Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • th darasi na 8 p. 11
  • Misalai Masu Amfani

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Misalai Masu Amfani
  • Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Makamantan Littattafai
  • “Ba Ya Faɗa Musu Kome Ba Sai Game Da Misali”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ka Yi Koyi Da Babban Malami
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Yin Amfani da Misalai
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Abubuwa Uku da Za Su Inganta Koyarwarka
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
th darasi na 8 p. 11

DARASI NA 8

Misalai Masu Amfani

Nassin da aka rubuta

Matiyu 13:​34, 35

ABIN DA ZA KA YI: Ka inganta koyarwarka da misalai masu sauƙi da za su ratsa zuciyar masu sauraro. Misalan su koyar da darussa masu muhimmanci.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka yi amfani da misalai masu sauƙi. Kamar Yesu, ka yi amfani da misalan da mutane suka saba da su don ka bayyana musu gaskiya. Kar ka yi bayani mai yawa don kada misalin ya yi wuyar fahimta. Ka tabbata cewa misalin ya yi daidai da darasin da kake so su fahimta don kada ka raba hankalin masu sauraronka.

    Shawara mai amfani

    Ka riƙa lura da abubuwa da suke faruwa kewaye da kai. Ka riƙa nazarin littattafanmu sosai kuma ka saurara da kyau yayin da ’yan’uwa da suka ƙware suke koyarwa. Yayin da kake yin hakan, ka lura da misalan da za ka iya yin amfani da su don ka inganta yadda kake koyarwa. Ka rubuta su.

  • Ka yi tunani a kan abin da zai amfane masu sauraronka. Ka yi amfani da misalin da masu sauraronka suka saba da shi. Kada ka yi amfani da misalin da zai ɓata musu rai ko ya sa su ji kunya.

  • Ka koya musu ainihin darasin. Ka yi amfani da misalai don fitar da muhimman darussan da kake koyarwa. Ka tabbata cewa masu sauraro sun tuna darasin da suka koya daga misalin ba misalin kawai ba.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba