Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • dg kashi 8 pp. 17-19
  • Sashe na 8—Nufe-Nufen Allah Na Tafiya Zuwa Cikawa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sashe na 8—Nufe-Nufen Allah Na Tafiya Zuwa Cikawa
  • Allah Yana Kula da Mu Kuwa da Gaske?
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sabon Sarkin Duniya
  • Abokai Masu Sarauta
  • Sarautar Yancin Kai Zai Kare
  • Mene ne Mulkin Allah?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Mulkin Allah—Sabuwar Sarauta Ta Duniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Menene Mulkin Allah?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Mulkin “da ba Za a Rushe Shi ba Daɗai”
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
Dubi Ƙari
Allah Yana Kula da Mu Kuwa da Gaske?
dg kashi 8 pp. 17-19

Sashe na 8—Nufe-Nufen Allah Na Tafiya Zuwa Cikawa

1, 2. Ina yadda Allah ya yi tanadin kawas da shan wahala ko?

SARAUTANCIN mutane da aljannu masu tawaye sun daɗe ko suna jan iyalin yan-Adam ƙasa ƙasa cikin ƙarnuka dayawa yanzu. Duk da haka, Allah baya yi biris da shan wahalolinmu ba. Maimakon haka, yana yin tanadi don yantadda yan-Adam daga riƙon mugunta da wahala, a duk ƙarnukan nan.

2 A lokacin tawayen a Adnin, Allah ya soma bayana nufe-nufensa don kafa wata gwamnati wadda zata maida duniyar nan gidan aljanna ga mutane. (Farawa 3:15) Nan gaba fa, kamar mai-maganar Allah mai-girma, Yesu fa ya maida gwamnatin Allahn nan ya zama jigon koyaswarsa. Ya ce wai ita ce zata zama begen mutane kaɗai.​—⁠Daniel 2:44; Matta 6:9, 10; 12:⁠21.

3. Minene Yesu ya ƙira gwamnati mai-zuwa ga duniya, kuma don me?

3 Yesu ya ƙira gwamnatin Allah mulki mai-zuwan nan “mulkin sammai,” da shike zata yi sarauta daga sama ne. (Matta 4:17) Ya kuma ƙira ta “mulkin Allah,” da shike Allah ne zai zama Mai-yinta. (Luka 17:20) Can cikin ƙarnuka fa Allah ya hure marubutansa su rubuta annabce-annabce game da waɗanda zasu zama gwamnatin nan da kuma abinda zai kamala.

Sabon Sarkin Duniya

4, 5. Ina yadda Allah ya nuna cewa Yesu shine Sarkinsa wanda ya zaɓa?

4 Yesu ne, wanda kusan shekaru dubu biyu da suka shige, ya cika annabce-annabce dayawa game da wanda zaya zama Sarkin Mulkin Allah. Ya tabbatas cewa shine zaɓen Allah na Masaraucin gwamnati na samaniyar nan bisa mutane. Bayan mutuwarsa kuwa, Allah ya tashe Yesu zuwa rai cikin sama kamar halittan ruhu mai-iko, mara mutuwa. Mutane dayawa sun shaida tashiwarsa daga matattu.​—⁠Ayukan Manzanni 4:10; 9:1-⁠9; Romawa 1:⁠1-⁠4; 1 Korinthiyawa 15:3-⁠8.

5 Sa’annan Yesu ya “zauna a hannun dama na Allah.” (Ibraniyawa 10:12) A wurin yana jirace lokacin da Allah zai ba shi iko shi soma aiki kamar Sarkin Mulkin Allah na samaniya. Wannan ya cika annabci da ke Zabura 110:1, inda Allah ya gaya masa: “Ka zauna ga hannun damana, har in maida maƙiyanka matashin sawunka.”

6. Ina yadda Yesu ya nuna cewa ya inganta ya zama Sarkin Mulkin Allah?

6 Yayinda yake nan duniya, Yesu ya nuna cewa ya inganta don matsayin nan. Duk da shan tsanani fa, ya zaɓa ya riƙe kāmalarsa ga Allah. Ta haka fa, ya nuna cewa Shaitan ya yi ƙarya da da’awar cewa babu wani ɗan-Adam da zai iya kasance da gaskiya ga Allah a ƙalƙashin gwadawa. Yesu, kamiltaccen mutum, ‘Adamu na biyu,’ ya nuna cewa Allah baya ƙusƙura wajen halittan kamiltattun yan-Adam ba.​—⁠1 Korinthiyawa 15:22, 45; Matta 4:​1-⁠11.

7, 8. Wane abubuwa masu kyau ne Yesu ya yi yayinda yake duniya, kuma minene ya nuna?

7 Wane Masarauci ne ya taɓa kamala abubuwa masu-kyau kamar yadda Yesu ya yi cikin yan shekarun hidimarsa? Da ikon ruhu mai-tsarki na Allah fa, Yesu ya warkas da masu ciwo, guragu, makafi, kurame, da bebaye. Har ya tadda matattu! Ya nuna a ƙanƙanin matsayi abinda zaya yi ga mutane a matsayi mai-girma yayinda ya shiga cikin ikon Mulkin.​—⁠Matta 15:​30, 31; Luka 7:​11-⁠16.

8 Yesu ya aika nagarta dayawa yayinda yake nan duniya har da almajirinsa Yohanna ya ce: “Akwai kuma waɗansu abu dayawa da Yesu ya yi; ina tsammani da a ce za a rubuta su kowane ɗaya da duniya da kanta ba zata ɗauki littattafai waɗanda za a rubuta ba.”​—⁠Yohanna 21:25.a

9. Me yasa masu zuciyar kirki suke zuɓowa wurin Yesu?

9 Yesu mai-alheri da tausayi ne, yana da ƙauna mai-girma ga mutane. Yana taimakon talakawa da tsiyayyu, amma baya wariya tsakanin mawadata ko kuwa matsayin wani. Masu zuciyar kirki sun mayas da martani ga gayyatowar Yesu na ƙauna yayinda ya ce: “Ku zo gareni, dukanku da ku ke wahala, masu-nauyin kaya kuma, ni kuwa in ba ku hutawa. Ku ɗauka ma kanku karkiyata, ku koya daga wurina; gama ni mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya. Ku samu hutawa ga rayukanku. Gama karkiyata mai-sauƙi ce, kayana kuma mara-nauyi.” (Matta 11:​28-⁠30) Mutane masu-tsoron Allah suna zuɓowa wurinsa suna kuma sauraron sarautancinsa.​—⁠Yohanna 12:⁠19.

Abokai Masu Sarauta

10, 11. Waɗannene zasu yi rabo da Yesu cikin sarauta bisa duniyar?

10 Kamar yadda gwamnati tana da tarin hakimai fa, haka ma Mulkin Allah na samaniya ta ke. Wasu wuce da Yesu fa zasu yi rabo cikin yin sarauta bisa duniya, gama Yesu ya yi ma abokan tarayyarsa na kurkusa alkawalin cewa zasu yi sarauta tare kamar sarakuna bisa mutane.​—⁠Yohanna 14:2, 3; Ru’ya ta Yohanna 5:⁠10; 20:⁠6.

11 Saboda haka, tare da Yesu fa, an tadda ƙaramin adadin yan-Adam zuwa rai na samaniya. Su suka zama Mulkin Allah da zai kawo madawwamiyar albarka ga mutane. (2 Korinthiyawa 4:14; Ru’ya ta Yohanna 14:​1-⁠3) Tun da daɗewa fa, Jehovah ya kafa tushen sarautanci da zai kawo albarkatai na har abada ga iyalin yan-Adam ko.

Sarautar Yancin Kai Zai Kare

12, 13. Minene Mulkin Allah a shirye yake yanzu ya yi?

12 A cikin wannan ƙarnin Allah ya sa hannu ko sosai cikin harƙoƙin duniya. Kamar yadda sura 9 na mujallar nan zai tattauna shi fa, annabcin Littafi Mai-tsarki ya nuna ko cewa an kafa Mulkin Allah ko ƙalƙashin Kristi tun 1914 kuma yanzu a shirye yake don kawas da dukan shirin Shaitan. Mulkin a shirye yake ya soma “sarauta tsakiyar maƙiyan [Kristi].”​—⁠Zabura 110:⁠2.

13 Game da wannan fa annabci da ke Daniel 2:44 ya ce: “A cikin zamanin waɗannan sarakuna [waɗanda suke wanzuwa yanzu] kuwa, Allah mai-sama zaya kafa wani mulki [cikin sama], wanda ba za a rushe shi ba daɗai, sarautassa kuwa ba za a bar ma wata al’umma [na sarautar yan-Adam kuma] ba. Amma [Mulkin Allah] zaya farfashe dukan waɗannan mulkoki ya cinye su, shi kuwa zaya tsaya har abada.”​—⁠Revised Standard Version.

14. Waɗanne albarkatai ne zasu zo kamar sakamakon ƙarshen sarautar yan-Adam?

14 Yayinda aka cire dukan sarautanci masu yancin kansu daga Allah fa, sarautar Mulkin Allah bisa duniya zai cika. Kuma domin Mulkin yana sarauta daga sama ne fa, babu yan-Adam da zasu ɓata shi. Ikon sarauta zai kasance inda yake a farko, watau cikin sama, tare da Allah. Kuma tun da shike sarautar Allah ne zai mallake duniya, ba za a ruɗas da wani ta wurin addinin ƙarya kuma, ko kuwa ussan ilimin yan-Adam mara ƙoshedwa da siyasa ba. Babu wani daga cikin waɗannan abubuwa da za a yarda masa ya wanzu kuma.​—⁠Matta 7:​15-⁠23; Ru’ya ta Yohanna, surori 17 zuwa 19.

[Hasiya]

a Don cikakken tarihin rayuwar Yesu, ka ga littafin nan The Greatest Man Who Ever Lived, wanda Watchtower Society, suka buga 1991.

[Hoto a shafi na 18]

Yayinda yake nan duniya Yesu ya warkas da masu ciwo, tadda matattu don ya nuna abinda zaya yi cikin sabuwar duniya

[Hoto a shafi na 19]

Mulkin Allah zai farfashe dukan ire-iren sarauta waɗanda suka yance kansu daga gareshi

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba