I would smile at them—they would not believe it—and the light of my face they would not cast down.” (Job 29:24) “The light” of Job’s face may have denoted his brightness or cheerfulness.
25-31 GA DISAMBA
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | AYUBA 30-31
“Ta Yaya Ayuba Ya Kasance da Tsabta a Ɗabiꞌarsa?”
Ka Kau Da Idanunka Daga Abubuwa Marasa Amfani!
8 Kiristoci na gaskiya ma suna shaꞌawar idanu da na jiki. Saboda haka, Kalmar Allah ta ƙarfafamu mu yi wa kanmu horo game da abin da muke kallo da abin da muke shaꞌawarsa. (1 Kor. 9:25, 27; karanta 1 Yoh. 2:15-17.) Ayuba mutum mai adalci ya fahimci cewa gani da shaꞌawa suna da alaƙa. Ya ce: “Na yi waꞌadi da idanuna; yaꞌya fa zan yi shaꞌawar budurwa?” (Ayu. 31:1) Ayuba ya ƙi taɓa mace ta hanyar lalata, kuma ba zai ma sa kansa ya yi irin wannan tunanin ba. Yesu ya nanata cewa dole ne a tsabtace zuciya ta wurin ƙin yin tunanin lalata saꞌad da ya ce: “Dukan wanda ya [kalli] mace har ya yi shaꞌawarta, ya rigaya ya yi zina da ita cikin zuciyatasa.”—Mat. 5:28.
Ka Yi Laꞌakari Da ‘Yadda Ƙarshen Zai Zama’
Kafin ka soma taku na farko a kan wannan mummunar hanyar, ka tambaye kanka ‘Ina ne wannan zai kai ni?’ Idan ka dakata, ka yi tunani a kan ‘yadda ƙarshen zai zama’ hakan zai iya hana ka yin tafiya da za ta kai ga mummunan sakamako. Cutar sida da wasu cututtuka da ake ɗauka ta jimaꞌi, cikin shege, zubar da ciki, matsala da abokanan zama da kuma lamiri mai sūka sun zama sakamako da waɗanda suka yi watsi da hanyar nan suka fuskanta. Manzo Bulus ya faɗi “yadda ƙarshe zai zama” ga waɗanda suke yin lalata. “Ba za su gāji mulkin Allah ba.”—1Korinthiyawa 6:9, 10.
w10 11/15 5-6 sakin layi na 15-16
Matasa, Ku Bar Kalmar Allah Ta Yi Muku Ja-gora
15 A wane lokaci ne kuke tunani cewa za a fi gwada amincinku ga Allah, saꞌad da kuke tare da mutane ko kuma saꞌad da kuka kaɗaita? Hakika, saꞌad da kuke a makaranta ko wajen aiki kun fi kasancewa a faɗake ga kome da zai ɓata dangantakarku da Allah. Amma saꞌad da ba ku a faɗake ne za ku fi faɗa wa hari da za a kai ga mizananku na ɗabiꞌa.
16 Me ya sa za ku so ku yi biyayya ga Jehobah ko a lokacin da kuka kaɗaita? Ku tuna wannan: Kuna iya ɓata wa Jehobah rai ko kuma ku sa shi farin ciki. (Far. 6:5, 6; Mis. 27:11) Abubuwan da kuke yi suna shafan Jehobah domin “yana kula da ku.” (1 Bit. 5:7) Yana son ku saurare shi don ku amfani kanku. (Isha. 48:17, 18) Wasu bayin Jehobah a Israꞌila ta dā sun ɓata masa rai, yayin da suka ƙi bin gargaɗinsa. (Zab. 78:40, 41) A wani ɓangare kuma, Jehobah yana ƙaunar annabi Daniyel sosai, gama wani malaꞌika ya kira shi “mutum ƙaunatacce ƙwarai.” (Dan. 10:11) Me ya sa? Daniyel ya kasance da aminci ga Allah ba a lokacin da yake tare da mutane kawai ba amma saꞌad da ya kaɗaita.—Karanta Daniyel 6:10.
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
Ku Riƙa Nuna Ƙauna Domin Ƙarfafa Mutane
13 Ka zama mai saurarawa da kyau. (Yaƙ. 1:19) Muna nuna cewa muna ƙaunar ɗanꞌuwan da ya yi sanyin gwiwa idan muka saurare shi kuma muka nuna masa juyayi. Ka yi ƙoƙari ka yi tunanin yadda za ka ji idan kai ne kake cikin yanayinsa. Ka yi tambayoyin da za su taimaka maka ka fahimci yanayinsa sosai kuma ka yi hakan cikin dabara. Yanayin fuskarka za ta nuna ko ka damu da shi da gaske. Saꞌad da mutumin yake magana, ka ƙyale shi ya faɗi abin da ke zuciyarsa ba tare da ka katse masa magana ba. Ta wurin saurarar sa da kyau, za ka san yadda yake ji kuma zai amince da kai. Ƙari ga haka, shi ma zai so ya bi shawarwarin da ka ba shi. Idan wasu sun san ka damu da su, za ka ƙarfafa su sosai.