WAƘA TA 98
Nassosi Hurarre Ne Daga Allah
Hoto
	(2 Timotawus 3:16, 17)
- 1. Kalmar Allah na taimaka, - Tana sa mu ga haske. - In muna bin umurninta, - Za mu ceci rayukanmu. 
- 2. Ya yi tanadin Kalmarsa, - Don mu san umurninsa. - Tana ƙarfafa mutane, - Tana horar da mu sosai. 
- 3. Kalmar Allah ta sa mu san, - Cewa Yana da ƙauna. - Karanta ta a koyaushe - Zai sa mu riƙe aminci. 
(Ka kuma duba Zab. 119:105; Mis. 4:13.)