Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp16 Na 4 p. 8
  • Me Ya Sa Aka Kasa Halaka Littafi Mai Tsarki?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ya Sa Aka Kasa Halaka Littafi Mai Tsarki?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Makamantan Littattafai
  • Littafi Mai Tsarki Sako Ne Daga Allah
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Labari Mai Muhimmanci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Mene Ne Ra’ayinka Game Da Littafi Mai Tsarki?
    Mene Ne Ra’ayinka Game Da Littafi Mai Tsarki?
  • Ta Yaya Littafi Mai Tsarki Zai Inganta Rayuwata?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
wp16 Na 4 p. 8
Wani mutum yana karanta Littafi Mai Tsarki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | YADDA AKA KĀRE LITTAFI MAI TSARKI

Me Ya Sa Aka Kasa Halaka Littafi Mai Tsarki?

Ba a iya halaka Littafi Mai Tsarki ba, shi ya sa za mu iya samun namu kofin a yau. Kuma idan ka zaɓi juyin Littafi Mai Tsarki mai kyau, babu shakka, za ka ga cewa abin da kake karantawa ya yi daidai da wanda aka fara wallafawa.a Amma me ya sa Littafi Mai Tsarki ya tsira duk da cewa an rubuta shi a kan abubuwan da za su iya lalacewa kuma ʼyan hamayya sun yi ƙoƙarin halaka shi da kuma canja saƙon da ke cikinsa? Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya fi sauran littattafai?

“Yanzu na yarda cewa Littafi Mai Tsarki da nake da shi kyauta ce daga Allah”

Ra’ayin ɗaliban Littafi Mai Tsarki da yawa ya yi daidai da na manzo Bulus wanda ya ce: “Kowane Nassi hurarre na Allah ne.” (2 Timotawus 3:16, Littafi Mai Tsarki) Sun gaskata cewa Littafi Mai Tsarki ya tsira don Kalmar Allah ce kuma don Allah ne da kansa ya kāre shi har wa yau. Faizal da aka ambata a farkon wannan mujallar ya tsai da shawarar bincika Littafi Mai Tsarki da kansa don ya ga ko Kalmar Allah ce da gaske. Abin da ya gano daga binciken ya ba shi mamaki sosai. Ya fahimci cewa abubuwa da dama da ake koyarwa a coci ba sa cikin Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, ya yi farin cikin koyon dalilin da ya sa Allah ya halicci mutane.

Ya ce: “Yanzu na yarda cewa Littafi Mai Tsarki da nake da shi kyauta ce daga Allah. Tun da Allah yana da ikon halittar sama da ƙasa, ai ba zai yi masa wuya ya ba mu littafi kuma ya kāre shi ba. Idan muka ce ba zai iya yin haka ba, muna raina ikon da Allah Maɗaukaki yake da shi ke nan! Kuma waye ne ni da zan raina ikon Allah?”—Ishaya 40:8.

a Ka duba talifin nan “How Can You Choose a Good Bible Translation?” a cikin Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Mayu, 2008 na Turanci.

Ta yaya za mu tabbatar da cewa sakon da ke cikin Littafi Mai Tsarki gaskiya ne?

Jerin talifofin nan sun nuna yadda Allah ya kāre Litafi Mai Tsarki. Amma ta yaya za ka tabbatar da cewa Littafi Mai Tsarki “maganar Allah” ce, ba tatsuniya ko ƙage ba? (1 Tasalonikawa 2:13) Ka kalli gajeren bidiyon nan Ta Yaya Za Mu San Cewa Abin da Ke Littafi Mai Tsarki Gaskiya Ne? Za a sami bidiyon a ƙarƙashin darasi na 3 na ƙasidar nan Albishiri Daga Allah! a dandalin www.pr418.com/ha. (Ka duba LITTATTAFAI > LITTATTAFAI DA ƘASIDU)

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba