Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • yc darasi na 13 pp. 28-29
  • Timoti Ya Taimaki Mutane

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Timoti Ya Taimaki Mutane
  • Ku Koyar da Yaranku
  • Makamantan Littattafai
  • Timothawus Yana Shirye Ya Yi Hidima
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Bulus da Timotawus
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • “Dana Cikin Ubangiji, Kaunatacce, Mai-Aminci.”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Matasa, Ku Biɗi Makasudan Da Za Su Daraja Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Dubi Ƙari
Ku Koyar da Yaranku
yc darasi na 13 pp. 28-29
Timoti yana koyo daga mahaifiyarsa, Afiniki, da kakarsa, Lois

DARASI NA 13

Timoti Ya Taimaki Mutane

Timoti matashi ne da ya taimaka wa mutane, kuma ya yi tafiya zuwa wurare da yawa don ya yi hakan. Saboda wannan, ya yi farin ciki sosai. Za ka so ka ji labarinsa?—

Mamar Timoti da kakarsa sun koya masa game da Jehobah

Timoti ya yi girma a birnin da ake kira Listra. Tun yana ƙarami, kakarsa Lois da mamarsa Afiniki sun soma koya masa game da Jehobah. Yayin da Timoti yake girma, ya so ya taimaka wa mutane su san Jehobah.

A lokacin da Timoti ɗan saurayi ne, Bulus ya gaya masa ya bi shi yin wa’azi a wasu wurare. Timoti ya yarda don yana shirye ya taimaki mutane.

Timoti ya bi Bulus zuwa birnin Tasalunika a Makidoniya. Sun yi tafiya mai nisa kuma sun shiga jirgin ruwa kafin su isa birnin. Sa’ad da suka isa, sun taimaki mutane da yawa su koya game da Jehobah. Amma wasu mutane sun yi fushi har sun yi ƙoƙari su ji musu rauni. Saboda haka, Bulus da Timoti suka bar birnin kuma suka koma yin wa’azi a wasu wurare dabam.

Timoti yana tafiya da manzo Bulus a jirgin ruwa

Timoti ya yi farin ciki kuma ya ji dadin rayuwa

Bayan wasu watanni, Bulus ya gaya wa Timoti ya koma Tasalunika don ya ga yadda ’yan’uwan suke ƙoƙarin bauta wa Jehobah. Bai yi masa sauƙi ya koma wannan birnin da mutanen suke da mugunta ba. Amma Timoti ya tafi, domin ya damu da ’yan’uwan da ke wurin. Da ya dawo sai ya gaya wa Bulus labari mai daɗi. Ya ce masa ’yan’uwa da ke Tasalunika suna ƙoƙari sosai.

Timoti ya yi shekaru da yawa yana wa’azi tare da Bulus. Bulus ya taɓa rubuta cewa Timoti ne mutumin da ya dace ya aike shi don ya taimaka wa ikilisiyoyi. Timoti ya ƙaunaci Jehobah da kuma mutane.

Kana ƙaunar mutane kuma kana so ka taimaka musu su koya game da Jehobah?— Idan ka yi hakan, za ka yi farin ciki sosai kamar Timoti!

KARANTA NASSOSIN NAN

  • 2 Timotawus 1:5; 3:15

  • Ayyukan Manzanni 16:1-5; 17:1-10

  • 1 Tasalonikawa 3:2-7

  • Filibiyawa 2:19-22

TAMBAYOYI:

  • A wane birni ne Timoti ya yi girma?

  • Timoti ya so ya yi tafiya da Bulus kuwa? Me ya sa?

  • Me ya sa Timoti ya koma Tasalunika?

  • Mene ne za ka yi don ka yi farin ciki kamar Timoti?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba