DARASI NA 56
Ku Kasance da Haɗin Kai a Ikilisiya
Sa’ad da muke tsakanin ’yan’uwa, mukan ji yadda Sarki Dauda ya ji, da ya ce: “Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma ’yan’uwa su zauna tare!” (Zabura 133:1) Haɗin kai ba ya faruwa haka kawai. Wajibi ne kowannenmu ya yi iya ƙoƙarinsa don a kasance da haɗin kai.
1. Me aka san bayin Allah da shi?
Idan ka halarci taro a wata ƙasa, wataƙila ba za ka fahimci yaren da ake yi ba, amma ba mamaki za ka saki jiki. Me ya sa? Domin muna nazarin Littafi Mai Tsarki da littattafai iri ɗaya a ko’ina kuma muna nuna wa juna ƙauna. A duk inda muke, dukanmu muna “kira ga Sunan Yahweh” kuma muna bauta masa da haɗin kai.—Zafaniya 3:9.
2. Mene ne za ka iya yi don ka sa ’yan’uwa su kasance da haɗin kai?
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku ci gaba da ƙaunar juna da zuciya ɗaya.” (1 Bitrus 1:22) Ta yaya za ka iya bin shawarar nan? Maimakon mu riƙa mai da hankali ga kasawar mutane, mu mai da hankali ga halayensu masu kyau. Kada ka riƙa yin tarayya kaɗai da waɗanda suke son abin da kake so, amma ka yi ƙoƙari ka riƙa tarayya da ’yan’uwa da suka fito daga wasu wurare. Ban da haka, ya kamata mu yi ƙoƙari mu daina nuna wariya idan muna yin hakan.—Karanta 1 Bitrus 2:17.a
3. Mene ne za ka yi idan ka sami saɓani da wani ɗan’uwa?
Ko da yake muna da haɗin kai, mu ajizai ne. A wasu lokuta mukan ɓata wa juna rai. Kalmar Allah ta ce: “Ku yi ta . . . gafarta wa juna,” ya kama daɗa da cewa: “Kamar yadda Jehobah yake gafarta muku zunubanku, wajibi ne ku ma ku gafarta wa juna.” (Karanta Kolosiyawa 3:13.) Sau da yawa, muna ɓata wa Jehobah rai kuma yana gafarta mana. Saboda haka, yana so mu gafarta wa ’yan’uwanmu. Idan ka ga cewa ka ɓata wa wani rai, ka yi ƙoƙari ka je ku sasanta.—Karanta Matiyu 5:23, 24.b
KA YI BINCIKE SOSAI
Za mu ga hanyoyin da za mu sa ’yan’uwa a ikilisiya su kasance da haɗin kai kuma su yi zaman lafiya.
Mene ne za ka yi don ka sasanta da ɗan’uwanka?
4. OKa guji nuna bambanci
Ya kamata mu ƙaunaci dukan ’yan’uwanmu. Amma yana iya yi mana wuya mu amince da wani da muke gani ya yi dabam da mu. Mene ne zai iya taimaka mana? Ku karanta Ayyukan Manzanni 10:34, 35, sai ku tattauna tambayoyin nan:
Jehobah yana amincewa da mutanen da suka fito daga wurare dabam-dabam su zama Shaidunsa. Ta yaya za ka iya yin koyi da shi ta yadda kake ɗaukan mutane da suka yi dabam da kai?
Wane irin bambanci ne ake nunawa a yankinku da za ka so ka guji yi?
Ku karanta 2 Korintiyawa 6:11-13, sai ku tattauna tambayar nan:
Ta yaya za ka koyi yadda za ka riƙa ƙaunar dukan ’yan’uwa sosai?
5. Ku riƙa gafartawa kuma ku sasanta matsaloli
Jehobah yana gafarta mana laifofinmu duk da cewa ba zai taɓa bukaci mu gafarta masa ba. Ku karanta Zabura 86:5, sai ku tattauna tambayoyin nan:
Mene ne wannan ayar ta nuna game da Jehobah?
Me ya sa kake son yadda yake gafarta mana?
Waɗanne yanayoyi ne za su iya sa ya yi mana wuya mu zauna lafiya da mutane?
Ta yaya za mu iya yin koyi da Jehobah kuma mu kasance da haɗin kai da ’yan’uwanmu? Ku karanta Karin Magana 19:11, sai ku tattauna tambayar nan:
Idan wani ya ɓata maka rai, mene ne za ka iya yi don kada yanayin ya daɗa taɓarɓarewa?
A wasu lokuta mukan ɓata wa wasu rai, mene ne za mu iya yi idan hakan ya faru? Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.
A bidiyon, mene ne ’yar’uwar ta yi don ta sasanta matsalar da ke tsakaninta da wata?
6. Ka riƙa mai da hankali ga halaye masu kyau na ’yan’uwa
Idan muka kusaci ’yan’uwanmu, za mu san halayensu masu kyau da kuma kasawarsu. Ta yaya za mu mai da hankali ga halayensu masu kyau? Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.
Mene ne zai taimaka maka ka ga halaye masu kyau na ’yan’uwa?
Jehobah yana mai da hankali ga halayenmu masu kyau. Ku karanta 2 Tarihi 16:9a, sai ku tattauna tambayar nan:
Yaya kake ji don yadda Jehobah yake mai da hankali ga halayenka masu kyau?
Ko da zoɓe mai tsada yana da ɗan matsala, yana da daraja har ila. Hakazalika, ko da yake dukan ’yan’uwa ajizai ne, suna da daraja a gaban Jehobah
WASU SUN CE: “Idan na yi saurin gafarta wa mutum, ba zai san cewa ya ɓata mini rai sosai ba.”
Me ya sa ya kamata mu yi saurin gafarta wa mutane?
TAƘAITAWA
Za ka iya sa ’yan’uwa a ikilisiya su kasance da haɗin kai ta wurin gafartawa da kuma nuna musu cewa kana ƙaunar su.
Bita
Ta yaya za ka guji nuna bambanci?
Mene ne za ka yi idan ka sami saɓani da wani ɗan’uwa?
Me ya sa za ka so ka yi koyi da yadda Jehobah yake gafarta wa mutane?
KA BINCIKA
Ku kalli bidiyon nan don ku ga wani misali da Yesu ya bayar da zai taimaka mana mu guji shari’anta mutane.
Ku karanta talifin don ku ga ko muna bukatar mu nemi gafara ko da muna ganin ba mu da laifi.
“Neman Gafara—Hanya Ce Mai Kyau na Samun Salama” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Nuwamba, 2002)
Ka ga yadda wasu suka koyi yin sha’ani da mutane ba tare da nuna bambanci ba.
Ku karanta talifin nan don ku san yadda za ku sasanta da wani kafin ya jawo matsala a ikilisiya.
“Ku Sasanta Matsalolinku Cikin Ƙauna” (Hasumiyar Tsaro, Mayu 2016)
a A Ƙarin Bayani na 6 za mu ga yadda ƙauna ta sa Kiristoci suka guji yaɗa cuta.
b A Ƙarin Bayani na 7 za a tattauna yadda za a magance matsaloli da suka shafi kasuwanci da kuma dokokin gwamnati.