WAƘA TA 120
Mu Koyi Nuna Sauƙin Kai Kamar Yesu
Hoto
1. Yesu Kristi yana da ɗaukaka fa,
Duk da hakan bai nuna girman kai ba.
Jehobah ne ya ba shi matsayin nan,
Ya nuna cewa yana da sauƙin kai.
2. Yesu Kristi ya ce wa duk mutanen,
Da ke shan wahala su kusace shi.
In suna biɗan Mulkin Maɗaukaki,
Da sauƙin kai, zai taimake su sosai.
3. ʼYan’uwa ne mu a ikilisiya,
Sai mu riƙa yi wa Yesu biyayya.
Allah yana ƙaunar masu sauƙin kai,
Ya ce zai ba su rai na har abada.
(Ka kuma duba Mis. 3:34; Mat. 5:5; 23:8; Rom. 12:16.)