Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lv p. 215-p. 218 par. 1
  • Abubuwan da Suka Zama Jini da Kuma Hanyoyin Fida

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Abubuwan da Suka Zama Jini da Kuma Hanyoyin Fida
  • “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Makamantan Littattafai
  • Ra’ayin Allah Game da Jini
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ka Bi Ja-gorar Allah Rayayye
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Karin Bayanai
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Rai Yana da Muhimmanci a Gare Ka Kamar Yadda Yake ga Allah?
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
Dubi Ƙari
“Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
lv p. 215-p. 218 par. 1

RATAYE

Abubuwan da Suka Zama Jini da Kuma Hanyoyin Fiɗa

Abubuwa da suka zama jini. Waɗannan abubuwa ana samunsu ne daga abubuwa huɗu da suka haɗu suka zama jini, jajayen ƙwan halitta, farare, kamewar jini, da kuma ruwan jini. Alal misali, jajayen ƙwan halitta sun ƙunshi furotin da ake kira himoglobin. Ana amfani da magunguna da aka yi daga wannan himoglobin na mutane ko kuma na dabbobi wajen yi wa majiyyata da suke fama da rashin jini magani.

Ruwan jini, wanda kashi 90 ɗinsa ruwa ne, yana ɗauke da wasu sinadarai, gishiri, kayan gina jiki, sukari, da dai sauransu. Ruwan jini kuma ya ƙunshi abubuwa da suke sa jini ya daskare, ƙwayoyi masu yaƙi da cututtuka, irinsu furotin da ake kira albumin. Idan mutum yana da wani irin cuta, likita zai iya cewa a ba shi allurar da ake kira gamma-globulin wadda aka samo daga ruwan jinin mutanen da suke da kāriya ga wannan cutar. Ƙila an samo fararen ƙwan halitta daga interferons da kuma interleukins da ake amfani da su wajen magance wasu cututtuka masu tsanani da kuma ciwon daji.

Ya kamata Kiristoci su karɓi maganin da ya ƙunshi iri waɗannan abubuwa ne? Littafi Mai Tsarki bai ba da cikakken bayani ba, dole ne kowa ya yanke shawararsa a gaban Allah. Wasu za su ƙi dukan wani abu da ya fito daga jini, suna tunanin cewa Dokar Allah ga Isra’ila ta bukaci cewa a zubar da jini da ya fita daga jikin halitta a “ƙasa.” (Kubawar Shari’a 12:22-24) Ko da yake wasu za su ƙi karin jini ko kuma karɓan waɗannan abubuwa huɗu da suka haɗu suka zama jini, suna iya amincewa da magani da ya ƙunshi sinadarai daga waɗannan abubuwa huɗu. Za su yi tunanin cewa irin waɗannan ba sa kuma wakiltan ran halitta da aka ɗauki jini daga jikinsa.

Sa’ad da za ka yanke shawara game da sinadari da aka samu daga abubuwa huɗu na jini, ka yi tunani a kan waɗannan tambayoyi: Na sani cewa ƙin dukan waɗannan sinadarai da aka samu daga jini yana nufin ba zan karɓi magunguna da suka ƙunshi waɗannan sinadarai domin magance wata cuta ko kuma domin hana jini zuba ta wajen sa jinin ya daskare ba? Zan iya yi wa likita bayanin dalilin da ya sa na ƙi ko na amince da amfani da ɗaya ko fiye da haka na abubuwa da suka zama jini?

Hanyoyin fiɗa. Wannan ya haɗa da hemodilution da cell salvage. Hemodilution yana nufin karkata hanyar jini daga jikin mutum, a sake shi da ruwan magani, sai daga baya a mai da hanyar jinin cikin jikin mutum. Cell salvage yana tare jini kuma ya mayar da shi cikin jikin mutum a lokacin fiɗa. Ana samun jini daga ciwo ko kuma wani rami na jiki, a wanke ko kuma a tace shi, sai kuma a mayar da shi cikin jikin mutum. Domin wannan tsarin ya bambanta daga likita zuwa likita, ya kamata Kirista ya tambayi likitansa abin da yake nufi.

Sa’ad da kake yanke shawara game da wannan ka tambayi kanka: ‘Idan za a karkata hanyar jini daga jikina kuma a dakatar da tafiyar jinina na ɗan lokaci, lamiri na zai ƙyale ni in ɗauki wannan jinin a kan matsayin ɓangaren jiki na ne, saboda haka ba a bukatar a zubar da shi a “ƙasa”? (Kubawar Shari’a 12:23, 24) Lamiri na da aka koyar da Littafi Mai Tsarki zai dame ni ne idan a lokacin fiɗa aka ja jinina aka haɗa da magani aka sake mayar a jikina? Na sani cewa idan na ƙi dukan wata hanyar magani da ta ƙunshi amfani da jinina, hakan yana nufin cewa ba zan yarda a gwada jinina ba, da kuma wasu hanyoyin yin magani?’

Taswira a shafi na 216

Dole ne Kirista ya yanke shawara wa kansa game da yadda za a bi da jininsa a lokacin fiɗa. Hakan kuma ya shafi gwaji da kuma wasu hanyoyin magani da za a ja jinin mutum, bayan an haɗa da wasu magunguna sai a mayar cikin jikin mutum.

TAMBAYOYI GA LIKITOCI

Idan kana fuskantar fiɗa ko kuma magani da zai ƙunshi sinadarai da aka samu daga cikin jini, ka duba ka ga ko ka cika bukatun doka, irin su Health Care Proxy, (ba wani izini ya yi magana a madadinka), wanda an shirya ne domin ya kāre ka daga ƙarin jini. Ƙari ga haka, za ka iya tambayar likitanka waɗannan tambayoyi na gaba:

  • Dukan malaman kiwon lafiya sun sani cewa ni Mashaidin Jehobah ne, kuma na ba da umurni cewa ba na so ƙarin jini (jini, jajayen ƙwan halitta, farare, kamewar jini, ko kuma ruwan jini) a cikin kowane irin yanayi?

  • Idan za a ba ni magani da ya ƙunshi sinadari daga jini, menene sauran abubuwa da ke ciki? Yaya yawan magani da za a ba ni, kuma ta yaya za a ba ni?

  • Idan lamiri na ya ƙyale ni na karɓi sinadari daga jini, wane haɗari ne ke tattare da wannan? Wace hanya kuma ake da ita na magance wannan cutar?

Kafin ka zaɓi kowane iri, ka furta damuwarka ga Jehobah cikin addu’a. Ya yi alkawari zai ba waɗanda suka ci gaba da “roƙo” tare da bangaskiya, hikima.—Yaƙub 1:5, 6.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba