Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lff darasi na 14
  • Me Za Ka Yi don Allah Ya Amince da Bautarka?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Za Ka Yi don Allah Ya Amince da Bautarka?
  • Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA YI BINCIKE SOSAI
  • TAƘAITAWA
  • KA BINCIKA
  • Yin Ibada ta Gaskiya Za Ta Sa Ka Daɗa Yin Farin Ciki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Ta Yaya Za Ka Amfana Daga Taron Shaidun Jehobah?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Yadda Ya Dace a Bauta wa Allah
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Ka Taimaka a Ikilisiyarku
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
lff darasi na 14
Darasi na 14. Shaidun Jehobah da baki suna waka a taron ikilisiya.

DARASI NA 14

Me Za Ka Yi don Allah Ya Amince da Bautarka?

Hoto
Hoto
Hoto

Kamar yadda muka tattauna a darasin da ya gabata, Allah ba ya amincewa da dukan addinai. Duk da haka, za mu iya bauta wa Mahaliccinmu a hanyar da za ta sa shi farin ciki. Amma, wacce irin bauta ko kuma “addini” ne Allah yake amincewa da shi? (Yakub 1:27) Bari mu ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce.

1. A ina ne za mu koyi yadda za mu bauta wa Allah a hanyar da ta dace?

Za mu koyi yadda za mu yi hakan a cikin Littafi Mai Tsarki. Yesu ya ce wa Allah: “Kalmarka . . . ita ce gaskiya.” (Yohanna 17:17) Wasu addinai suna yin watsi da gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki don su bi koyarwar ’yan Adam da kuma al’adunsu. Jehobah ba ya farin ciki da waɗanda suke ‘barin umarninsa.’ (Karanta Markus 7:9.) Amma zai yi farin ciki idan muna bin shawarar da ke Littafi Mai Tsarki a bautarmu.

2. Ta yaya za mu bauta wa Jehobah?

Jehobah ne Mahaliccinmu, saboda haka ya kamata mu bauta masa shi kaɗai. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:11) Hakan yana nufin cewa wajibi ne mu ƙaunace shi kuma mu bauta masa shi kaɗai ba tare da yin amfani da gunki ko hoto ko kuma wani abu ba.​—Karanta Ishaya 42:8.

Wajibi ne bautarmu ta zama “mai tsarki, da kuma abin karɓa” ga Jehobah. (Romawa 12:1) Hakan yana nufin cewa muna bukatar mu riƙa bin dokokinsa. Alal misali, waɗanda suke ƙaunar Jehobah suna bin dokokinsa game da aure. Kuma suna guje wa halaye marasa kyau kamar, shan taba ko ƙwaya da kuma buguwa da giya.a

3. Me ya sa zai dace mu bauta wa Jehobah tare da mutanensa?

Zuwa taro kowane mako, yana ba mu damar mu “yabi Yahweh . . . a cikin taron jama’a.” (Zabura 111:​1, 2) Wata hanyar da muke yin hakan, ita ce ta wajen rera waƙar yabo ga Allah. (Karanta Zabura 104:33.) Jehobah yana so mu riƙa zuwa taro domin yana ƙaunar mu kuma ya san yin hakan zai taimaka mana mu ji daɗin rayuwa har abada. A taro, mukan ƙarfafa juna.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi dalilin da ya sa Jehobah ba ya so mu yi amfani da gumaka a bautarmu. Za mu kuma ga wasu muhimman hanyoyin da za mu iya yabon Allah.

4. Bai kamata mu yi amfani da gumaka a bautarmu ba

Ta yaya muka san cewa yin hakan zai ɓata wa Allah rai? Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

BIDIYO: Allah Yana So Mu Yi Amfani da Siffofi a Ibada Kuwa? (3:26)

Hotuna: 1. Wani mutum yana addu’a da kwanukan abinci a gabansa a gaban wani gunki. 2. Wani mutum yana rike da carbi yana addu’a a gaban gunkin Maryamu.
  • Me ya faru sa’ad da wasu bayin Allah a zamanin dā suka yi ƙoƙari su yi amfani da gunki a bautarsu?

Wasu mutane suna amfani da gumaka don suna zato zai sa su kusaci Allah sosai. Amma yin haka zai taimaka musu su kusace Allah kuwa? Ku karanta Fitowa 20:​4-6 da Zabura 106:​35, 36, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Waɗanne abubuwa ne kake ganin mutane suke amfani da su a bautarsu?

  • Yaya Jehobah yake ɗaukan yin amfani da gumaka a bauta?

  • Kana ganin yin amfani da gumaka a bautarmu ya dace ne?

5. Bauta wa Jehobah shi kaɗai yana sa mu sami ’yanci daga ƙaryace-ƙaryace

Ku ga yadda bauta wa Jehobah a hanyar da ta dace za ta iya ’yantar da mu daga ƙaryace-ƙaryace. Ku kalli BIDIYON nan.

BIDIYO: Sanin Gaskiya Ya Sa Na Samu ’Yanci (5:​16)

Ku karanta Zabura 91:​14, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Wane lada ne Jehobah zai ba mu idan muka nuna cewa muna ƙaunar sa ta wajen bauta masa shi kaɗai?

6. Muna bauta wa Jehobah a taron ikilisiya

Muna yabon Jehobah da kuma ƙarfafa juna sa’ad da muke waƙa da kuma yin kalami a taro. Ku karanta Zabura 22:​22, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Ka ji daɗin kalamin da ake yi a taronmu?

  • Za ka so ka shirya kuma ka yi kalami a taro?

Hotuna: Wata tana koyan yadda ake bauta wa Allah a hanyar da ta dace. 1. Tana wakar yabo ga Allah a taron ikilisiya. 2. Tana yin kalami a taron ikilisiya. 3. Tana nuna wa wata mata da ’yarta bidiyo.

7. Jehobah yana farin ciki idan muna gaya wa mutane abin da muke koya

Akwai hanyoyi da yawa da za mu iya gaya wa mutane gaskiyar da muke koya. Ku karanta Zabura 9:1 da 34:1, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Mene ne ka koya daga Littafi Mai Tsarki da za ka so ka gaya wa wani?

WASU SUN CE: “Kowa zai iya bauta wa Allah yadda yake so.”

  • Mene ne ra’ayinka?

TAƘAITAWA

Mahaliccinmu zai yi farin ciki idan muna bauta masa shi kaɗai, muna yabonsa a taron ikilisiya, kuma muna gaya wa mutane abin da muka koya.

Bita

  • Ta yaya za mu koyi yadda za mu bauta wa Allah?

  • Me ya sa ya dace mu riƙa bauta wa Jehobah shi kaɗai?

  • Me ya sa ya dace mu riƙa bauta wa Jehobah tare da mutanen da suke so su faranta masa rai?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan mai jigo “Na Daina Bauta wa Gumaka” don ku ga yadda wata mata ta daina bauta wa gumaka.

“Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Oktoba, 2011)

Ku karanta talifin nan don ku ga abin da zai taimaka muku ku yi kalami a taron ikilisiya.

“Mu Yabi Jehobah a Cikin Ikilisiya” (Hasumiyar Tsaro, Janairu 2019)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda wani matashi ya amfana sa’ad da ya halarci taro duk da cewa hakan bai yi masa sauƙi ba.

Jehobah Ya Kula Da Ni (3:07)

Mutane da yawa sun ce ya dace a yi amfani da gicciye, wato kuros a bauta. Ku karanta talifin nan don ku ga ko hakan ya dace.

“Me Ya Sa Ba Ku Amfani da Gicciye a Sujjadarku?” (Talifin jw.org)

a Za a tattauna waɗannan batutuwan a darussa na gaba.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba