Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lff darasi na 18
  • Yadda Za Ka San Kiristoci na Gaske

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za Ka San Kiristoci na Gaske
  • Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA YI BINCIKE SOSAI
  • TAƘAITAWA
  • KA BINCIKA
  • Shaidun Jehobah Kiristoci Ne na Gaske?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ina Yadda Zaka Sami Addini na Gaskiya?
    Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
  • Su Wane ne Suke Wa’azin Labari Mai Dadi?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Waɗanne Irin Halaye Ne Yesu Yake da Su?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
lff darasi na 18
Darasi na 18. Yesu ya ba almajiransa umurni kuma ya tura su bibbiyu su yi wa’azi.

DARASI NA 18

Yadda Za Ka San Kiristoci na Gaske

Hoto
Hoto
Hoto

Akwai biliyoyin mutane a yau da suke cewa su Kiristoci ne. Amma sun yi imani da abubuwa dabam-dabam, kuma ba sa bin ƙa’idodi ɗaya. Ta yaya, za mu san Kiristoci na gaske?

1. Su Waye ne Kiristoci?

Kiristoci almajirai ko mabiyan Yesu Kristi ne. (Karanta Ayyukan Manzanni 11:26.) Ta yaya suke nuna cewa su almajiran Yesu ne? Yesu ya ce: “In dai kun ci gaba da riƙe koyarwata, ku almajiraina ne na gaske.” (Yohanna 8:31) Hakan yana nufin cewa wajibi ne Kiristoci na gaske su riƙa bin koyarwar Yesu. Yesu ya koyar da abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki, mabiyansa na gaske ma suna yin hakan.​—Karanta Luka 24:27.

2. Ta yaya Kiristoci na gaske suke nuna ƙauna?

Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa: “Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku.” (Yohanna 15:12) Ta yaya Yesu ya nuna cewa yana ƙaunar almajiransa? Ya kasance tare da su, ya ƙarfafa su kuma ya taimaka musu. Har ma ya ba da ransa dominsu. (1 Yohanna 3:16) Hakazalika, Kiristoci na gaske suna nuna ta furucinsu da ayyukansu cewa suna ƙaunar juna sosai.

3. Wane aiki ne Kiristoci na gaske suke yi?

Yesu ya ba almajiransa aiki. “Ya . . . aike su su je su yi wa’azin mulkin Allah.” (Luka 9:2) Ba a wuraren ibada ne kawai Kiristoci na farko suka yi wa’azi ba, amma sun je wasu wurare har da gidajen mutane. (Karanta Ayyukan Manzanni 5:42; 17:17.) Kiristoci na gaske a yau ma suna wa’azi a duk inda suka sami mutane. Suna amfani da lokaci da kuzarinsu wajen koya wa mutane abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki don suna ƙaunar su. Hakan zai sa su sami bege kuma zai ƙarfafa su.—Markus 12:31.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi abin da ya bambanta Kiristoci na gaske da mutanen da ba sa bin koyarwar Yesu da misalinsa.

4. Sun bincika koyarwar Littafi Mai Tsarki

Kiristoci biyu a karni na farko suna karanta nadadun Littafi Mai Tsarki don su san gaskiya.

Kiristoci na farko sun daraja Kalmar Allah

Wasu mutane da suka ce su Kiristoci ne ba sa ganin yana da muhimmanci su fahimci koyarwar Littafi Mai Tsarki ko kuma su yi amfani da ita. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

BIDIYO: Yadda Kiristoci Suka Bijire wa Koyarwar Kristi (5:11)

  • Ta yaya wasu addinai da suke da’awa cewa su Kiristoci ne suka hana mutane koya game da Yesu?

Yesu ya koyar da gaskiya da ke Kalmar Allah. Ku karanta Yohanna 18:​37, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Kamar yadda Yesu ya ce, ta yaya za mu san Kiristoci da ke koyar da “gaskiya”?

5. Suna koyar da gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki

Kiristoci a karni na farko suna yi wa mutane wa’azi a gidajensu.

Kiristoci na farko sun yi wa mutane wa’azi

Kafin Yesu ya koma sama, ya ba mabiyansa aiki mai muhimmanci da suke yi har wa yau. Ku karanta Matiyu 28:​19, 20 da Ayyukan Manzanni 1:​8, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Kiristoci za su yi wa’azi har zuwa wane lokaci, kuma a waɗanne wurare ne za su yi hakan?

6. Suna yin abin da suke koyarwa

Mene ne ya tabbatar ma wani mutum mai suna Tom cewa ya koyi gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki? Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

BIDIYO: Na Gaji da Batun Addini (5:20)

  • A bidiyon, me ya sa Tom ya gaji da addini?

  • Me ya tabbatar masa cewa ya gano addini na gaskiya?

Idan mutum ya ce shi mabiyin Yesu ne, ya kamata ya nuna hakan ta ayyukansa. Ku karanta Matiyu 7:​21, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Kamar yadda Yesu ya faɗa, me ya sa muke bukatar mu nuna ta ayyukanmu cewa mu mabiyansa ne?

7. Suna ƙaunar juna

Mama da baba da ’yarsu a karni na farko sun kawo wa wani iyali kwandon abinci.

Kiristoci na farko sun ƙaunaci juna

Shin Kiristoci sun taɓa saka ransu cikin haɗari don su ceci ’yan’uwansu? Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

BIDIYO: Ya Ce Gwamma A Kashe Shi (2:55)

  • A bidiyon, me ya sa Ɗan’uwa Lloyd ya saka ransa cikin haɗari don ya ceci Ɗan’uwa Johansson?

  • Kana ganin ya ɗauki mataki kamar Kirista na gaske?

Ku karanta Yohanna 13:​34, 35, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Ta yaya Kiristoci na gaske suke ɗaukan mutane daga wasu ƙasashe ko ƙabilu?

  • Ta yaya za su yi hakan a lokacin da ake yaƙi?

WASU SUN CE: “Dukanmu muna bauta wa Allah ɗaya, ko da wane addini ne muke bi.”

  • Wane nassi ne za ka iya karanta ma wani don ka nuna masa yadda za mu san Kiristoci na gaske?

TAƘAITAWA

Kiristoci na gaske suna bin koyarwar Littafi Mai Tsarki, suna ƙaunar juna sosai kuma suna koyar da gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

Bita

  • Mene ne tushen koyarwar Kiristoci na gaske?

  • Wane hali ne aka fi sanin Kiristoci na gaske da shi?

  • Wane aiki ne Kiristoci na gaske suke yi?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku kalli bidiyon nan don ku ƙara koya game da mutanen da suke iya ƙoƙarinsu don su yi koyi da Yesu Kristi kuma su yi amfani da koyarwarsa.

Su Wane ne Shaidun Jehobah? (1:13)

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda wata da ke hidima a wani coci ta sami “’yan’uwa na gaske.”

“Sun Yi Amfani da Littafi Mai Tsarki don Su Amsa Dukan Tambayoyin!” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Afrilu, 2014)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda Kiristoci na gaske suka nuna ƙauna ga ’yan’uwan da suke bukatar taimako.

Yadda Muke Taimaka wa ’Yan’uwanmu a Lokacin Bala’i​—Gajeren Bidiyo (3:57)

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda Kiristoci na gaske suke yin abubuwan da Kiristoci na farko suka yi da ke nuna cewa su mabiyan Yesu ne.

“Mene Ne Alamun Kiristoci na Gaskiya?” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Yuli, 2012)

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba