Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 5/1 p. 14
  • ‘Wace Doka Ce ta Fi Muhimmanci?’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Wace Doka Ce ta Fi Muhimmanci?’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Ƙaunaci Allah Da Yake Ƙaunarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Abin Da Ake Nufi Da Mu Ƙaunaci Makwabcinmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • “Wajibi Ne Ka Ƙaunaci Jehobah Allahnka”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ka ‘Ƙaunaci Maƙwabcinka Kamar Ranka’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 5/1 p. 14

KA KUSACI ALLAH

‘Wace Doka Ce ta Fi Muhimmanci?’

Mene ne Allah yake bukata a gare mu? Shin Allah ya ba da dokoki ne birjik da sai lallai mun bi? A’a, kuma hakan abin farin ciki ne. Bisa ga abin da Ɗan Allah, Yesu Kristi ya faɗi, za mu iya bayyana abin da Allah yake bukata a gare mu da kalma guda.—Ka karanta Markus 12:28-31.

Ka yi la’akari da abin da ke faruwa sa’ad da Yesu ya yi wannan magana. Yana koyarwa ne a cikin haikali a ranar 11 ga Nisan, ’yan kwanaki kafin mutuwarsa. Magabtansa sun sha yi masa irin tambayoyin da za su sa a kama shi da laifi. A duk lokacin da suka yi masa irin waɗannan tambayoyi, sai ya ba su amsoshi da suka dace da su. Sai daga baya, suka tambaye shi: ‘Wace doka ce ta fi muhimmanci?’—Aya ta 28.

Amsar wannan tambayar ba ta da sauƙi. Me ya sa? Wasu Yahudawa suna da’awa cewa cikin dokoki sama da 600 da aka bayar ta hannun Musa, akwai wadda ta fi sauran muhimmanci. Wasu kuma sun ce bai dace a ɗauki wasu dokoki da muhimmanci fiye da wasu ba. Yaya Yesu zai amsa wannan tambayar?

Sa’ad da Yesu yake ba su amsa, ya ambaci dokoki guda biyu, ba ɗaya ba. Da farko, ya ce: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka, da dukan ƙarfinka.” (Aya ta 30; Kubawar Shari’a 6:5) A wasu lokatai, waɗannan kalmomin ‘zuciya’ da ‘rai’ da ‘azanci’ da kuma ‘ƙarfi’ suna nufin abu ɗaya.a Abin da ƙaunar Jehobah yake nufi shi ne mutum ya ƙaunaci Allah da dukan tunaninsa da kuma abubuwan da yake da shi. Wani littafin bincike na Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya kamata mu ƙaunaci Allah da kome da muke da shi kuma da zuciya ɗaya.” Saboda haka, idan kana ƙaunar Allah, kowace rana za ka riƙa iyakacin ƙoƙarinka don ka yi abin da zai faranta masa rai.—1 Yohanna 5:3.

Na biyu, Yesu ya ce: “Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.” (Aya ta 31; Levitikus 19:18) Akwai alaƙa sosai tsakanin ƙaunar Allah da ƙaunar maƙwabcinmu. Muna ƙaunar maƙwabtanmu domin muna ƙaunar Allah. (1 Yohanna 4:20, 21) Idan muka ƙaunaci maƙwabtanmu kamar yadda muke ƙaunar kanmu, za mu bi da su kamar yadda muke son su bi da mu. (Matta 7:12) Ta hakan, za mu nuna cewa muna ƙaunar Allah, wanda ya halicce mu duka cikin surarsa.—Farawa 1:26.

Shin yin ƙaunar Allah da maƙwabcinmu tana da muhimmanci sosai kuwa? Yesu ya ce: “Babu wata doka wadda ta fi waɗannan girma.” (Aya ta 31) A Linjilar Matta, Yesu ya bayyana cewa dukan sauran dokoki sun dangana bisa waɗannan dokoki biyu ne.—Matta 22:40.

Bai da wuya a faranta wa Allah rai. Za mu kwatanta dukan abubuwan da yake bukata daga gare mu da kalma guda, wato, ƙauna. Allah yana bukatar masu bauta masa su riƙa ƙaunarsa, kuma zai bukace mu mu ci gaba da yin hakan. Amma ƙauna ba maganar baki ko kuma yadda mutum yake ji kawai ba; muna nuna ƙauna ta yadda muke yin abubuwa. (1 Yohanna 3:18) Babu shakka, za ka so ka koyi yadda za ka ƙaunaci Jehobah, Allah wanda shi ne ‘ƙauna,’ ko ba haka ba?—1 Yohanna 4:8.

Karatun Littafi Mai Tsarki na Mayu

Luka 22–Yohanna 16

a A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan ‘rai’ tana nufin mutum ne gaba ɗaya. Saboda haka ‘rai’ ya ƙunshi ‘zuciya’ da ‘azanci’ da kuma ‘ƙarfi.’

Za mu kwatanta dukan abubuwan da Jehobah yake bukata daga masu bauta masa da kalma guda, wato, ƙauna

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba