Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp16 Na 4 pp. 14-15
  • Bincike Mafi Muhimmanci da Kake Bukatar Ka Yi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bincike Mafi Muhimmanci da Kake Bukatar Ka Yi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA GWADA ABIN DA KA YI IMANI DA SHI DA LITTAFI MAI TSARKI
  • Menene Mulkin Allah?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Mene ne Mulkin Allah?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Wanene Yesu Kristi?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Kiristoci Suna Bauta Cikin Ruhu Da Gaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
wp16 Na 4 pp. 14-15

Bincike Mafi Muhimmanci Da Kake Bukatar Ka Yi

KANA ɗaukan kanka a matsayin Kirista kuwa? Idan haka ne, kana ɗaya daga cikin mutane fiye da biliyoyi biyu a faɗin duniya da ke da’awa cewa su Kiristoci ne. Muna da dubban ɗariku da suke da’awa cewa su Kiristoci ne amma koyarwarsu da ra’ayinsu ba ɗaya ba ne. Kuma wataƙila abubuwan da ka yi imani da su sun bambanta da na wasu Kiristoci. Shin abin da ka yi imani da shi yana da wani muhimmanci ne? Hakika yana da muhimmanci idan kana son ka yi abin da Littafi Mai Tsarki ya ce Kiristoci su riƙa yi.

An san mabiyan Yesu na ƙarni na farko da sunan nan “Kirista.” (Ayyukan Manzanni 11:26) Ba a kira su da wasu sunaye ba don imaninsu ɗaya ne a lokacin. Kiristocin sun bi koyarwa da kuma umurnin wanda ya kafa Kiristanci, wato Yesu Kristi. Kana gani cocinku yana koyar da abin Kristi ya ce da kuma abin da Kiristoci na farko suka yi imani da shi? Ta yaya za ka tabbatar da hakan? Littafi Mai Tsarki ne kaɗai zai iya taimaka mana mu san gaskiyar.

Ka yi la’akari da wannan: Yesu Kristi ya daraja Littafi Mai Tsarki kuma ya ɗauke shi a matsayin Kalmar Allah. Bai amince da waɗanda suka yi watsi da koyarwar Littafi Mai Tsarki kuma suka mai da hankali ga koyarwar mutane ba. (Markus 7:9-13) Amma muna da tabbaci cewa mabiyan Yesu na gaske suna bin koyarwar Littafi Mai Tsarki. Don haka, ya kamata Kiristoci su tambayi kansu, ‘Abin da ake koyarwa a cocinmu ya yi daidai da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa kuwa?’ Idan kana son ka san amsar, zai dace ka gwada abin da cocinku yake koyarwa da kuma wanda Littafi Mai Tsarki yake koyarwa.

Yesu ya ce ya kamata mu riƙa bauta cikin gaskiya kuma wannan gaskiyar tana cikin Littafi Mai Tsarki. (Yohanna 4:24; 17:17) Kuma manzo Bulus ya ce idan muna so mu sami ceto, ya kamata mu ‘san gaskiya.’ (1 Timotawus 2:4) Don haka, yana da muhimmanci abin da muka yi imani da shi ya zama gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Me ya sa? Don idan ba mu yi hakan ba, ba za mu sami ceto ba!

KA GWADA ABIN DA KA YI IMANI DA SHI DA LITTAFI MAI TSARKI

Muna so ka karanta tambayoyi shida na gaba da kuma amsoshin da ke Littafi Mai Tsarki. Ka karanta ayoyin Littafi Mai Tsarki da ke wurin kuma ka yi tunani sosai a kan su. Bayan haka, sai ka tambayi kanka, ‘Ana koyar da Littafi Mai Tsarki a cocinmu kuwa?’

Wannan ɗan bincike da kuma tunanin da za ka yi za su taimaka maka sosai a bincike mai muhimmanci da kake bukatar yi. Za ka so ka bincika don ka tabbatar da cewa abin da ake koyarwa a cocinku ya jitu da Littafi Mai Tsarki kuwa?Shaidun Jehobah za su yi farin cikin taimaka maka ka bincika ainihin abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Zai dace ka gaya wa ɗaya daga cikinsu ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kai kyauta. Ko kuma ka shiga dandalinmu na jw.org/ha.

1 TAMBAYA: Wane ne Allah?

AMSA: Jehobah, Uban Yesu ne Maɗaukaki da kuma Mahaliccin kome.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE:

“Muna godiya ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kristi, kullayaumi muna yi maku addu’a.”—Kolosiyawa 1:3.

“Kai ne mai-isa ka karɓi ɗaukaka da daraja da iko, ya Ubangijinmu da Allahnmu: gama kai ka halicci dukan abu.”—Ru’ya ta Yohanna 4:11.

Ka kuma duba Romawa 10:13; 1 Timotawus 1:17.

2 TAMBAYA: Wane ne Yesu Kristi?

AMSA: Yesu shi ne Ɗan fari na Allah. Allah ne ya halicce shi, don haka, yana da mafari. Yesu yana wa Allah biyayya don Allah ya fi shi girma.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE:

“Uba ya fi ni girma.”—Yohanna 14:28.

‘[Yesu ne] surar Allah marar-ganuwa, ɗan fari ne gaban dukan halitta.ʼ—Kolosiyawa 1:15.

Ka kuma duba Matta 26:39; 1 Korintiyawa 15:28.

3 TAMBAYA: Mene ne ruhu mai tsarki?

AMSA: Ruhu mai tsarki iko ne da Allah yake amfani da shi don ya cim ma nufinsa. Ruhu mai tsarki ba mutum ba ne. Za a iya cika ko ƙarfafa mutane da ruhu mai tsarki.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE:

“Sa’anda Alisabatu ta ji gaisuwar Maryamu, jariri ya zabura a cikin cikinta. Alisabatu ta cika da ruhu mai-tsarki.”—Luka 1:41.

“Za ku karɓi iko lokacin da ruhu mai-tsarki ya zo bisanku.” —Ayyukan Manzanni 1:8.

Ka kuma duba Farawa 1:2; Ayyukan Manzanni 2:1-4; 10:38.

4 TAMBAYA: Mene ne Mulkin Allah??

AMSA: Mulkin Allah gwamnati ce da aka kafa a sama. Yesu ne Sarkin Mulkin Allah. Nan ba da daɗewa ba, Mulkin Allah zai sa a yi nufin Allah a dukan duniya.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE:

“Mala’ika na bakwai ya busa; daga bisani sai manyan muryoyi cikin sama, kuma suka ce, Mulkin duniya ya zama na Ubangijinmu, da na Kristinsa: zai yi mulki kuma har zuwa zamanun zamanai.”—Ru’ya ta Yohanna 11:15.

Ka kuma duba Daniyel 2:44; Matta 6:9, 10.

5 TAMBAYA: Shin dukan masu adalci ne za su je sama?

AMSA: A’a. Mutane ƙalilan masu adalci da aka kira “ƙaramin garke” da Allah ya zaɓa ne kawai za su je sama. Kuma za su yi sarauta tare da Yesu bisa ’yan Adam.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE:

“Ku ƙaramin garke, kada ku ji tsoro; gama Ubanku yana jin daɗi shi ba ku mulkin.”—Luka 12:32.

“Za su zama firistoci na Allah da na Kristi, za su yi mulki kuma tare da shi.”—Ru’ya ta Yohanna 20:6.

Ka kuma duba Ru’ya ta Yohanna 14:1, 3.

6 TAMBAYA: Me ya sa Allah ya halicci duniya da kuma mutane?

AMSA: A ƙarƙashin Mulkin Allah, duniya za ta zama aljanna kuma mutane masu aminci za su kasance da ƙoshin lafiya da salama kuma su yi rayuwa har abada.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE:

“Masu-tawali’u za su gāji ƙasan; za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.”—Zabura 37:10, 11.

“Zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.”—Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.

Ka kuma duba Zabura 37:29; 2 Bitrus 3:13.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba