Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 7/15 pp. 29-32
  • Ka Kafa Makasudai da za su Yiwu Kuma ka Yi Farin Ciki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Kafa Makasudai da za su Yiwu Kuma ka Yi Farin Ciki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Kafa Makasudai da Za su Yiwu
  • Ka Yi Abubuwan da Za ka Iya Yi
  • Ka Yi Gyara Idan Ya Yiwu
  • Makasudai da za Su Yiwu Suna Kawo Albarka
  • Ka Yi Farin Ciki don Ci-gaba da Kake Samu a Ibadarka!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Bauta wa Jehobah da Iya Karfinka Zai Sa Ka Farin Ciki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Yadda Za Mu Iya Kafa da Kuma Cim ma Makasudai a Hidimarmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Ku Zama Masu Sanin Yakamata Kamar Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 7/15 pp. 29-32

Ka Kafa Makasudai da za su Yiwu Kuma ka Yi Farin Ciki

“NA SAKE kasawa!” Sau nawa ne ka faɗi hakan domin ka kasa cim ma abin da ka shirya za ka yi? Wata mata tana iya furta hakan domin ta gaji don jaririnta na bukata a mai da masa hankali kuma tana baƙin ciki cewa ba za ta iya mai da hankali ga abubuwa na ruhaniya ba. Wani Kirista zai ga ya kasa domin yadda aka yi renonsa kuma yana ganin cewa hidimar da yake yi a ikilisiya bai isa ba. Wata Mashaidiya tsohuwa tana baƙin ciki domin ba ta iya yin ayyuka na Kirista sosai kamar sa’ad da take da ƙarfi kuma tana iya yin tafiya ba. “Jawabi da ke ƙarfafa hidimar majagaba wani lokaci ya kan sa ni kuka,” in ji Christiane, wadda yanayin iyalinta na hana ta yin yadda take so a hidimar Jehobah.

Menene za mu yi idan muka ji hakan? Ta yaya wasu Kiristoci suka kasance da ra’ayin da ya dace game da yanayinsu? Menene amfanin kafa makasudai da za ka iya cim ma?

Ka Kafa Makasudai da Za su Yiwu

Manzo Bulus ya gaya mana yadda za mu ci gaba da yin farin ciki sa’ad da ya ce: “Ku yi farinciki cikin Ubangiji kullayaumi: sai in sake cewa, Ku yi farinciki. Ku bari jimrewarku [sanin ya kamata, NW] ta sanu ga dukan mutane.” (Filib. 4:4, 5) Don mu yi farin ciki kuma mu samu gamsuwa a hidimarmu ga Allah, muna bukatar mu kafa makasudai da suka yi daidai da iyawarmu da kuma yanayinmu. Idan muka yi ƙoƙari muka kafa makasudai masu wuya, muna jawo wa kanmu matsi da bai dace ba. A wani ɓangare kuma, ya kamata mu mai da hankali kada muna sauƙaƙa wa kanmu ainun, mu yi amfani da kasawarmu a matsayin hujja don rage hidimarmu na Kirista fiye da yadda ya kamata.

Ko menene yanayinmu, Jehobah na bukatar mu ba shi abu mafi kyau, wato, mu yi masa hidima da dukan zuciyarmu. (Kol. 3:23, 24) Idan muka ba Jehobah kaɗan daga cikin abin da ya kamata, ba ma yin rayuwa daidai da keɓe kanmu. (Rom. 12:1) Ƙari ga haka, za mu hana wa kanmu gamsuwa, farin ciki, da wasu albarka da ake samu ta yin hidima da dukan zuciyarmu.—Mis. 10:22.

Kalmar da aka fassara “sanin ya kamata” a cikin Littafi Mai Tsarki yana nufin sanin iyakar abin da za mu iya yi. A zahiri yana nufin sauƙin hali. (Yaƙ. 3:17) Kalmar tana kuma nufin kada mutum ya matsa wa kansa ainun. Saboda haka, idan muka san abin da ya dace, za mu bincika yanayinmu yadda ya dace. Hakan yana da wuya ne? Ga wasu yana da wuya, ko da yake suna iya ɗaukan wasu yadda ya kamata. Alal misali, idan abokinmu na kud da kud yana gajiya don yana yin abubuwa masu yawa, za mu yi ƙoƙari mu taimake shi ya ga amfanin yin gyara a rayuwarsa. Haka nan ma, muna bukatar mu san lokacin da muke yin abubuwa da sun fi ƙarfinmu.—Mis. 11:17.

Kasancewa da ra’ayin da ya dace game da kasawarmu zai fi wuya idan iyayen da suka yi renonmu suna bukatar mu yi abubuwa da sun fi ƙarfinmu. Da suke yarantaka wasu suna jin cewa koyaushe ya kamata su ƙara yin abubuwa ko fiye da haka don iyayensu su ƙaunace su. Idan haka yanayinmu yake, wataƙila ba mu fahimci yadda Jehobah yake ɗaukanmu ba. Jehobah yana ƙaunarmu don hidimar da muke masa da zuciya ɗaya. Kalmar Allah ta tabbatar mana cewa Jehobah “ya san tabi’ammu; Ya kan tuna mu turɓaya ne.” (Zab. 103:14) Ya san kasawarmu kuma yana ƙaunarmu idan muka bauta masa da himma duk da kasawarmu. Idan muka tuna cewa Allah ba shugaba ba ne mai matsa wa mutane zai taimake mu mu san abin da za mu iya yi, kuma mu san kasawarmu.—Mi. 6:8.

Duk da haka, yana yi wa wasu wuya su kasance da ra’ayin da ya dace. Idan haka kake, ka nemi taimakon Kirista da ya manyanta da ya san ka da kyau. (Mis. 27:9) Alal misali, kana son ka yi hidimar majagaba na kullum? Wannan makasudi ne mai kyau ƙwarai! Yana maka wuya ka cim ma wannan makasudin? Wataƙila kana bukatar taimako don ka sauƙaƙa rayuwarka. Ko kuwa abokinka Kirista da ka amince da shi ya tattauna da kai ko hakkinka na iyali zai yiwu ka yi hidimar majagaba ta kullum a wannan lokacin ko ba zai yiwu ba. Zai ko za ta taimake ka ka ga ko za ka iya ɗaukan ƙarin aikin da hidimar majagaba ta ƙunsa ko kuma gyara da zai taimake ka ka yi hakan. Ya kamata maigida ya taimaki matarsa ta yi abubuwa da za ta iya yi. Alal misali, yana iya ba ta shawara ta huta sosai kafin ta soma sabuwar wata da za ta ƙara hidimarta. Wannan zai iya sa ta yi ƙarfi kuma ya taimake ta ta ci gaba da farin ciki a hidima.

Ka Yi Abubuwan da Za ka Iya Yi

Tsufa ko kuma rashin lafiya zai iya hana mu yin abubuwan da muke so mu yi a hidimar Jehobah. Idan kana da yara, za ka ga kamar ba ka amfana sosai daga nazari na kai ko kuma taron Kirista saboda kana kula da yaranka. Amma, mai da hankali ga kasawarka zai hana ka ganin abin da ya kamata ka yi?

Shekaru dubbai da suka shige, wani Balawi ya furta abin da yake son ya yi da ke da wuyan cim mawa. Yana da gatar yin hidima na makonni biyu a kowace shekara a haikali. Duk da haka, yana sha’awar zama kusa da bagadi a koyaushe. (Zab. 84:1-3) Menene ya taimaki wannan mutum mai aminci ya gamsu? Ya fahimci cewa rana guda a haikali gata ne mai muhimmanci. (Zab. 84:4, 5, 10) Hakazalika, maimakon mu damu da kasawarmu, ya kamata mu yi ƙoƙari mu fahimci kuma mu nuna godiya ga abin da za mu iya yi.

Ka yi la’akari da misalin Nerlande, wata ’yar’uwa Kirista da ke Kanada. Da yake tana amfani da keken guragu tana gani ba ta yin abin da ya kamata ta yi a hidima. Amma, ta canja ra’ayinta ta wajen ɗaukan wajen saye-saye da ke kusa da gidanta ya zama yankinta. Ta bayyana: “Ina zaune a keken guragu kusa da wajen saye-sayen. Ina farin cikin yin wa’azi da mutanen da sukan zo su huta.” Yin irin wannan hidima mai muhimmanci ya gamsar da Nerlande.

Ka Yi Gyara Idan Ya Yiwu

Wani jirgin ruwa yana gudu sosai kuma iska yana hura filafilan jirgin. Amma, sa’ad da mai tukin jirgin ya fuskanci hadari mai tsanani, hakan zai sa ya zama dole ya gyara filafilan. Ba shi da iko bisa hadarin, amma idan ya yi gyara zai iya riƙe filafilan. Haka nan ma, sau da yawa ba za mu iya magance wani yanayi masu kama da hadari da muke fuskanta a rayuwa ba. Amma za mu iya daidaita rayuwarmu yadda ya kamata ta wurin gyara yadda muke yin amfani da jikinmu da hankalinmu. Idan muka lura da sabuwar yanayinmu, hakan zai taimake mu mu ci gaba da gamsuwa da kuma samun farin ciki a hidimar Allah.—Mis. 11:2.

Yi la’akari da wasu misalai. Idan ba mu da ƙarfi sosai, zai dace mu guji ayyuka da za su gajiyar da mu da sauri don mu samu ƙarfin halartan taron Kirista da yamma. Hakan zai sa mu amfana sosai daga tarayyar ’yan’uwanmu Kiristoci. Idan wata uwa ba ta iya fita hidimar gida gida ba domin yaron ba shi da lafiya, za ta iya gayyatar wata ’yar’uwa ta zo gidanta don su yi wa’azi na tarho sa’ad da yaron yake barci.

Idan yanayinka bai ƙyale ka ka yi nazarin abubuwan da za a tattauna a taron ikilisiya kuma fa? Za ka san iyakan abin da za ka iya shiryawa kuma ka yi wannan da kyau yadda zai yiwu. Ta wurin daidaita makasudinmu na nan da nan, za mu kasance da ƙwazo kuma mu yi farin ciki.

Daidaita makasudinmu yana bukatar tsayin daka da kuma yin ƙoƙari. Serge da Agnès, ma’aurata da ke Faransa sun yi canji sosai a shirye-shiryensu. “Sa’ad da muka san cewa Agnès tana da ciki, mun san ba za mu iya zama masu wa’azi a ƙasar waje ba,” in ji Serge. Serge da yanzu ya zama baban yara mata biyu ya bayyana yadda shi da matarsa suka kafa sabon makasudi. Ya ce: “Ko da yake ba mu yi hidima a wata ƙasa ba, mun tsai da shawara mu yi ‘hidima’ a ƙasarmu. Mun soma hidima da wani rukuni da suke yin wani yare.” Sun amfana daga wannan sabon makasudi da suka kafa kuwa? Serge ta ce: “Muna da amfani sosai a cikin ikilisiyar.”

Odile, wata ’yar’uwa Kirista a Faransa da take cikin shekarunta na 70 tana da ciwon gwiwa kuma ba ta iya tsayawa na dogon lokaci. Ta yi sanyin gwiwa cewa matsalarta ta hana ta sa hannu cikin hidima ta gida gida. Amma, ba ta kasala ba. Sai ta daidaita ayyukanta ta wajen yin hidima ta tarho. Ta ce: “Ya fi sauƙi kuma ina jin daɗin hidimar fiye da yadda nake tsammani!” Wannan hanyar wa’azi ya ƙarfafa ta don hidima.

Makasudai da za Su Yiwu Suna Kawo Albarka

Kafa makasudai da za mu iya cim ma zai sa mu guji baƙin ciki masu yawa. Ta wajen kafa makasudai da za mu iya cim ma, za mu san mun cim ma wani abu duk da kasawarmu. Da hakan za mu yi farin ciki don abin da muka cim ma, ko idan abin da muka cim ma bai yi yawa ba.—Gal. 6:4.

Yayin da muka kasance da daidaita daga abin da muke so mu cim ma, za mu fi yin la’akari da ’yan’uwanmu masu bi. Da yake mun san kasawarsu, za mu yi godiya don abin da suke yi mana. Ta wajen yin godiya da kowane taimako da aka ba da, muna ba da haɗin kai da kuma fahimi. (1 Bit. 3:8) Ka tuna cewa da yake Jehobah Uba ne mai ƙauna ba ya biɗan abin da ya fi ƙarfinmu. Kuma sa’ad da muka kafa makasudai da za mu iya cim ma, ayyukanmu na ruhaniya zai kawo mana ƙarin gamsuwa da farin ciki.

[Bayanin da ke shafi na 29]

Don mu samu farin ciki da gamsarwa a hidimarmu ga Allah, muna bukatar mu kasance da makasudai da za su yiwu don iyawarmu da yanayinmu

[Hoto a shafi na 30]

Nerlande tana yin farin cikin yin abin da za ta iya yi a hidima

[Hoto a shafi na 31]

Ka koyi yadda ake daidaita “filafilan jirgin”

[Inda aka Dauko]

© Wave Royalty Free/age fotostock

[Hoto a shafi na 32]

Serge da Agnès sun amfana ta wurin kafa sabon makasudi

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba