Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lff darasi na 44 sakin layi na 1-6
  • Dukan Bukukuwa Ne Allah Yake Amincewa da Su?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Dukan Bukukuwa Ne Allah Yake Amincewa da Su?
  • Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA YI BINCIKE SOSAI
  • TAƘAITAWA
  • KA BINCIKA
  • Ka Yanke Shawarar Bauta wa Allah
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Dukan Bukukuwa Ne Allah Yake So?
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Me Ya Sa Shaidun Jehobah Ba Sa Yin Wasu Bukukuwa?
    Tambayoyin da Ake Yawan Yi
  • Ka Dage Domin Bauta ta Gaskiya
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
Dubi Ƙari
Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
lff darasi na 44 sakin layi na 1-6
Darasi na 44. Daruruwan mutane suna sake wuta a sama da daren a lokacin wani biki.

DARASI NA 44

Dukan Bukukuwa Ne Allah Yake Amincewa da Su?

Hoto
Hoto
Hoto

Jehobah yana so mu ji daɗin rayuwa kuma mu yi biki a wasu lokuta. Amma dukan bukukuwa ne Allah yake amincewa da su? Ta yaya za mu nuna muna ƙaunar Jehobah a wannan batun?

1. Me ya sa Jehobah ya tsani bukukuwa da yawa da ake yi a yau?

Ka san cewa bukukuwa da yawa da ake yi a yau ba su jitu da koyarwar Littafi Mai Tsarki ba? Wasu bukukuwan suna da alaƙa da addinin ƙarya. Wasu kuma suna da alaƙa da sihiri ko camfi ko koyarwar rai marar mutuwa ko kuma allolin sa’a da ƙaddara. (Ishaya 65:11) Jehobah ya gargaɗi bayinsa cewa “Ku ware kanku, . . . Kada ku haɗa kanku da wani abu mai ƙazanta.”​—2 Korintiyawa 6:17.a

2. Yaya Jehobah yake ji game da bukukuwan da ke ɗaukaka ’yan Adam?

Jehobah ya gargaɗe mu cewa kada mu “dogara ga ɗan Adam.” (Karanta Irmiya 17:5.) Wasu bukukuwa suna ɗaukaka shugabanni ko kuma sojoji. Wasu suna bikin ranar da ƙasarsu ta sami ’yanci. (1 Yohanna 5:21) Har ila, wasu suna bikin ɗaukaka ƙungiyoyin siyasa ko kuma na jama’a. Yaya Jehobah zai ji idan muka ɗaukaka wani mutum ko ƙungiyar da suke yin abin da ba ya so?

3. Waɗanne abubuwa ne ake yi a bukukuwan da ba su dace ba?

Littafi Mai Tsarki ya haramta “buguwa, da bukukuwan shaye-shaye, da fitar shan iska ta lalata.” (1 Bitrus 4:3) A wasu bukukuwa, mutane suna yin abin da suka ga dama har da lalata. Don mu ci gaba da zama abokan Jehobah, muna bukatar mu guji waɗannan halayen.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yadda za mu faranta ran Jehobah ta wajen yanke shawarwari masu kyau game da bukukuwa.

Abokin aikin wani dan’uwa yana ba shi kyauta a lokacin bikin Kirsimati.

4. Ka guji bukukuwan da ba sa ɗaukaka Jehobah

Ku karanta Afisawa 5:​10, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Mene ne ya kamata mu tabbatar kafin mu yanke shawara yin wani biki?

  • Waɗanne bukukuwa ne ake yi a yankinku?

  • Kana ganin waɗannan bukukuwan suna faranta ran Jehobah?

Alal misali, ka taɓa tunani ko mene ne ra’ayin Allah game da bikin ranar haihuwa? Babu inda aka ambata a Littafi Mai Tsarki cewa wani bawan Jehobah ya yi bikin ranar haihuwarsa. Amma akwai bikin ranar haihuwa na mutane biyu da ba su bauta wa Jehobah ba. Ku karanta Farawa 40:​20-​22 da Matiyu 14:​6-10. Sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Wace alaƙa ce ke tsakanin bikin ranar haihuwa nan guda biyu?

  • Kamar yadda aka nuna a waɗannan labaran, yaya kake ganin Jehobah yake ɗaukan bikin ranar haihuwa?

Har ila kana iya yin tunani cewa, ‘Shin Jehobah ya damu ne ko na yi bikin ranar haihuwa ko kuma bukukuwan da suka saɓa wa koyarwar Littafi Mai Tsarki?’ Ku karanta Fitowa 32:​1-8. Sai ku kalli BIDIYON nan kuma ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

BIDIYO: Hutu da Bukukuwan da Allah Ba Ya So (5:​07)

  • Me ya sa muke bukatar mu san abubuwan da Jehobah ya amince da su?

  • Ta yaya za mu iya yin hakan?

Ta yaya za mu san bikin da Allah ba ya so?

  • Bikin ya saɓa wa koyarwar Littafi Mai Tsarki ne? Ka bincika tushensa don ka sani.

  • Shin bikin yana ɗaukaka ’yan Adam ko ƙungiyoyi ko kuma tutar ƙasa? Muna ɗaukaka Jehobah fiye da kome kuma mun tabbata cewa zai kawar da dukan matsalolin ’yan Adam.

  • Al’adu da kuma abubuwan da ake yi a bikin sun saɓa wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne? Ya kamata ɗabi’unmu su kasance da tsabta.

5. Ka taimaka wa wasu su daraja abin da ka yi imani da shi

Idan mutane suka matsa maka ka yi bukukuwan da Jehobah ba ya so, zai iya yi maka wuya ka ce a’a. Amma za ka iya bayyana musu ra’ayinka cikin basira. Don ka ga yadda za ka yi hakan, ku kalli BIDIYON nan.

BIDIYO: Ka Bayyana Imaninka Cikin Basira (2:​01)

Ku karanta Matiyu 7:​12, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Kamar yadda ayar nan ta nuna, ya dace ne ka gaya wa ’yan’uwanka da ba sa bauta wa Jehobah kada su yi wani biki?

  • Me za ka yi don ka tabbatar wa iyalinka cewa kana ƙaunar su ko da ba za ka yi wasu bukukuwa tare da su ba?

6. Jehobah yana so mu yi farin ciki

Jehobah yana so mu ji daɗi tare da iyalanmu da abokanmu. Ku karanta Mai-Wa’azi 8:​15, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Ta yaya wannan ayar ta nuna cewa Jehobah yana so mu yi farin ciki?

Jehobah yana so bayinsa su yi farin ciki kuma su ji daɗi. Ku kalli BIDIYON nan don ku ga yadda muke yin hakan a taron ƙasashe.

BIDIYO: Nuna Alheri a Taron Ƙasa da Ƙasa (5:​40)

Ku karanta Galatiyawa 6:​10, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • A lokacin da ake yin bukukuwa ne kawai za mu iya “kyautata” wa mutane?

  • Wane irin ba da kyauta ne zai fi sa ka farin ciki, wanda aka ce wajibi ne ka bayar a lokacin wani biki, ko wanda ka bayar don kana so ka yi hakan?

  • A wasu lokuta, Shaidun Jehobah da yawa sukan shirya biki na musamman don su sa yaransu farin ciki ko su saya musu kyaututtuka. Idan kana da yara, waɗanne abubuwa na musamman ne za ka iya yi musu?

Wata yarinya tana karban kyautan da iyayenta suka saya mata.

WASU SUN CE: “Ai, lokacin bukukuwa lokacin jin daɗi da ’yan’uwa da abokan arziki ne. A ganina, yadda aka soma bikin bai da muhimmanci.”

  • Me za ka ce?

TAƘAITAWA

Jehobah yana so mu ji daɗi tare da ’yan’uwa da abokanmu. Amma yana so mu guji bukukuwan da ba ya so.

Bita

  • Waɗanne tambayoyi ne za mu iya yi, da za su taimaka mana mu san bukukuwan da Jehobah ba ya so?

  • Ta yaya za mu taimaka wa ’yan’uwa da abokanmu su fahimci ra’ayinmu game da wasu bukukuwa?

  • Ta yaya muka san cewa Jehobah yana so mu yi farin ciki kuma mu riƙa shaƙatawa?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga wasu bukukuwan da Kiristoci ba sa yi.

“Me Ya Sa Shaidun Jehobah Ba Sa Yin Wasu Bukukuwa?” (Talifin jw.org)

Ku karanta talifin nan don ku ga dalilai huɗu da suka sa muka yi imani cewa Allah bai amince da bikin ranar haihuwa ba.

“Me Ya Sa Shaidun Jehobah Ba Sa Bikin Ranar Haihuwa?” (Talifin jw.org)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda yara da ke ƙaunar Jehobah za su iya faranta masa rai a lokacin bukukuwa.

Kana da Daraja a Gaban Jehobah (11:35)

Ku karanta talifin nan don ku ga abin da ya sa miliyoyin Kiristoci suka yanke shawara cewa ba za su yi bikin Kirsimati ba.

“Sun Sami Abin da Ya Fi Kyau” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Disamba, 2012)

a Ka duba Ƙarin Bayani na 5 don ka san abin da za ka iya yi a lokacin wasu bukukuwa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba