TALIFIN NAZARI NA 7
Muna Ƙaunar Jehobah, Ubanmu Sosai
“Muna ƙauna gama Allah ne ya fara ƙaunace mu.”—1 YOH. 4:19.
WAƘA TA 3 Ƙarfinmu, Begenmu da Makiyayinmu
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1-2. Ta yaya Jehobah ya buɗe mana hanyar kasancewa cikin iyalinsa?
JEHOBAH ya gayyace mu mu kasance cikin bayinsa. Wannan gayyata ce mai ban-sha’awa sosai! Dukan bayin Jehobah suna cikin iyalinsa, sun yi alkawarin bauta masa kuma suna da imani ga fansar da Yesu ya yi. Iyalinmu na cike da farin ciki. Muna ɗan jin daɗin rayuwa a yau kuma muna sa ran jin daɗin rayuwa sosai a nan gaba a sama ko kuma a Aljanna a duniya.
2 Jehobah ya sa ya yiwu mu kasance cikin iyalinsa domin yana ƙaunar mu sosai. Amma domin Jehobah ya yi hakan, ya yi sadaukarwa sosai. (Yoh. 3:16) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ‘sayen mu aka yi, aka kuma biya.’ (1 Kor. 6:20) Jehobah ya yi amfani da fansar Yesu don ya sa ya yiwu mu ƙulla dangantaka mai kyau da shi. Muna da gatar kiran Allah mafi iko a sararin sama Uba. Kuma kamar yadda muka tattauna a talifin da ya gabata, Jehobah ne Uba mafi kirki.
3. Waɗanne tambayoyi ne za mu iya yi? (Ka kuma duba akwatin nan “Jehobah Ya San da Ni Kuwa?”)
3 Za mu iya yin irin tambayar da wani marubucin zabura ya yi cewa: “Me zan ba Yahweh saboda dukan alheransa gare ni?” (Zab. 116:12) Amsar ita ce ba za mu iya biyan sa duban alherin da ya yi mana ba. Duk da haka, ƙaunarsa gare mu ta motsa mu mu ƙaunace shi. Manzo Yohanna ya ce: “Muna ƙauna gama Allah ne ya fara ƙaunace mu.” (1 Yoh. 4:19) A waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna wa Ubanmu na sama cewa muna ƙaunar sa?
KA KUSACI JEHOBAH
Muna nuna ƙaunarmu ga Ubanmu Jehobah ta wajen yin addu’a da biyayya da kuma taimaka wa mutane su ƙaunace shi (Ka duba sakin layi na 4-14)
4. Kamar yadda Yaƙub 4:8 ta nuna, me ya sa ya kamata mu ƙoƙarta don mu kusaci Jehobah?
4 Jehobah yana so mu kusace shi kuma mu riƙa tattaunawa da shi. (Karanta Yaƙub 4:8.) Ya ƙarfafa mu cewa mu nace ‘cikin addu’armu’ kuma zai riƙa saurarar mu. (Rom. 12:12) Ba ya gajiya da jin addu’o’inmu. Mu kuma muna saurarar sa ta wajen karanta Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki da kuma littattafanmu. Ƙari ga haka, muna saurarar sa ta wajen saurarar abin da ake faɗa a taron ikilisiya. Kamar yadda tattaunawa take sa yara su kusaci iyayensu, tattaunawa da Jehobah a kai a kai yana taimaka mana mu kusace shi.
Ka duba sakin layi na 5
5. Me za mu iya yi don Jehobah ya ji addu’o’inmu?
5 Ka yi tunani a kan irin tattaunawa da kake yi da Allah. Jehobah yana so mu gaya masa dukan abin da ke zuciyarmu. (Zab. 62:8) Ya kamata mu yi wa kanmu tambayar nan: ‘Shin addu’o’ina suna kamar saƙon da aka sake bugawa ne ko suna kamar wasiƙar da aka rubuta da alƙalami?’ Babu shakka, kana ƙaunar Jehobah sosai, kuma kana so dangantakarka da shi ta yi ƙarfi. Idan haka ne, dole ne ka riƙa tattaunawa da shi a kai a kai. Ka gaya masa dukan damuwarka. Ka gaya masa abin da ke sa ka murna da kuma abin da ke ci maka rai. Ka kasance da tabbaci cewa za ka iya neman taimakonsa.
6. Me ya kamata mu yi don mu kusaci Ubanmu na sama?
6 Idan muna so mu kusaci Jehobah, dole ne mu riƙa nuna masa godiya. Mun yarda da furucin da wani marubucin zabura ya yi, cewa: “Ya Yahweh Allahna, ayyukanka na ban mamaki suna da yawa! Shirye-shiryenka gare mu sun fi gaban ƙirge! Ko da na so in yi shelarsu, ko in ba da labarinsu, yawansu sun fi gaban ƙirge!” (Zab. 40:5) Ba nuna godiya kaɗai ya kamata mu yi ba, amma ya kamata mu nuna hakan ta furucinmu da ayyukanmu. Hakan zai nuna cewa mun fita dabam da sauran mutane. Muna rayuwa a duniyar da mutane da yawa ba sa nuna godiya ga Allah don abubuwa da yake musu. Alama ɗaya da ta nuna cewa muna rayuwa a “kwanaki na ƙarshe” ita ce mutane za su zama marasa nuna godiya. (2 Tim. 3:1, 2) Bai kamata mu kasance da irin wannan halin ba!
7. Mene ne Jehobah yake so mu yi, kuma me ya sa?
7 Iyaye ba sa so yaransu su riƙa yin faɗa da mutane, amma suna so yaran su zama mutanen kirki. Hakazalika, Jehobah yana son dukan yaransa su zama abokan juna. Ƙari ga haka, ƙaunar da muke yi wa juna ne take nuna cewa mu Kiristoci ne na gaskiya. (Yoh. 13:35) Mun amince da abin da wani marubucin Zabura ya rubuta, ya ce: “Hakika, abu mai kyau ne, mai daɗi kuma ’yan’uwa su zauna tare kamar ɗaya!” (Zab. 133:1) Idan muna ƙaunar ’yan’uwanmu, muna tabbatar wa Jehobah da cewa muna ƙaunar sa. (1 Yoh. 4:20) Hakika abin ban sha’awa ne mu kasance cikin iyalin da kowa yake da kirki, kuma suna jin tausayin juna.—Afis. 4:32.
KA NUNA ƘAUNA TA YIN BIYAYYA
Ka duba sakin layi na 8
8. Kamar yadda 1 Yohanna 5:3 ta nuna, wane dalili ne ya sa muke biyayya ga Jehobah?
8 Jehobah yana so yara su riƙa yi wa iyayensu biyayya, kuma yana so mu riƙa yi masa biyayya. (Afis. 6:1) Jehobah ya cancanci mu riƙa yi masa biyayya don shi ne Mahaliccinmu, kuma ya fi kowane ɗan Adam hikima. Dalili mafi muhimmanci da ya sa muke yi wa Jehobah biyayya shi ne domin muna ƙaunar sa. (Karanta 1 Yohanna 5:3.) Ko da yake da akwai dalilai da yawa da ya kamata su sa mu riƙa yi wa Jehobah biyayya, Allah ba ya tilasta mana mu yi hakan. Jehobah ya ba mu ’yanci, don haka, yana farin ciki idan ya ga cewa mun zaɓi mu bauta masa domin muna ƙaunar sa.
9-10. Me ya sa yake da muhimmanci mu san ƙa’idodin Jehobah kuma mu bi su?
9 Iyaye suna so su kāre yaransu. Shi ya sa suke kafa dokokin da za su kāre yaran. Idan yara suna bin waɗannan dokokin, suna nuna wa iyayensu cewa sun amince da su kuma suna daraja su. Hakazalika, yana da muhimmanci mu san dokokin Ubanmu na sama kuma mu riƙa bin su. Idan muka yi hakan, za mu nuna wa Jehobah cewa muna ƙaunar sa da kuma daraja shi. Ƙari ga haka, za mu amfana sosai. (Isha. 48:17, 18) Amma mutanen da suka ƙi bin ƙa’idodin Jehobah za su cutar da kansu.—Gal. 6:7, 8.
10 Idan muna yin rayuwar da ta jitu da ƙa’idodin Jehobah, za mu kāre kanmu daga abubuwan da za su iya cutar da mu da kuma dangantakarmu da Jehobah. Allah ya san abubuwan da muke bukata. Wata ’yar’uwa mai suna Aurora da take zama a Amirka ta ce: “Na san cewa yin biyayya ga Jehobah zai sa in more rayuwa.” Hakan gaskiya ne. Ta yaya ka amfana daga bin ƙa’idodin Jehobah?
11. Ta yaya addu’a take taimaka mana?
11 Yin addu’a yana taimaka mana mu riƙa yin biyayya, har ma a lokacin da muke fuskantar matsala. A wasu lokuta, yana mana wuya mu yi biyayya ga Jehobah don mu ajizai ne, amma muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu don mu guji yin rashin biyayya. Wani marubucin Zabura ya roƙi Allah, ya ce: “Ka ba ni ruhun biyayya.” (Zab. 51:12) Wata ’yar’uwa mai suna Denise da take hidimar majagaba ta ce: “Idan bin dokokin Jehobah ya yi mini wuya, ina addu’a domin ya taimaka mini na yi abin da ya dace.” Muna bukatar mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai amsa irin wannan addu’ar.—Luk. 11:9-13.
KA TAIMAKA WA MUTANE SU ƘAUNACI UBANMU
12. Kamar yadda Afisawa 5:1 ta nuna, mene ne muke bukatar mu yi?
12 Karanta Afisawa 5:1. Domin mu “ ’ya’ya waɗanda Allah yake ƙauna” ne, muna yin iya ƙoƙarinmu don mu yi koyi da shi. Muna yin koyi da shi ta wajen nuna alheri da ƙauna da kuma gafarta wa mutane. Sa’ad da mutanen da ba su san Allah ba suka ga halayenmu masu kyau, za su so su koya game da Allah. (1 Bit. 2:12) Iyaye Kiristoci suna bukatar su yi iya ƙoƙarinsu don su yi koyi da Jehobah ta wajen bi da yaransu yadda ya dace. Idan iyaye suka yi koyi da Jehobah, yaransu ma za su so su ƙulla abokantaka da Ubanmu mai ƙauna.
Ka duba sakin layi na 13
13. Me muke bukatar mu mai da wa hankali?
13 Yara suna alfahari da iyayensu kuma suna farin cikin yin magana game da su. Hakazalika, muna alfahari da Jehobah Ubanmu kuma muna so mutane su san shi. Dukanmu muna da ra’ayin Sarki Dauda wanda ya ce: “Raina zai yabi Yahweh.” (Zab. 34:2) Amma idan muna jin kunya kuma fa? Ta yaya za mu yi ƙarfin zuciya? Idan muka mai da hankali ga yadda muke faranta wa Jehobah rai da kuma yadda mutane suke amfana daga koya game da shi, za mu kasance da ƙarfin zuciya. Jehobah zai taimaka mana mu yi gaba gaɗi. Ya taimaka wa ’yan’uwanmu a ƙarni na farko su yi ƙarfin zuciya, kuma zai taimaka mana.—1 Tas. 2:2.
14. Waɗanne dalilai ne suke sa yake da muhimmanci mu yi wa’azi?
14 Jehobah ba ya nuna son kai kuma yana farin ciki idan ya ga muna ƙaunar mutane ko da daga ina ne suka fito. (A. M. 10:34, 35) Wata hanya mafi kyau da za mu iya nuna cewa muna ƙaunar mutane ita ce ta yi musu wa’azi. (Mat. 28:19, 20) Mene ne hakan zai cim ma? Mutanen da ke saurarar mu za su inganta salon rayuwarsu kuma za su kasance da begen yin rayuwa har abada.—1 Tim. 4:16.
ZA KA YI FARIN CIKI IDAN KA ƘAUNACI JEHOBAH
15-16. Waɗanne dalilai ne suke sa mu farin ciki?
15 Jehobah Uba ne mai ƙauna, don haka, yana son iyalinsa su riƙa farin ciki. (Isha. 65:14) Da akwai dalilai da yawa da za su sa mu farin ciki a yanzu ko da muna fuskantar matsaloli. Alal misali, muna da tabbaci cewa Ubanmu yana ƙaunar mu sosai. Ban da haka, mun san gaskiyar da ke Kalmar Allah. (Irm. 15:16) Ƙari ga haka, muna cikin iyalin da ke ƙaunar Jehobah da dokokinsa kuma suna ƙaunar juna.—Zab. 106:4, 5.
16 Za mu ci gaba da yin farin ciki domin mun san cewa a nan gaba rayuwa za ta gyaru. Mun san cewa nan ba daɗewa ba, Jehobah zai halaka mugaye kuma zai yi amfani da mulkinsa don ya mayar da duniya ta zama Aljanna. Ƙari ga haka, muna da bege cewa za a ta da matattu kuma za su sake haɗuwa da iyalinsu. (Yoh. 5:28, 29) Wannan abin farin ciki ne! Mafi muhimmanci ma, muna da tabbaci cewa nan ba da daɗewa ba, dukan waɗanda suke sama da kuma duniya za su yabi Ubanmu mai ƙauna kuma su bauta masa domin ya cancanci hakan.
WAƘA TA 12 Jehobah, Allah Mafi Iko
a Mun san cewa Ubanmu Jehobah yana ƙaunar mu sosai kuma ya sa mu kasance cikin bayinsa. Saboda haka, muna bukatar mu ƙaunace shi. Ta yaya za mu nuna wa Ubanmu cewa muna ƙaunar sa. A wannan talifin, za mu tattauna wasu abubuwa da za mu iya yi.