Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • th darasi na 1 p. 4
  • Gabatarwa Mai Dadi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Gabatarwa Mai Dadi
  • Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Nuna Yadda Za Su Amfana
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
th darasi na 1 p. 4

DARASI NA 1

Gabatarwa Mai Daɗi

Nassin da aka rubuta

Ayyukan Manzanni 17:22

ABIN DA ZA KA YI: Gabatarwarka ta zama wadda za ta jawo hankali, ta yi daidai da jigon jawabin ta kuma nuna wa masu sauraron yadda za su amfana daga batun.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka ja hankalin mutane. Ka yi amfani da tambaya ko labarin wani ko abin da ka ji a rediyo ko talabijin da zai ja hankalin masu sauraronka.

    Shawar mai amfani

    Ka yi tunani sosai a kan batutuwan da masu sauraronka suke so da abubuwan da ke damunsu, sai ka yi amfani da gabatarwar da ta shafi batun.

  • Ka bayyana jigon jawabin. Ka tabbata cewa gabatarwarka ta yi daidai da jigon jawabinka da kuma saƙon da ke ciki.

  • Ka nuna yadda batun yake da muhimmanci. Ka faɗi abin da ya fi damun masu sauraronka. Ka sa su fahimci yadda batun zai iya taimaka musu.

    Shawar mai amfani

    A lokacin da kake shirya jawabinka, ka tambayi kanka, ‘Waɗanne irin matsaloli ne ’yan’uwa maza da mata a ikilisiya suke fuskanta?’ Hakan zai sa ka yi amfani da gabatarwa da ta yi daidai da bukatunsu.

SA’AD DA KAKE WA’AZI

Don sanin abin da mutane suke so, ka lura da irin aikin da suke yi. Gidan yana da ado ne? Akwai yara a gidan? Da dai sauransu. Ka soma tattauna da shi ta wurin yi masa tambaya game da waɗannan abubuwan.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba