Menene Mulkin Allah?
MENENE jigon wa’azin Yesu? Yesu kansa ya ce, Mulkin Allah ne. (Luka 4:43) Sa’ad da mutane suka saurare shi, babu shakka sun ji ya ambaci wannan Mulki sau da yawa. Sun yi mamaki ne ko kuma abin ya ruɗar da su? Sun yi tambaya ne cewa menene ne wannan Mulkin? A’a. A Linjila babu irin waɗannan tambayoyin. To shin Mulkin Allah abu ne da waɗannan mutane suka riga suka sani?
Gaskiya ita ce, Nassosi masu tsarki da Yahudawa suke ba wa daraja sun kwatanta Mulkin, sun yi bayani dalla-dalla game da abin da Mulkin yake nufi da kuma abin da zai cim ma. A yau, za mu ƙara fahimtar Mulkin a wannan hanyar, wato daga Littafi Mai Tsarki. Bari mu bincika wasu abubuwa bakwai na gaskiya da Littafi Mai Tsarki ya koyar game da Mulkin. Yahudawan zamanin Yesu da kuma waɗanda suka kasance kafin su, suna sane da abubuwa nan uku na farko. Wasu uku kuma Kristi ne ko kuma manzanninsa suka bayyana su a ƙarni na farko. Na ƙarshe kuma ya bayyana ne a zamaninmu.
1. Mulkin Allah gwamnati ce takamaimai wadda za ta kasance har abada. Annabci na farko na Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah zai aiko da mai ceto ga ’yan Adam masu aminci. An kira shi “zuriya,” kuma zai kawar da dukan miyagun abubuwa da suka fara faruwa sa’ad da Adamu, Hauwa’u da Shaiɗan suka yi tawaye. (Farawa 3:15) Bayan shekaru masu yawa, aka gaya wa Sarki Dauda mai aminci wani abu mai ban sha’awa game da “zuriyar” ko kuma Almasihu. Zai yi sarautar wani Mulki. Wannan gwamnatin za ta bambanta da dukan wasu gwamnatoci. Za ta dawwama har abada.—2 Samuila 7:12-14.
2. Mulkin Allah za ta hallaka dukan gwamnatocin ’yan Adam. An bai wa annabi Daniel wahayi, a cikin wahayin ya ga masarauta da suka mallaki duniya, daga zamanin dā har zuwa zamaninmu. Ka lura da ƙarshen wannan wahayi mai ban sha’awa: “A cikin zamanin waɗannan sarakuna [mutane na ƙarshe] kuwa, Allah mai-sama za ya kafa wani mulki, wanda ba za a rushe shi ba daɗai, sarautassa kuwa ba za a bar ma wata al’umma ba; amma za ya parpashe dukan waɗannan mulkoki ya cinye su, shi kuwa za ya tsaya har abada.” Saboda haka, dukan Masarauta, ko kuma gwamnatoci na wannan duniya, da yaƙe-yaƙensu da lalaci, za a halaka su har abada. Kamar yadda annabcin Daniel ya nuna, Mulkin Allah ba da daɗewa ba za ya mallaki dukan duniya. (Daniel 2:44, 45) Wannan Mulkin ne zai kasance gwamnati ɗaya kawai da ke wanzuwa.a
3. Mulkin Allah zai kawar da yaƙe-yaƙe, cututtuka, yunwa, har da mutuwa. Annabce-annabce masu ban sha’awa na Littafi Mai Tsarki sun nuna abin da Mulkin Allah zai yi a nan duniya. Gwamnatin za ta cim ma abin da babu wata ƙungiyar ’yan Adam da ta yi ko kuma za ta iya yi. Ka yi tunani, an halaka dukan makaman yaƙi har abada! “Ya sa yaƙoƙi su ƙare har iyakar duniya.” (Zabura 46:9) Likitoci, asibitoci, da kuma dukan cututtuka ba za su kasance ba. “Wanda ya ke zaune a ciki ba za ya ce, Ina ciwo ba.” (Ishaya 33:24) Yunwa, rashin abinci ba za su kasance ba. “Za a yi albarkar hatsi a ƙasa a bisa ƙwanƙolin duwatsu.” (Zabura 72:16) Ba za a yi jana’iza, makoki, makabarta, ɗakin gawawwaki da kuma baƙin ciki da ke biyo bayansu ba. A ƙarshe za a halaka abokiyar gabanmu mutuwa. Allah za “ya haɗiye mutuwa har abada: Ubangiji Yahweh za ya shafe hawaye daga dukan fuskoki.”—Ishaya 25:8.
4. Mulkin Allah yana da Sarki da Allah ya zaɓa. Almasihu ba shi ya naɗa kansa ba, ba kuma mutane ne ajizai suka zaɓe shi ba. Jehobah Allah ne da kansa ya zaɓe shi. Ma’anar laƙabin nan ke nan Almasihu da kuma Kristi. Dukan kalmomin biyu suna nufin “Shafaffe.” Saboda haka, Sarkin shafaffe ne, kuma matsayin da Jehobah ya ba shi ke nan. Allah ya ce game da shi: “Ku duba barana wanda ni ke tokara; zaɓaɓena wanda raina yana murna da shi: na ɗibiya masa ruhuna: za ya kawo shari’a ga al’ummai.” (Ishaya 42:1; Matta 12:17, 18) Wa ya fi Mahaliccinmu sanin irin Sarki da muke bukata?
5. Sarkin Mulkin Allah ya nuna tamaninsa a gaban dukan ’yan Adam. Yesu Banazare ya kasance wannan Almasihu da aka yi alkawarinsa. An haife shi cikin zuriyar da Allah ya zaɓa. (Farawa 22:18; 1 Labarbaru 17:11; Matta 1:1) Sa’ad da yake duniya ya cika annabce-annabce masu yawa game da Almasihu da aka rubuta su shekaru masu yawa kafin lokacin. Kuma an nuna cewa shi ne Almasihu daga samaniya. Ta yaya? Allah ya yi magana daga sama, ya ce Ɗansa ne; mala’iku sun nuna cewa Yesu shi ne Almasihu da aka yi annabcinsa; kuma Yesu ya yi ayyukan al’ajabi, sau da yawa a gaban dubban mutane, waɗanda babu shakka da ikon Allah ya yi su.b Yesu ya nuna sau da yawa irin sarauta da zai yi. Yana da iko da kuma muradin son ya taimaka wa mutane. (Matta 8:1-3) Ba shi da son kai, yana da juyayi, da gaba gaɗi, da kuma tawali’u. Tarihin rayuwarsa a duniya yana rubuce cikin Littafi Mai Tsarki domin kowa ya karanta.
6. Kristi yana da abokan sarauta 144,000 a Mulkin Allah. Yesu ya ce wasu har da manzanninsa za su yi sarauta tare da shi a samaniya. Ya kira wannan rukunin “ƙaramin garke.” (Luka 12:32) Daga baya, aka gaya wa manzo Yohanna cewa wannan ƙaramin garken adadinsu 144,000 ne. Za a ba su aiki mai ban sha’awa a samaniya, sarauta tare da Kristi da kuma kasancewa firistoci.—Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10; 14:1, 3.
7. Mulkin Allah ya fara sarauta a samaniya yanzu, kuma yana shirye ya kafa ikonsa bisa dukan duniya. Wannan tana ɗaya daga cikin gaskiya masu ban sha’awa da za mu koya. Littafi Mai Tsarki ya ba da tabbaci cewa an ba wa Yesu ikon zama Sarki a samaniya. Yana sarauta a can yanzu a wannan zamaninmu, ba da daɗewa ba zai fara sarautar dukan duniya kuma ya cika annabce-annabce masu ban sha’awa da muka riga muka ambata. Amma ta yaya za mu tabbata cewa Mulkin Allah yana sarauta a yanzu? Kuma yaushe ne zai fara sarauta bisa duniya?
[Hasiya]
a Irin waɗannan annabce-annabce sun nuna cewa Mulkin Allah ba abu ba ne kawai da ke cikin zuciyarmu, kamar yadda ake koya wa mutane da yawa. Ka karanta talifin nan “Masu Karatu Sun Yi Tambaya,” da ke shafi na 31.
b Alal misali ka karanta Matta 3:17; Luka 2:10-14; Yohanna 6:5-14.