DARASI NA 13
Ka Nuna Yadda Za Su Amfana
Karin Magana 3:21
ABIN DA ZA KA YI: Ka taimaka wa masu sauraronka su fahimci yadda batun da kake tattaunawa ya shafe su kuma ka nuna abin da ya kamata su yi.
YADDA ZA KA YI HAKAN:
Ka yi tunani game da masu sauraronka. Ka yi tunani a kan dalilin da ya sa masu sauraronka suke bukatar su ji saƙon kuma ka zaɓi batutuwa da za su amfane kowannensu.
Ka nuna wa masu sauraronka abin da ya kamata su yi yayin da kake jawabi. Tun daga farko, ka taimaka wa masu sauraronka su ga cewa batun zai amfane kowannensu. A lokacin da kake bayyana muhimman darussa, ka nuna yadda za su yi amfani da darussan. Kuma ka bayyana darussan dalla-dalla.