ABIN DA KE SHAFIN FARKO | WANE SAƘO NE KE LITTAFI MAI TSARKI?
Allah Ya Shirya Yadda Zai Ceci ’Yan Adam
Allah ya yi wa Ibrahim mai aminci alkawari cewa ‘zuriyar’ da aka yi annabci a kanta za ta fito daga wurinsa ne. Kuma ta wurin wannan zuriyar ‘dukan al’ummai’ za su sami albarka. (Farawa 22:18) Daga baya, Yakubu jikan Ibrahim ya ƙaura zuwa ƙasar Masar kuma a nan ne iyalinsa suka yalwata har suka zama al’ummar Isra’ila ta dā.
A kwana a tashi aka yi wani azzalumin Fir’auna da ya mai da Isra’ilawan bayi. Hakan ya sa Allah ya aika da annabi Musa wanda ya fitar da su daga wannan ƙasar kuma ya raba Jar Teku ta mu’ujiza don su bi cikinta. Daga baya Allah ya ba al’ummar Isra’ila Dokoki Goma da kuma wasu dokoki don su yi musu ja-gora da kuma kāriya. Waɗannan dokokin sun bayyana irin hadayu da za su riƙa yi don a gafarta musu zunubansu. Allah ya hure Musa ya gaya musu cewa zai aika musu da wani annabi. Wannan annabin ne zai zama ‘zuriyar’ da aka yi alkawarinta.
Bayan shekaru fiye da ɗari huɗu, Allah ya yi wa Sarki Dauda alkawari cewa wannan ‘zuriyar’ da aka yi alkawarinta a cikin gonar Adnin za ta yi sarautar Mulkin da zai dawwama har abada. Zuriyar nan ne ta zama Almasihu, wato Mai ceto da Allah ya zaɓa don ya ceci ’yan Adam kuma ya sake mai da duniya Aljanna.
Da sannu-sannu Allah ya ci gaba da bayyana abubuwa game da Almasihun ta bakin Dauda da kuma wasu annabawa. Sun annabta cewa Almasihun zai zama mai tawali’u da alheri kuma sarautarsa za ta sa yunwa da rashin adalci da kuma yaƙi su zama labari. ’Yan Adam baki ɗaya za su yi zaman lafiya da juna da kuma dabbobi. Ciwo da wahala da mutuwa ma duk za su zama labari, da yake tun dā can ba nufin Allah ba ne. Za a kuma ta da matattu don su ci gaba da rayuwa a duniya.
Ta bakin annabi Mikah, Allah ya annabta cewa za a haifi Almasihun a garin Bai’talami. Annabi Daniyel kuma ya annabta cewa za a kashe shi, amma Allah zai ta da shi kuma ya naɗa shi Sarki a sama. Ƙari ga haka, Daniyel ya ga wata ru’ya cewa Mulkin Almasihun zai sauya duk sauran mulkoki. Shin Almasihun ya bayyana kamar yadda aka annabta kuwa?
—Bisa ga abin da ke littafin Farawa surori 22-50, Fitowa, Kubawar Shari’a, 2 Sama’ila, Zabura, Ishaya, Daniyel, Mikah, Zakariya 9:9.