DARASI NA 38
Ka Nuna Godiya don Ran da Allah Ya Ba Ka
Akwai abubuwa da yawa da za mu iya yi kuma mu ji daɗinsu don muna da rai. Ko da muna fama da matsaloli, akwai abubuwan da za mu iya jin daɗinsu a rayuwa. Ta yaya za mu nuna godiya don ran da Jehobah ya ba mu? Kuma wane dalili mafi muhimmanci ne zai sa mu yi hakan?
1. Me ya sa ya kamata mu daraja rai?
Ya kamata mu daraja rai domin kyauta ce daga wurin Ubanmu mai ƙauna, wato Jehobah. Shi ne “mai ba da . . . rai” kuma shi ne ya halicci dukan abubuwa. (Zabura 36:9) “Shi ne yake ba dukan mutane rai, da numfashi da dukan abubuwan da suke bukata.” (Ayyukan Manzanni 17:25, 28) Jehobah ya ba mu duk abubuwan da muke bukata don mu rayu. Ƙari ga haka, ya yi mana tanadin abubuwan da za su sa mu ji daɗin rayuwa.—Karanta Ayyukan Manzanni 14:17.
2. Ta yaya za mu gode wa Jehobah don ran da ya ba mu?
Jehobah ya damu da kai tun kana cikin mahaifiyarka. A Littafi Mai Tsarki, wani bawan Allah mai suna Dauda ya yi addu’a, ya ce: “Idanunka sun ga gaɓoɓin jikina kafin su cika.” (Zabura 139:16) Ran ɗan Adam yana da daraja sosai a wurin Jehobah. (Karanta Matiyu 10:29-31.) Jehobah yana baƙin ciki idan mutum ya kashe wani ko ya kashe kansa da gangan.a (Fitowa 20:13) Jehobah zai yi baƙin ciki idan muka sa ranmu da kuma na wasu a cikin haɗari. Idan muna kula da kanmu kuma muna daraja rayukan mutane, hakan ya nuna muna godiya don ran da Jehobah ya ba mu.
KA YI BINCIKE SOSAI
Za mu koyi yadda za mu nuna godiya don ran da Jehobah ya ba mu.
3. Ka kula da lafiyarka
Waɗanda suka yi alkawarin yin duk abin da Jehobah yake so, suna bauta masa da dukan ransu. Hakan ya yi kamar sun ba da ransu hadaya ga Allah. Ku karanta Romawa 12:1, 2, sai ku tattauna tambayoyin nan:
Mene ne zai sa ka kula da lafiyarka?
A waɗanne hanyoyi ne za ka yi hakan?
4. Ka mai da hankali don kada ka ji wa mutum rauni ko ka zama sanadiyyar mutuwar wani
Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu cewa mu guji ayyukan da za su jefa ranmu cikin haɗari. Ku kalli BIDIYON nan don ku ga wasu abubuwan da za su taimaka wa mutum ya riƙa kiyaye kansa.
Ku karanta Karin Magana 22:3, sai ku tattauna yadda kai da waɗansu za ku iya kiyaye kanku . . .
a gida.
a wurin aiki.
a wurin yin wasanni.
sa’ad da kake tuƙi ko an ɗauke ka a mota ko babur da dai sauran su.
5. Ka daraja ran jaririn da ba a haifa ba tukun
Dauda ya ce Jehobah ya san yadda jariri ke girma a cikin mahaifiyarsa. Ku karanta Zabura 139:13-17, sai ku tattauna tambayar nan:
Shin Jehobah yana ɗaukan jaririn da ba a haifa ba tukun a matsayin abu mai rai?
Dokokin da Jehobah ya ba Isra’ila ta dā sun kāre mata masu juna biyu. Ku karanta Fitowa 21:22, 23, sai ku tattauna tambayoyin nan:
Yaya Jehobah yake ɗaukan mutumin da ya kashe jaririn da ke cikin mahaifiyarsa ba da gangan ba?
Yaya Jehobah zai ji idan mutum ya yi hakan da gangan?b
Kana ganin ra’ayin Jehobah ya dace? Me ya sa?
Mace da take daraja rai za ta iya shiga wani yanayin da zai sa ta ɗauka cewa zub da ciki ne mafita. Ku karanta Ishaya 41:10, sai ku tattauna tambayoyin nan:
Idan an matsa wa mace ta zub da ciki, wa zai iya taimaka mata? Me ya sa?
WASU SUN CE: “Mace tana da ’yanci ta zub da ciki don jikinta ne.”
Mene ne ya tabbatar maka cewa Jehobah yana daraja ran mace da na jariri da ke cikinta?
TAƘAITAWA
Littafi Mai Tsarki ya ce mu riƙa ƙauna da daraja da kuma kiyaye ran da Jehobah ya ba mu. Hakan ya haɗa da ranmu da kuma na wasu.
Bita
Me ya sa Jehobah yake daraja ran ɗan Adam?
Yaya Jehobah yake ji sa’ad da wani ya kashe kansa ko ya kashe wani da gangan?
Me ya sa kake gode wa Jehobah don ran da ya ba ka?
KA BINCIKA
Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda za mu nuna godiya don ran da Jehobah ya ba mu?
Ku karanta talifin nan don ku ga amsar tambayar nan, Shin Allah zai gafarta wa macen da ta zub da ciki?
“Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Zub da Ciki?” (Talifin jw.org)
Ku karanta talifin nan don ku ga yadda bin ra’ayin Allah zai iya taimaka mana mu zaɓi nishaɗin da ba zai jefa ranmu cikin haɗari ba.
“Zai Dace Ka Yi ‘Wasanni Masu Haɗari Sosai?’” (Awake!, 8 ga Oktoba, 2000)
Idan mutum yana tunanin kashe kansa fa? Ku karanta talifin nan don ku ga yadda Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka masa.
a Jehobah ya damu da waɗanda suka yi sanyin gwiwa. (Zabura 34:18) Ya fahimci abin da ke sa mutane su yi tunanin kashe kansu kuma yana so ya taimaka musu. Don ka ga yadda Jehobah zai taimaka wa mutum ya daina tunanin kashe kansa, ka karanta talifin nan “Ina So In Mutu—Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka Min Idan Ina Tunanin Kashe Kaina?” a sashen Ka Bincika a darasin nan.
b Bai kamata waɗanda suka taɓa zub da ciki kuma suka tuba da gaske su damu ainun ba, don Jehobah zai iya gafarta musu. Don ƙarin bayani, ka duba talifin nan “Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Zub da Ciki?” a sashen Ka Bincika na wannan darasin.