ABIN DA KE SHAFIN FARKO | WANE SAƘO NE KE LITTAFI MAI TSARKI?
Albishiri ga Dukan Mutane
Tashiwar Yesu daga matattu ta sa almajiransa suka kasance da tabbaci da kuma ƙwazo. Manzo Bulus musamman ma ya bi ƙasashe da ke Asiya Ƙarama da Bahar Rum don ya kafa ikilisiyoyi kuma ya ƙarfafa Kiristoci su yi tsayin daka sa’ad da ake matsa musu su taka dokar Allah da kuma sa’ad da ake tsananta musu. Duk da waɗannan matsalolin, mutane da yawa sun zama Kiristoci.
Daga baya an jefa Bulus cikin fursuna. Duk da haka, ya rubuta wasiƙu zuwa ga ikilisiyoyi don ya ƙarfafa da kuma gargaɗar da su. Ya yi musu gargaɗi a kan wata babbar matsala da za su fuskanta, wato, ridda. Ruhu mai tsarki ya nuna wa Bulus yadda “kerketai masu-zafin hali” da suke faɗin “karkatattun zantattuka” za su shigo cikinsu domin “su janye masu-bi.”—Ayyukan Manzanni 20:29, 30.
Wannan ridda ta soma kafin ƙarshen ƙarni na farko. A wannan lokacin ne Yesu ya saukar wa manzo Yohanna da wahayin abin da zai faru a nan gaba. Kamar yadda Yohanna ya rubuta, ’yan hamayya da kuma malaman ƙarya ba za su iya hana Allah cika asalin nufinsa ga duniya da kuma ’yan Adam ba. Kowace “ƙabila da harshe da al’umma” za ta ji bisharar Mulkin Allah. (Ru’ya ta Yohanna 14:6) Duniya za ta zama Aljanna kuma duk wanda ya yi nufin Allah zai iya more rayuwa a lokacin!
Shin hakan albishiri ne a gare ka? Idan amsarka e ce, to ka ƙara koya game da saƙon da Allah ya aika wa mutane a cikin Littafi Mai Tsarki, kuma ka koyi yadda wannan saƙon zai amfane ka yanzu da kuma nan gaba.
Za ka iya karanta Littafi Mai Tsarki a cikin harsuna wajen 50 a dandalin www.pr418.com. Ƙari ga haka, za ka iya karanta ƙasidun nan Littafi Mai Tsarki—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa? da Albishiri Daga Allah! da kuma littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da dai wasu littattafai a wannan dandalin. Dukansu suna tattauna dalilin da ya sa za mu iya amince da Littafi Mai Tsarki da kuma yadda mu da iyalinmu za mu iya bin shawarar da ke cikinsa. Ko kuma ka nemi ƙarin bayani daga duk Mashaidin Jehobah da ka gani.
—Bisa ga abin da ke littafin Ayyukan Manzanni, Afisawa, Filibiyawa, Kolosiyawa, Filimon, 1 Yohanna, Ru’ya ta Yohanna.