SASHE NA 8
Ka Ƙi Addinin Ƙarya; Ka Yi Addini na Gaskiya
1. Game da bauta, wane zaɓe mutane suke fuskanta a yau?
YESU ya ce: “Wanda ba shi wajena gāba da ni ya ke.” (Matta 12:30) Dole ne mu kasance a gefen Jehobah ko kuma na Shaiɗan. Yawancin mutane suna tunanin cewa suna bauta wa Allah yadda yake so, amma Littafi Mai Tsarki ya ce Shaiɗan yana “ruɗin dukan duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 12:9) Miliyoyin mutane sun gaskata cewa suna bauta wa Allah, amma hakikanin gaskiya suna bauta wa Shaiɗan Iblis ne! Mutane a yau suna fuskantar zaɓe: Dole ne su bauta wa Jehobah, “Allah na gaskiya,” ko kuma Shaiɗan, “uban ƙarya.”—Zabura 31:5; Yohanna 8:44.
Ka Samu ’Yanci Daga Addinin Ƙarya
2. Ta wace hanya ɗaya ce Shaiɗan yake so ya hana mutane bauta wa Jehobah?
2 Yanke shawarar bauta wa Jehobah ita ce zaɓe cikin hikima zaɓe da yake kawo yardar Allah. Amma Shaiɗan ba ya farin ciki da dukan wanda yake bauta wa Allah; yana haddasa bala’i ga waɗanda suke yin haka. Hanya ɗaya da yake yin haka ita ce ta wajen ba’a ko kuma hamayya daga wasu, har da abokane da kuma ’yan’uwa. Yesu ya yi gargaɗi: “Maƙiyan mutum za su kasance daga iyalin gidansa.”—Matta 10:36.
3. Idan iyalinka ko kuma abokananka suka yi hamayya da bautarka ga Allah, me za ka yi?
3 Idan haka ya faru da kai, me za ka yi? Mutane da yawa sun sani cewa hanyar bautarsu ba daidai ba ce, duk da haka suna jinkirin ’yantar da kansu daga gare ta. Suna tunanin cewa zai kasance cin amanar iyalinsu idan suka yi haka. Amma hakan daidai ne? Idan ka gano cewa ’yan’uwanka suna shan miyagun ƙwayoyi, ba za ka yi musu gargaɗi ba cewa ƙwayoyin za su yi musu lahani? Ba za ka bi su ka riƙa shan waɗannan ƙwayoyin ba, ko za ka sha ne?
4. Menene Joshua ya gaya wa Isra’ilawa game da bauta a zamaninsa?
4 Joshua ya ƙarfafa Isra’ilawa su bar ayyukansu marasa kyau na addini da kuma al’adu na kakaninsu. Ya ce: “Yanzu fa sai ku ji tsoron Ubangiji, ku bauta masa cikin sahihanci da cikin gaskiya: ku kawar da allolin nan waɗanda ubanninku suka bauta masu a ƙetaren Kogin, da cikin Masar; ku bauta ma Ubangiji.” (Joshua 24:14) Joshua mai aminci ne ga Allah, kuma Jehobah ya yi masa albarka. Idan mun kasance amintattu ga Jehobah, zai yi mana albarka mu ma.—2 Samu’ila 22:26.
Ka Halaka Abubuwa da Ake Amfani da Su a Bautar Ƙarya
5. Me ya sa za mu halaka abubuwa na sihiri?
5 Samun ’yanci daga addinin ƙarya yana nufin halaka kowane abin sihiri da muke da shi, kamar su magani, laya, zoben sihiri da kuma kambu, da irin waɗannan abubuwa. Wannan yana da muhimmanci domin zai nuna cewa mun dogara ga Jehobah.
6. Menene Kiristoci na farko suka yi da littattafansu na sihiri?
6 Ka yi la’akari da abin da wasu Kiristoci na farko suka yi sa’ad da suka shawarta su yi addini na gaskiya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Waɗansu kuwa ba kaɗan ba daga masu-yin sihiri suka tattara littattafansu, suka ƙone su a gaban dukan mutane.”—Ayyukan Manzanni 19:19.
7. Menene za mu iya yi idan aljannu suka dame mu?
7 Wasu da suka fara bauta wa Jehobah waɗanda dā suna yin maita, duba, ko kuma sihiri wataƙila aljannu su dame su. Idan hakan ya faru da kai, ka ɗaga murya ka kira Jehobah cikin addu’a, kana kiran sunansa. Zai taimake ka.—Misalai 18:10; Yaƙub 4:7.
8. Yaya Kiristoci suke ɗaukan gumaka, siffofi, da kuma hotuna da ake amfani da su wajen bautar ƙarya?
8 Waɗanda suke so su bauta wa Jehobah ba za su ajiye ko kuma su yi amfani da gunki ba, ko siffa, ko hoto na bautar ƙarya. Kiristoci na gaskiya “bisa ga bangaskiya [su] ke tafiya, ba bisa ga gani ba.” (2 Korintiyawa 5:7) Suna daraja dokar Allah da ta hana amfani da gunki wajen bauta.—Fitowa 20:4, 5.
Ka Yi Tarayya da Mutanen Jehobah
9. Wace shawara ce Littafi Mai Tsarki ya bayar game da zama mai hikima?
9 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka yi tafiya tare da masu-hikima, kai kuwa za ka yi hikima.” (Misalai 13:20) Idan muna so mu zama masu hikima, muna bukatar mu yi tafiya, ko kuma tarayya, da Shaidun Jehobah. Mutane ne da suke tafiya bisa hanyar da take kai wa zuwa rai.—Matta 7:14.
10. Ta yaya Shaidun Jehobah za su taimake ka ka bauta wa Allah?
10 Hakika Shaidun suna damuwa game da mutane. Aikinsu su taimaki mutane masu zukatan kirki ne su fahimci gaskiyar Littafi Mai Tsarki da take kai wa zuwa rai madawwami. Za su taimake ka ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kai, kyauta. Za su amsa tambayoyi da kake da su kuma su nuna maka yadda za ka yi amfani da ilimi na Littafi Mai Tsarki a rayuwarka.—Yohanna 17:3.
11. Ta yaya taron Kirista zai taimake ka?
11 A taronsu, da ake yi a Majami’ar Mulki, za ka ƙara ilimi game da hanyoyin Jehobah. Za ka ƙarfafa a muradinka na yin addini na gaskiya. Kuma za ka koyi yadda za ka taimake wasu su koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki.—Ibraniyawa 10:24, 25.
12. Ta yaya addu’a za ta taimake ka ka bauta wa Allah?
12 Sa’ad da kake ƙara ilimi game da nufin Jehobah da kuma ƙudurinsa, wataƙila ka ƙara fahimtar hanyoyinsa na ƙauna. Kuma ya kamata ka ƙara muradinka na yin abin da zai faranta masa rai kuma ka guji abin da zai ɓata masa rai. Ka tuna cewa za ka iya yi wa Jehobah addu’a ka roƙe shi ya taimake ka, ka yi abin da yake daidai kuma ka guje wa abin da ba daidai ba.—1 Korintiyawa 6:9, 10; Filibiyawa 4:6.
Ta yaya za ka yi bauta ta gaskiya?
13. Ta yaya za ka faranta wa Jehobah rai?
13 Da shigewar lokaci, sa’ad da kake girma a ruhaniya, babu shakka za ka ga dalilin zama Mashaidin Jehobah da ya keɓe kai ya yi baftisma. Ta kasancewa cikin mutanen Jehobah, za ka faranta wa Jehobah rai. (Misalai 27:11) Za ka kasance tsakanin mutane masu farin ciki da Allah ya ce game da su: “Ni zauna a cikinsu, ni yi tafiya a cikinsu; in zama Allahnsu, su kuma su zama mutanena.”—2 Korintiyawa 6:16.