Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwyp talifi na 104
  • Ta Yaya Zan Iya Mai da Hankali Sosai ga Abin da Nake Yi?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta Yaya Zan Iya Mai da Hankali Sosai ga Abin da Nake Yi?
  • Tambayoyin Matasa
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Me ke raba hankalina?
  • Abin da zai taimake ka ka mai ga hankali ga abin da kake yi
  • Za Ka Iya Koyo da Kyau Idan Ba Ka Cikin Makaranta?
    Tambayoyin Matasa
  • Tambayoyin Masu Shela
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Me ya kamata na sani game da aika sako ta wayar selula?
    Tambayoyin Matasa
  • Ka Nemi Wuri Mai Kyau don Yin Nazari
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
Dubi Ƙari
Tambayoyin Matasa
ijwyp talifi na 104
Wata yarinya tana yi kamar tana korin abubuwan da suke so su hana ta natsuwa sa’ad da take karatu. Abubuwan nan sun hada da waka, da bidiyoyi, da sakonni, da kuma hotuna.

TAMBAYOYIN MATASA

Ta Yaya Zan Iya Mai da Hankali Sosai ga Abin da Nake Yi?

  • Me ke raba hankalina?

  • Abin da zai taimake ka ka mai ga hankali ga abin da kake yi

  • Abin da tsararka suka ce

Me ke raba hankalina?

Wata mai suna Elaine ta ce: “A dā, nakan karanta littattafai da dama amma yanzu yana min wuya in yi hakan. Ko da sakin layi daya ne, idan ya yi tsawo, ba na so in karanta shi.”

Miranda kuma ta ce: “Nakan kara saurin bidiyon da nake kallo idan na ga kamar yana bata min lokaci.”

Jane ta ce: “Ko da abu mai muhimmanci ne nake yi, idan wayata ta yi kara, nan da nan sai in soma tunani, ‘Wa ya tura min sako?’ ”

Shin, na’urorin zamani za su iya hana mutum natsuwa? Wasu sun ce kwarai kuwa. Wani marubuci mai ba da shawara mai suna Nicholas Carr ya ce: “Idan muna amfani da intane da yawa, hakan zai sa hankalinmu ya rika saurin rabuwa. Kwakwalwarmu za ta saba da yin tunani da wuri ba tare da mun mai da hankali ga bin da muke yi ba.”a

Ga fannoni uku da na’urori za su iya hana ka natsuwa.

  • Sa’ad da kake magana. Wata matashiya mai suna Maria ta ce: “Ko da mutane suna tattaunawa ido-da-ido ne, wasu sukan ci gaba da tura sakonni, ko buga game ko kuma duba dandalin sada zumunta, maimakon su mai da hankali ga wanda suke magana da shi.”

  • Sa’ad da kake aji. Wani littafi mai suna Digital Kids ya ce: “Yawancin dalibai sun ce sukan yi amfani da wayoyinsu wajen tura sakonni, ko neman abubuwa a intane ko su shiga kallon bidiyoyin da ba su shafi abin da suke koya a makaranta ba.”

  • Sa’ad da kake nazari ko karatu. Wani dan shekara 22 mai suna Chris ya ce: “Wani abin da yake min wuya shi ne in guji duba wayata a duk lokacin da ya yi kara.” Idan kai dalibi ne, kuma an ba ka aiki a makaranta ka yi a gida, kila aikin na awa daya ne, amma za ka iya yin awa uku ko fiye da hakan idan na’urorinka suna raba hankalinka.

Gaskiyar batun: Zai yi maka wuya ka natsu idan na’urorinka ne ka sa a gaba kuma kana barin su su raba hankalinka.

Wani yaro yana fadowa daga kan dokin da ya daga kafafunsa.

Idan tunaninka yana yawo nan da can, yana kama da dokin da yake gudu da kai kuma ka kasa yi masa ja-gora

Abin da zai taimake ka ka mai ga hankali ga abin da kake yi

  • Sa’ad da kake magana. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku kula da kanku kadai, amma ku kula da wadansu kuma.” (Filibiyawa 2:⁠4) Ka nuna wa mutane cewa ka damu da su ta wurin sauraronsu da kyau. Ka kalle su sa’ad da suke magana kuma kar ka bar na’urorinka su janye hankalinka.

    Wani mai suna Thomas ya ce, “Idan kana magana da mutane, kada ka rika duba wayarka. Ka daraja wanda kake magana da shi ta wurin ba shi hankalinka.”

    ABIN DA ZAI TAIMAKA: Idan kana magana da wani, za ka iya ajiye wayarka a inda ba za ka gani ba. Masu bincike sun ce ganin wayarka kawai ma zai iya hana ka mai da hankali ga abin da kake yi, don zai rika tuna maka cewa wayar za ta yi kara nan ba da dadewa ba.

  • Sa’ad da kake aji. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku yi hankali fa da yadda kuke [sauraro].” (Luka 8:18) Bisa ga wannan abin da Littafi Mai Tsarki ya fada, kar ka rika karanta sakonni ko buga game ko ka rika tura sakonni a aji, ko da akwai sabis na intane a ajinku. Maimakon haka, ka dinga mai da hankali ga abin da ake koyarwa.

    Wata mai suna Karen ta ce: “Ka yi kokari ka saurari abin da ake koyarwa da kyau. Ka rubuta muhimman darussa da malaminku yake koyarwa. Idan zai yiwu ka zauna a kujerar da ke gaba don kar wani abu ya dauke hankalinka.”

    ABIN DA ZAI TAIMAKA: Ka dinga rubutu da hannunka maimakon ka yi amfani da kwamfuta. Masu bincike sun gano cewa hakan zai taimaka maka ka natsu kuma ka tuna abin da ka koya.

    Wata yarinya tana karatu a kan teburi. Ta ajiye jakarta da wayarta da mujallunta a inda ba za ta dinga ganin su ba.
  • Sa’ad da kake nazari ko karatu. Littafi Mai Tsarki ya ce mu kokarta mu ‘sami hikima da ganewa.’ (Karin Magana 4:⁠5) Hakan yana bukatar yin tunani sosai a kan abin da kake karantawa, ba yin karatu sama-sama don ka ci jarrabawa kawai ba.

    Wani mai suna Chris ya ce: “Idan ina nazari, nakan saita wayata yadda kira ko sakonni ba za su shigo ba kuma in mai da hankali ga abin da nake yi. Ba na dauka wayata ko da ta yi wata kara. Idan na tuna wani abin da ba na so in manta, nakan rubuta shi.”

    ABIN DA ZAI TAIMAKA: Ka kawar da duk wani abin da zai raba hankalinka a inda kake karatu. Wurin ya zama da tsabta kuma a shirye.

a Daga littafin nan, The Shallows​—⁠What the Internet Is Doing to Our Brains.

Abin da tsararka suka ce

Katie.

Wata mai suna Katie ta ce: “Sa’ad da kake nazari, za ka iya zama kamar wanda ke kan kwale-kwale na zamani da ke gudu sosai. Yakan yi tafiya mai nisa amma a saman ruwan yake. Idan kana so ka koyi abubuwa da yawa, kana bukatar ka zama kamar masu iyo da suke shiga har karkashin teku don su samo abubuwa masu daraja.”

Rogelio.

Wani mai suna Rogelio ya ce: “Idan mutum yana da koshin lafiya, hakan zai inganta tunaninsa. Cin abinci mai gina jiki yana taimaka min in tattara hankalina a wuri daya. Samun isasshen barci ma yakan taimaka min in mai da hankali ga abubuwan da nake yi washegari.”

Bita: Ta yaya zan iya mai da hankali sosai ga abin da nake yi?

  • Sa’ad da kake magana. Ka nuna cewa ka damu da wanda kake magana da shi, ta wajen saurarar sa da kyau ba tare da barin wani abu ya raba hankalinka ba.

  • Sa’ad da kake aji. Kar ka rika karanta sakonni ko buga game ko ka rika tura sakonni a aji. Maimakon haka, ka dinga mai da hankali ga abin da ake koyarwa.

  • Sa’ad da kake nazari ko karatu. Ka kawar da duk wani abin da zai raba hankalinka a inda kake karatu. Wurin ya zama da tsabta kuma a shirye.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba