Mummunan Sakamakon Yaƙi
Yaƙe-yaƙe suna jawo mummunan sakamako ga mutane. Sojoji da fararen hula da yaƙi ya shafa sun san mummunan sakamako da hakan yake jawowa.
SOJOJI
Gary daga ƙasar Birtaniya ya ce: “Za ka riƙa ganin ana kashe mutane ko kuma an ji musu raunuka masu muni. Hankalinka ba zai taɓa kwantawa ba.”
Wilmar daga ƙasar Kwalambiya ya ce: “An harbe ni da harsasai a baya da fuska. Na ga mutane da yawa da aka kashe, har da yara da kuma tsofaffi. Yaƙi yana sa ka daina damuwa idan mutane suna mutuwa da kuma shan wahala.”
Zafirah daga ƙasar Amurka ta ce: “Idan aka harbi mutum a gabanka, zai yi wuya ka manta da abin da ya faru. Za ka yi ta tunanin yadda mutumin yake ta kuka da ihu. Ba za ka taɓa manta da mutumin ba.”
FARAREN HULA
Oleksandra daga ƙasar Yukiren ta ce: “Na ji kamar ba zan taɓa sake yin farin ciki ba. Za ka riƙa jin tsoro cewa za a kashe ka, ko a kashe wani daga iyalinka, ko kuma a kashe wani abokinka.”
Daler daga ƙasar Tajikistan ya ce: “Muna jin tsoro sosai domin muna tsayawa a layi daga ƙarfe 2 na safe zuwa ƙarfe 11 na dare don karɓan abinci, kuma mun san cewa harsashi zai iya samun mu ba zato.”
Marie daga ƙasar Ruwanda ta ce: “An kashe iyayena a lokacin yaƙi. Hakan ya sa ba wanda yake kula da ni ko ya taꞌazantar da ni.”
Duk da cewa yaƙi ya sa mutanen nan sun sha wahala sosai, sun sami kwanciyar hankali. Ƙari ga haka, suna da tabbaci cewa dukan yaƙe-yaƙe da tashin hankali za su ƙare nan ba da daɗewa ba. Wannan fitowar Hasumiyar Tsaro za ta yi amfani da Littafi Mai Tsarki don ta bayyana yadda hakan zai faru.