DARASI NA 36
Ku Kasance Masu Gaskiya Cikin Dukan Abu
Kowa yana son abokai masu faɗin gaskiya. Jehobah ma yana so abokansa su riƙa faɗin gaskiya. Amma yin hakan ba shi da sauƙi a duniyar da mutane da yawa suke son yin rashin gaskiya. Ta yaya za mu amfana idan muna faɗin gaskiya a duk abin da muke yi?
1. Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa faɗin gaskiya?
Idan muna faɗin gaskiya, hakan zai nuna cewa muna ƙaunar Jehobah kuma muna daraja shi. Gaskiyar ita ce, Jehobah ya san dukan tunaninmu da ayyukanmu. (Ibraniyawa 4:13) Yana ganin lokacin da muke faɗin gaskiya kuma hakan yana sa shi farin ciki. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yahweh yana ƙyamar mai halin ruɗu, amma yana amincewa da mai gaskiya a zuci.”—Karin Magana 3:32.
2. Ta yaya za mu riƙa faɗin gaskiya a kullum?
Jehobah yana so mu ‘dinga faɗa wa maƙwabtanmu gaskiya.’ (Zakariya 8:16, 17) Mene ne hakan yake nufi? Idan muna magana da iyalinmu ko abokan aikinmu, ko ’yan’uwanmu Kiristoci ko ma’aikatan gwamnati, bai kamata mu yi musu ƙarya ko mu ruɗe su ba. Masu faɗin gaskiya ba sa sata ko su damfari mutane. (Karanta Karin Magana 24:28 da Afisawa 4:28.) Kuma suna biyan haraji. (Romawa 13:5-7) Ta yin waɗannan abubuwan, muna “aikata abin da yake daidai cikin ayyukanmu duka.”—Ibraniyawa 13:18.
3. Mene ne amfanin faɗin gaskiya?
Idan an san cewa mu masu faɗin gaskiya ne, mutane za su yarda da mu. Hakan zai sa kowa ya kasance da kwanciyar hankali a ikilisiya, kamar iyalin da suke ƙaunar juna. Kuma zuciyarmu ba za ta riƙa damun mu ba. Faɗin gaskiya zai sa mutane su riƙa ‘daraja koyarwar nan da take game da Allah Mai Cetonmu,’ kuma zai sa su so bauta masa.—Titus 2:10.
KA YI BINCIKE SOSAI
Za mu ga amfanin faɗin gaskiya da yadda zai sa Jehobah farin ciki. Kuma za mu koyi yadda za mu riƙa faɗin gaskiya a kowane yanayi.
4. Faɗin gaskiya na faranta ran Jehobah
Ku karanta Zabura 44:21 da Malakai 3:16, sai ku tattauna tambayoyin nan:
- Me ya sa kake gani ba za mu iya ɓoye wa Jehobah kome ba? 
- Yaya kake ganin Jehobah yake ji sa’ad da muka faɗi gaskiya, ko a lokacin da yin hakan ya yi mana wuya? 
Yara suna faranta ran iyayensu sa’ad da suka faɗi gaskiya. Hakazalika, muna faranta ran Jehobah sa’ad da muka faɗi gaskiya
5. Ka riƙa faɗin gaskiya a kowane lokaci
Mutane da yawa suna ganin cewa ba za mu iya faɗin gaskiya a kowane lokaci ba. Amma ka ga dalilin da ya sa ya kamata mu riƙa faɗin gaskiya a kullum. Ku kalli BIDIYON nan.
Ku karanta Ibraniyawa 13:18, sai ku tattauna yadda za mu riƙa faɗin gaskiya a . . .
- iyali. 
- wurin aiki ko makaranta. 
- yanayi dabam-dabam. 
6. Faɗin gaskiya yana amfanar mu
Mutum zai iya shiga matsala idan ya faɗi gaskiya. Amma abin da ya kamata mu riƙa yi kowane lokaci ke nan. Ku karanta Zabura 34:12-16, sai ku tattauna tambayar nan:
- Ta yaya faɗin gaskiya zai inganta rayuwarka? 
- Mata da miji da suke gaya wa juna gaskiya suna ƙarfafa aurensu 
- Masu faɗin gaskiya a wurin aiki suna samun amincewar shugabanninsu 
- Ma’aikatan gwamnati suna daraja masu faɗin gaskiya 
WASU SUN CE: “Ba laifi ba ne ka ɗan yi ƙarya muddin ba ka ɓata sunan wani ba.”
- Me ya sa ka gaskata cewa Jehobah ya tsani kowane irin ƙarya? 
TAƘAITAWA
Jehobah yana so aminansa su riƙa faɗin gaskiya a koyaushe.
Bita
- Ta yaya za mu riƙa faɗin gaskiya? 
- Me ya sa kake ganin ba za mu iya ɓoye wa Jehobah kome ba? 
- Me ya sa kake so ka riƙa faɗin gaskiya a kowane lokaci? 
KA BINCIKA
Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda iyaye za su riƙa koya wa yaransu su riƙa faɗin gaskiya.
Ku kalli bidiyon nan don ku ga amfanin cika alkawari.
Ku karanta talifin nan don ku ga ko wajibi ne mu biya haraji ko da ba a amfani da kuɗin a hanyar da ta dace.
“Biyan Haraji Dole Ne?” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Satumba, 2011)
Ku karanta talifin nan don ku ga yadda wani ɗan damfara ya canja salon rayuwarsa.
“Na Koyi Cewa Jehobah Mai Jinƙai Ne da Kuma Gafartawa” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Yuli, 2015)