Zaɓin da Na Yi Sa’ad da Nake Yaro
A shekara ta 1985 sa’ad da nake ɗan shekara goma, wasu yara daga ƙasar Kambodiya sun soma zuwa makarantarmu a birnin Columbus, Ohio, Amirka. Ɗaya cikin yaran ya ɗan iya Turanci. Ta wajen nuna mini hotuna, sai ya gaya mini labarai masu ban tsoro, da azabtar da mutane da kashe-kashe da kuma tserewa daga gidan yari. Ina yawan kuka daddare sa’ad da nake tunani game da waɗannan yaran. Na yi marmarin tattauna da su game da begen yin rayuwa cikin Aljanna da kuma tashin matattu, amma ba sa jin Turanci. Ko da yake ni ƙaramin yaro ne a lokacin, amma sai na soma koyon yaren Kambodiya don na sami damar yi wa ’yan ajinmu wa’azi game da Jehobah. Ban san cewa wannan zaɓin da na yi zai shafe ni sosai a nan gaba ba.
Koyon yaren Kambodiya ba shi da sauƙi.. Na tuna sau biyu da na kusan karaya, amma Jehobah ya sa iyayena suka ƙarfafa ni. Da sannu-sannu, sai malamaina da kuma abokan makaranta suka soma ƙarfafa ni cewa in biɗi sana’a mai kyau sosai. Amma, abin da nake so shi ne yin hidimar majagaba. A sakamako, sai na zaɓi wasu kwas a makarantar sakandare da za su taimaka mini in sami aiki na ɗan lokaci don in cim ma burina. Bayan mun tashi daga makaranta, ina yawan zuwa wajen wasu majagaba don mu fita wa’azi tare. Na kuma soma koya wa wasu ɗalibai Turanci kuma na amfana sosai daga yin hakan.
Sa’ad da nake ɗan shekara 16, na ji cewa akwai wani rukunin Kambodiya a birnin Long Beach, jihar Kalifoniya, Amirka. Na je wurin kuma na koyi yadda ake karatu a yaren Kambodiya. Da zarar na sauƙe karatu, sai na soma hidimar majagaba kuma na ci gaba da yi wa ’yan Kambodiya da ke kusa da gidanmu wa’azi. Sa’ad da na kai ɗan shekara 18, sai na soma la’akarin ƙaura zuwa ƙasar Kambodiya. A lokacin, ana tarzoma a Kambodiya, amma na san cewa ƙalilan ne kawai cikin mutane miliyan goma da suke zama a ƙasar ne aka taɓa wa wa’azin bishara. Kuma akwai ikilisiya ɗaya da masu shela sha uku kawai a ƙasar baki ɗaya. Lokaci na farko da na je Kambodiya shi ne sa’ad da nake ɗan shekara 19. Bayan shekara biyu, sai na ƙaura zuwa ƙasar kuma na soma aikin fassara da kuma koyar da Turanci don in tallafa wa wa’azin da nake yi. Daga baya sai na auri mace wadda muke da maƙasudi ɗaya. Mun ji daɗin taimaka wa mutanen Kambodiya da yawa su zama Shaidun Jehobah.
Jehobah ya ‘biya muradin zuciyata.’ (Zab. 37:4) Babu abin da ke sa mu farin ciki kamar yin wa’azi. A shekara sha shida da na yi a ƙasar Kambodiya, wannan ƙaramar ikilisiya da ke da masu shela 13 ta haifar da ikilisiyoyi 12 da ƙananan rukunoni huɗu.—Jason Blackwell ne ya ba da labarin.