Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 11/1 p. 11
  • “Ubangiji Ya Gafarta Muku”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ubangiji Ya Gafarta Muku”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Rika Gafartawa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ka Riƙa Gafarta Wa Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ka Daraja Amincin Jehobah da Gafartawarsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Allah “Mai Yin Gafara”
    Ka Kusaci Jehobah
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 11/1 p. 11

KA KUSACI ALLAH

“Ubangiji Ya Gafarta Muku”

“Wanda ya ƙi gafarta wa wani yau zai yi da-na-sani gobe.” Abin da wani ɗan tarihi mai suna Edward Herbert ya faɗa ke nan wajen shekaru 400 da suka wuce. Kalaminsa ya nuna ɗaya cikin dalilan da ya sa muke bukata mu riƙa gafartawa, domin nan ba da daɗewa ba mu ma za mu bukaci a gafarta mana. (Matta 7:12) Amma, akwai babban dalilin da ya sa ya kamata mu riƙa gafartawa. Ka lura da abin da manzo Bulus ya faɗa a littafin Kolosiyawa 3:13.—Karanta.

Tun da yake dukanmu ajizai ne, za mu iya ɓata wa mutane rai kuma su ma za su iya yi mana hakan a wasu lokatai. (Romawa 3:23) Mene ne za mu yi don mu ci gaba da zaman lafiya da mutane? Allah ya hure Bulus ya umurce mu mu riƙa gafarta wa juna kuma mu yi zaman haƙuri da juna. Ko da yake an rubuta wannan umurnin kusan shekaru dubu biyu da suka shige, yana da amfani har ila. Bari mu bincika abin da Bulus ya faɗa da kyau.

Ku riƙa “haƙuri da juna.” Wata majiya ta ce Kiristoci suna nuna wannan halin ta wajen kasancewa a shirye su jure da mutanen da halayensu ke ɓata musu rai. Furucin nan “da juna” yana nuna cewa kowannenmu yana bukata ya riƙa haƙuri da ɗan’uwansa. Wato, idan muka tuna cewa mu ma wasu halayenmu za su iya ɓata wa mutane rai, ba za mu bar halayensu da ba ma so su hana mu zaman lafiya da su ba. Amma idan suka yi mana laifi fa?

Ku riƙa “gafarta ma juna.” Wani manazarci ya ce kalmar Helenanci da aka yi amfani da ita a nan tana nufin gafartawa daga zuci kuma a yalwace. Wani bincike kuma ya nuna cewa wannan kalmar tana iya nufin a yi wa mutum jin ƙai ko alheri ko kuma rangwame. Muna nuna cewa mu masu alheri ne ta wajen gafarta wa mutane ko da muna da dalilin yin “ƙara game da” su, wato idan suka yi mana laifi. Amma, me ya sa ya kamata mu kasance a shirye don mu nuna musu alheri? Domin mu ma jim kaɗan za mu bukace su su yi mana alheri ta wajen gafarta mana.

“Kamar yadda Ubangiji ya gafarta muku, hakanan kuma sai ku yi.” Wannan ne dalili mafi muhimmanci da ya kamata mu riƙa gafartawa, wato, domin Jehobah yana gafarta mana. (Mikah 7:18) Ka yi tunanin alherin da Jehobah yake nuna wa masu zunubi da suka tuba. Jehobah ba kamar mu da muke yin zunubi ba ne. Duk da haka, yana shirye ya gafarta wa masu zunubi da suka tuba ko da yake ya san ba zai bukaci su gafarta masa ba. Hakika, Jehobah ne ya kafa mana misali mafi kyau na gafartawa!

Hakika, Jehobah ne ya kafa mana misali mafi kyau na gafartawa!

Jin ƙai da Jehobah yake nuna mana yana sa mu kusace shi kuma mu bi misalinsa. (Afisawa 4:32–5:1) Saboda haka, ya dace mu tambayi kanmu, ‘Tun da yake Jehobah yana gafarta mini, me zai hana in gafarta ma wanda ajizi ne kamar ni da ya yi mini laifi amma ya nuna cewa ya tuba?’—Luka 17:3, 4.

Karatun Littafi Mai Tsarki na watan Disamba

1 Bitrus 1-5; 2 Bitrus 1-3; 1 Yohanna 1-5; 2 Yohanna 1-13; 3 Yohanna 1-14; Yahuda 1-25–Ru’ya ta Yohanna 1-22

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba