Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • th darasi na 14 p. 17
  • Muhimman Bayanan Su Fita Dalla-Dalla

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Muhimman Bayanan Su Fita Dalla-Dalla
  • Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Tuna da Muhimman Darussan
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Kammalawa Mai Dadi
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
th darasi na 14 p. 17

DARASI NA 14

Muhimman Bayanan Su Fita Dalla-Dalla

Nassin da aka ambata

Ibraniyawa 8:1

ABIN DA ZA KA YI: Ka taimaka wa masu sauraronka su riƙa bin jawabin, kuma ka nuna musu yadda muhimman bayanan suka jitu da jigon da kuma darasin.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka kasance da manufa. Ka bincika ka ga ko manufar jawabin shi ne a sanar da su ko tabbatar musu da wani batu, ko kuma ƙarfafa su su yi wani abu. Ka tabbata cewa abin da za ka tattauna zai taimaka maka ka cim ma manufar jawabin.

    Shawara mai amfani

    Ka tambayi kanka: ‘Waɗanne tambayoyi ne suke zukatan masu sauraro? Idan na amsa tambayoyin nan, wace tambaya ce za ta iya tasowa?’ Sai ka jera darussan daidai yadda masu sauraronka za su iya bi, su fahimta kuma su karɓi abin da kake cewa.

  • Ka riƙa nanata jigon jawabinka. Sa’ad da kake tattaunawar, ka riƙa nanata jigon jawabinka. Kana iya sake maimaita kalamai ko furucin da suka jitu da jigon.

  • Ka sa bayanan su fita sarai da kuma sauƙin fahimta. Ka zaɓi batutuwan da suka jitu da jigon jawabinka don ka iya gama aikin daidai kan lokaci. Kada bayanan su yi yawa, amma su fita sarai. Ka riƙa dakatawa sa’ad da kake magana don masu sauraron su fahimce su da kyau. Ka gama bayanin kafin ka shiga na gaba.

    Shawara mai amfani

    Za ka iya ambata muhimman darussan a farkon jawabinka ko kuma ka nanata su sa’ad da kake kammalawa don masu sauraro su tuna.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba