Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • bm sashe na 12 p. 15
  • Hurarriyar Hikima don Samun Rai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Hurarriyar Hikima don Samun Rai
  • Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
  • Makamantan Littattafai
  • Sulemanu Sarki Ne Mai Hikima
    Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
  • Darussa Daga Littafin Misalai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
bm sashe na 12 p. 15

Sashe 12

Hurarriyar Hikima don Samun Rai

Littafin Misalai yana ƙunshe ne da hurarriyar shawara, Sulemanu ne ya rubuta yawancinsu kuma yana ɗauke da ja-gorancin da ake bukata a rayuwa ta yau da kullum

SHIN Jehobah Sarki ne mai hikima? Hanya mafi kyau ta amsa wannan tambayar ita ce yin la’akari da shawarar da yake bayarwa. Tana da amfani kuwa? Yin amfani da ita yana kyautata rayuwa kuma ya sa ta kasance mai ma’ana? Sulemanu Sarki mai hikima ya rubuta ɗarurruwan karin magana. Sun shafi kusan dukan sashe na rayuwa. Yi la’akari da wasu misalai.

Dogara ga Allah. Dogara tana da muhimmanci idan muna so mu kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. Sulemanu ya rubuta: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: A cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka.” (Misalai 3:5, 6) Dogara ga Allah ta wajen neman ja-gorancinsa da kuma yi masa biyayya yana sa rayuwa ta kasance da ma’ana sosai. Irin wannan tafarkin yana sa mutum ya faranta zuciyar Allah kuma zai sa Jehobah ya mayar da martani ga batutuwan da babban maƙiyansa, Shaiɗan ya ta da.—Misalai 27:11.

Yin amfani da hikima sa’ad da muke sha’ani da wasu. Shawarar da Allah ya ba magidanta, matan aure, da yara ta fi muhimmanci sosai a yau. Allah ya shawarci magidanta, “ka yi murna da matar kuruciyarka,” hakan na nufin cewa maigida ya kasance da aminci ga matarsa. (Misalai 5:18-20) Matan aure suna da kwatanci mai kyau a cikin littafin Misalai na mace mai tsarkin rai wadda mijinta da yaranta suke ƙaunarta sosai. (Misalai, sura na 31) Kuma yara za su ga ja-gorancin yin biyayya ga iyayensu. (Misalai 6:20) Wannan littafin ya kuma nuna cewa abota na da muhimmanci, domin ware kai yana jawo son kai. (Misalai 18:1) Abokai suna iya rinjayarmu mu yi abin da ke da kyau ko marar kyau, saboda haka, muna bukatan mu yi amfani da hikima sa’ad da muke zaɓansu.—Misalai 13:20; 17:17.

Ka yi amfani da hikima sa’ad da kake kula da jikinka. Littafin Misalai yana ɗauke da shawara mai tamani game da guje wa mugun shan giya, mu yi tunanin da zai daɗa ga lafiyar jikinmu mu kuma yaƙi tunanin da bai da kyau, mu kuma zama masu aiki tuƙuru. (Misalai 6:6; 14:30; 20:1) Ya yi gargaɗi cewa dogara da shawarar mutum wadda ta bambanta da na Allah zai kai ga halaka. (Misalai 14:12) Ya aririce mu mu kāre zuciyarmu daga abubuwan da za su ɓata ta, kuma ya tuna mana cewa “daga cikinta [zuciya] mafitan rai su ke.”—Misalai 4:23.

Miliyoyin mutane a dukan duniya sun ga cewa bin wannan shawarar yana kyautata rayuwa. A sakamakon haka, suna da dalilai masu yawa su amince cewa Jehobah ne Sarkinsu.

—An ɗauko daga littafin Misalai.

◼ Menene za mu iya koya daga yin nazarin littafin Misalai?

◼ Wane ja-goranci ne littafin Misalai ya yi tanadinsa game da dogara ga Allah da kuma yin amfani da hikima sa’ad da muke sha’ani da wasu da kuma a yadda muke kula da kanmu?

[Akwati a shafi na 15]

MAI-WA’AZI

A ina za a iya samun gamsuwa da ma’ana a rayuwa? Sulemanu yana da dama mai kyau na neman amsar. Tun da yake yana da arziki, hikima, da kuma iko mai yawan gaske, ya bincika ya gani ko waɗannan abubuwan za su ba shi farin ciki na gaskiya. Ya biɗi duk wani jin daɗi da abubuwan duniya za su iya kawowa, ya auri mata kyawawa masu yawa, kuma ya more nishaɗi mafi daɗi sosai. Ya yi manyan gine-gine. Ya bincika rubuce-rubucen hikima. Menene ya gani? “Duk banza ne.” Amma, ya faɗi wannan gaskiyar: “Wannan shi ne ƙarshen zancen; duk an rigaya an ji: ji tsoron Allah, ka kiyaye dokokinsa; gama wannan kaɗai ne wajibin mutum.”—Mai-Wa’azi 12:8, 13.

[Taswira a shafi na 15]

Farawa

Fitowa

Levitikus

Littafin Lissafi

Kubawar Shari’a

Joshua

Alƙalawa

Ruth

1 Sama’ila

2 Sama’ila

1 Sarakuna

2 Sarakuna

1 Labarbaru

2 Labarbaru

Ezra

Nehemiya

Esther

Ayuba

Zabura

Misalai ●

Mai-Wa’azi ●

Waƙar Waƙoƙi

Ishaya

Irmiya

Makoki

Ezekiel

Daniyel

Hosiya

Joel

Amos

Obadiya

Yunana

Mikah

Nahum

abakkuk

Zafaniya

Haggai

Zakariya

Malakai

Matta

Markus

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba