DARASI NA 26
Me Ya Sa Akwai Mugunta da Wahala a Ko’ina?
Sa’ad da wani mummunan abu ya faru, mutane sukan ce: “Me ya sa abin ya faru?” Muna farin ciki domin Littafi Mai Tsarki ya amsa tambayar!
1. Me Shaiɗan ya yi da ya sa aka soma mugunta a duniya?
Shaiɗan ya yi wa Allah tawaye. Yana so ya mulki mutane, shi ya sa ya ruɗi Adamu da Hauwa’u su yi tawaye da Allah. Shaiɗan ya yi hakan ta wajen yi wa Hauwa’u ƙarya. (Farawa 3:1-5) Ya sa ta soma gani kamar akwai wani abu mai kyau da Jehobah ba ya so ta samu. Yana ƙoƙari ya nuna cewa mutane za su fi jin daɗi idan ba sa biyayya ga Allah. Shaiɗan ya tabka ƙarya na farko ta wurin gaya wa Hauwa’u cewa ba za ta mutu ba. Don haka, Littafi Mai Tsarki ya ce Shaiɗan “mai ƙarya ne, uban ƙarya kuma.”—Yohanna 8:44.
2. Me Adamu da Hauwa’u suka yi?
Jehobah ya ba wa Adamu da Hauwa’u abubuwa da yawa. Ya ce za su iya cin dukan ’ya’yan itatuwan da ke lambun Adnin, amma ban da guda ɗaya. (Farawa 2:15-17) Duk da haka, sun ci ’ya’yan itacen da aka hana su. Hauwa’u ta ‘tsinki’ ’ya’yan itacen ta ci. Daga baya, sai Adamu “ma ya ci.” (Farawa 3:6) Adamu da Hauwa’u sun yi wa Allah rashin biyayya. Da yake su kamiltattu ne kafin su yi zunubi, yana da sauƙi su yi abin da ya dace. Amma sun yanke shawarar yi wa Allah rashin biyayya, ta yin hakan sun yi zunubi kuma suka ƙi sarautar Allah. Shawarar da suka yanke ta sa sun sha wahala sosai.—Farawa 3:16-19.
3. Ta yaya shawarar Adamu da Hauwa’u ta shafe mu?
Da Adamu da Hauwa’u suka yi zunubi, sai suka zama ajizai kuma ta haka ne dukan ’ya’yansu suka zama ajizai. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya, zunubin nan kuwa shi ya jawo mutuwa, ta haka mutuwa ta bi ta shiga dukan ’yan Adam.”—Romawa 5:12.
Akwai abubuwa da yawa da suke sa mu shan wahala. A wani lokaci, mukan sha wahala don mun yanke shawarar da ba ta dace ba. Ban da haka, mukan sha wahala don shawara marar kyau da wasu suka tsai da. Wani lokaci kuma, muna shan wahala don muna wurin da bai dace ba, a lokacin da bai dace ba.—Karanta Mai-Wa’azi 9:12.
KA YI BINCIKE SOSAI
Za mu san dalilin da ya sa ba Allah ba ne yake jawo mugunta da wahala a duniya da kuma yadda yake ji sa’ad da muke shan wahala.
4. Waye ne yake jawo wahalar da muke sha?
Mutane da yawa suna gani kamar Allah ne yake iko da duniya. Hakan gaskiya ne kuwa? Ku kalli BIDIYON nan.
Ku karanta Yakub 1:13 da 1 Yohanna 5:19, sai ku tattauna tambayar nan:
Shin Allah ne yake jawo wahala da mugunta?
5. Mene ne ya faru tun lokacin da Shaiɗan ya soma iko da duniya?
Ku karanta Farawa 3:1-6, sai ku tattauna tambayoyin nan:
Wace ƙarya ce Shaiɗan ya yi?—Ka duba ayoyi na 4 da 5.
Ta yaya Shaiɗan yake sa mutane su ga kamar Jehobah ba ya so su ji daɗi?
Ta yaya Shaiɗan ya yi da’awa cewa ’yan Adam ba sa bukatar ja-gorancin Jehobah don su yi farin ciki?
Ku karanta Mai-Wa’azi 8:9, sai ku tattauna tambayar nan:
Me ya faru tun lokacin da Jehobah ya daina iko da duniya?
Adamu da Hauwa’u kamiltattu ne kuma a Aljanna aka saka su. Amma sun bi Shaiɗan kuma suka yi wa Jehobah rashin biyayya
Bayan Adamu da Hauwa’u sun yi tawaye, duniya ta cika da zunubi da wahala da kuma mutuwa
Jehobah zai kawar da zunubi da wahala da kuma mutuwa. Bayan haka, ’yan Adam za su zama kamiltattu kuma su zauna a Aljanna
6. Jehobah ya damu don wahalar da muke sha
Shin Allah ya damu don wahalar da muke sha? Bari mu ga abin da Sarki Dauda da manzo Bitrus suka rubuta. Ku karanta Zabura 31:7 da 1 Bitrus 5:7, sai ku tattauna tambayar nan:
Yaya ka ji sa’ad da ka san cewa Jehobah yana ganin wahalar da muke sha kuma ya damu da mu?
7. Allah zai kawar da dukan wahala
Ku karanta Ishaya 65:17 da Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:3, 4, sai ku tattauna tambayar nan:
Me ya sa sanin cewa Jehobah zai kawar da dukan wahalar da ’yan Adam suke sha yake ƙarfafa mu?
Ka sani?
Shaiɗan ya ɓata sunan Jehobah sa’ad da ya tabka ƙarya na farko. Kuma ya sa mutane tunanin da bai dace ba game da Jehobah, sa’an nan suna ganin kamar shi ba Allah mai adalci ba ne. Nan ba da daɗewa ba, Jehobah zai tsarkake sunansa sa’ad da ya kawar da wahalar da mutane suke sha. Ta yin haka, zai nuna cewa sarautarsa ce ta fi kyau. Tsarkake sunan Jehobah batu ne da ya fi muhimmanci a sama da duniya.—Matiyu 6:9, 10.
WASU SUN CE: “Ai nufin Allah ne mu sha wahala.”
Mene ne ra’ayinka?
TAƘAITAWA
Shaiɗan da Adamu da Hauwa’u ne suka jawo mugunta da ke duniya a yau. Jehobah ya damu don muna shan wahala kuma nan ba da daɗewa ba, zai kawar da dukan matsalolinmu.
Bita
Wace ƙarya ce Shaiɗan ya tabka wa Hauwa’u?
Ta yaya rashin biyayyar Adamu da Hauwa’u ya shafe mu?
Ta yaya muka san cewa Jehobah ya damu don wahalar da muke sha?
KA BINCIKA
Ku karanta talifin nan don ku ga abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da zunubi.
Ku karanta talifin nan don ku ga ƙarin bayani game da batun da Shaiɗan ya tayar a lambun Adnin.
“Me Ya Sa Allah Ya Ƙyale Mutane Su Sha Wahala?” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Maris, 2014)
Ku karanta talifin nan don ku sami amsoshin wata tambaya mai wuya.
“Me Ya Sa Ake Kisan Kare Dangi? Me Ya Sa Allah Ya Ƙyale Hakan Ya Faru?” (Talifin jw.org)
Ku kalli bidiyon nan don ku ga abin da wani mutum ya koya game da wahalar da mutane suke sha.