Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 4/1 pp. 8-10
  • Abin da Yesu Ya Koyar Game da Mulkin Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Abin da Yesu Ya Koyar Game da Mulkin Allah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Fada Game da Mulkin Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
  • Minene Mulkin Allah?
    Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
  • Game da Mulkin Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Menene Mulkin Allah?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 4/1 pp. 8-10

Abin da Yesu Ya Koyar Game da Mulkin Allah

‘Ya yi ta yawo a cikin birane da ƙauyuka, yana wa’azin . . . bishara ta mulkin Allah.’—LUKA 8:1.

MUNA son tattauna abubuwan da ke da muhimmanci a gare mu, da kuma waɗanda ke da tamani a gare mu. Kamar yadda Yesu da kansa ya ce, “daga cikin yalwar zuciya baki ya kan yi magana.” (Matta 12:34) Idan muka duba abubuwan da Yesu ya ce game da hidimarsa, za mu iya kammala cewa Mulkin Allah yana da muhimmanci a wurinsa.

Menene Mulkin Allah? Mulki gwamnati ce da ke da sarki. Saboda haka, Mulkin Allah gwamnati ce da Allah ya kafa. Yesu ya yi magana sosai game da Mulkin Allah, kuma shi ne jigon saƙonsa. An ambata wannan Mulkin fiye da sau 110 a cikin Linjilolin guda huɗu. Amma Yesu bai koyar da kalmomi kawai ba. Abubuwan da ya yi su ma sun koyar da abubuwa masu yawa game da Mulkin Allah da kuma abin da zai yi.

Wanene Sarkin? Ba mutane ba ne suka zaɓi Sarkin Mulkin Allah ba. Maimakon haka, Allah ne da kansa ya zaɓi wannan Masaraucin. A cikin koyarwarsa, Yesu ya bayyana cewa shi ne wanda Allah ya zaɓa ya zama Sarki.

Yesu ya san cewa annabce-annabcen da ke cikin Littafi Mai Tsarki sun annabta cewa Almasihun da aka yi alkawarinsa ne zai yi sarauta bisa madawwamin Mulkin. (2 Sama’ila 7:12-14; Daniyel 7:13, 14; Matta 26:63, 64) Ka tuna cewa Yesu ya kira kansa a fili cewa shi ne Almasihun da aka annabta. Ta haka, Yesu yana jaddada cewa shi ne Sarkin da Allah ya naɗa. (Yohanna 4:25, 26) Shi ya sa a lokatai da yawa Yesu ya yi amfani da furcin nan “mulkina.”—Yohanna 18:36.

Yesu ya kuma koyar cewa akwai wasu da za su yi sarauta tare da shi a wannan Mulkin. (Luka 22:28-30) Ya kira waɗannan abokan sarautarsa “ƙaramin garke,” domin adadinsu yana da iyaka. Ya ce game da su: “Ubanku yana jin daɗi shi ba ku mulkin.” (Luka 12:32) Littafi na ƙarshe a cikin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mutane 144,000 ne za su sami gatan yin sarauta tare da Kristi.—Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10; 14:1.

A ina Mulkin yake? Yesu ya gaya wa masarauci ɗan ƙasar Roma, Bilatus Ba-bunti cewa, “mulkina ba na wannan duniya ba ne.” (Yohanna 18:36) Mulkin Allah a ƙarƙashin Kristi ba zai yi sarauta ta hanyar mutane ba. A kai a kai Yesu ya kira Mulkin Allah “mulkin sama.”a (Matta 4:17; 5:3, 10, 19, 20) Saboda haka, Mulkin Allah gwamnati ce ta samaniya.

Yesu zai koma sama bayan zamansa a duniya. A can, ya ce zai ‘shirya wuri,’ don buɗe wa abokan sarautarsa hanyar zuwa samunsa a sama.—Yohanna 14:2, 3.

Menene Mulkin ya cim ma? Yesu ya koya wa masu sauraronsa su yi addu’a ga Allah: “Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.” (Matta 6:9, 10) Ana yin nufin Allah a sama. Ta hanyar wannan Mulkin ne za a cika nufin Allah game da duniya. Don a cim ma haka, Mulkin zai kawo gagarumin canje-canje a wannan duniyar.

Menene Mulkin zai yi a duniya? Yesu ya koyar da cewa Mulkin Allah zai kawar da mugunta ta wajen cire waɗanda suka ƙudurta aikata ta. (Matta 25:31-34, 46) Hakan zai kawo ƙarshen dukan ire-iren ɓatanci da mugunta. Yesu ya koyar da cewa duniya za ta cika da mutane “masu-tawali’u,” masu aminci, masu gafartawa, “masu-tsabtan zuciya,” da kuma masu son zaman lafiya.—Matta 5:5-9.

Waɗannan mutane masu aminci za su zauna ne a doron ƙasar da aka gurɓata? Ko kaɗan! Yesu ya yi alkawarin cewa duniya za ta fuskanci canje-canje a ƙarƙashin Mulkin Allah. Wani mutumin da ake son a kashe tare da Yesu ya ce: “Yesu, ka tuna da ni lokacinda ka shiga mulkinka.” Sai Yesu ya ce masa: ‘Gaskiya ina ce maka yau, kana tare da ni cikin Al’janna.’ (Luka 23:42, 43) Hakika, Mulkin Allah zai mai da wannan duniyar zuwa aljanna, irin wadda ta wanzu a lambun Adnin.

Menene kuma wannan Mulkin zai yi wa ’yan Adam? Ba wai alkawari kawai Yesu ya yi ba game da abin da Mulkin Allah zai yi. Ya kuma nuna abin da Mulkin zai yi. Yesu ya yi warkarwa masu yawa ta hanyar mu’ujizai, hakan kaɗan ne kawai daga cikin abubuwa masu yawan gaske da zai yi a nan gaba sa’ad da ya soma sarauta a Mulkinsa. Hurarren Linjila ya ce game da Yesu: “Yesu kuwa ya yi yawo cikin dukan Galili, yana koyarwa a cikin majami’unsu, yana wa’azin bishara ta mulkin, yana warkar da kowace irin cuta da kowane irin rashin lafiya a cikin mutane.”—Matta 4:23.

Yesu ya yi warkarwa dabam-dabam. Ya “buɗe idanun mutum wanda aka haife shi da makanta.” (Yohanna 9:1-7, 32, 33) Ta wajen taɓa shi a hankali, Yesu ya warkar da wani mutumin da ke da muguwar cutar kuturta. (Markus 1:40-42) Sa’ad da aka kawo masa “wani kurma, mai-ana’ana kuma,” Yesu ya nuna cewa zai iya sa “kurame . . . su ji, bebaye kuma su yi magana.”—Markus 7:37.

Mutuwa ma ba ta fi ƙarfin Sarkin da Allah ya naɗa ba. A lokatai uku da ke a rubuce, Yesu ya ta da mutane daga matattu. Ya ta da ɗa tilo na wata gwauruwa daga matattu, wata yarinya ’yar shekara sha biyu, da kuma ƙaunataccen abokinsa Li’azaru.—Luka 7:11-15; 8:41-55; Yohanna 11:38-44.

Sa’ad da yake kwatanta rayuwa mai kyau a nan gaba da ke jiran talakawan Mulkin Allah, Yesu ya annabta ta hanyar manzo Yohanna: “Duba, mazaunin Allah yana wurin mutane, za ya zauna tare da su kuma, za su zama al’ummai nasa, Allah kuma da kansa za ya zauna tare da su, ya zama Allahnsu: zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.” (Ru’ya ta Yohanna 1:1; 21:3, 4) Ka yi tunanin duniyar da babu hawaye ko baƙin ciki, babu ciwo, da kuma mutuwa! A wannan lokacin ne addu’ar da Yesu ya koya mana za ta cika sosai, wato, za a yi nufin Allah da gaske a duniya kamar yadda ake yi a sama.

A wane lokaci ne Mulkin Allah zai zo? Yesu ya koyar da cewa somawar sarautarsa ta mulki zai yi daidai da wani lokaci na musamman da ya kira ‘zuwansa.’ Yesu ya yi annabci dalla-dalla da za su nuna sa’ad da zuwansa a ikon mulki zai soma. Wannan lokacin zai cika da matsaloli a dukan duniya, har da yaƙe-yaƙe, yunwa, girgizar ƙasa, annoba, da kuma ƙaruwar mugunta. (Matta 24:3, 7-12; Luka 21:10, 11) Waɗannan da wasu fasaloli masu yawa da Yesu ya annabta musamman sun bayyana tun shekara ta 1914, shekarar da Yaƙin Duniya na Ɗaya ya ɓarke. Da haka, Yesu yana sarauta a matsayin Sarki a yanzu. Ba da daɗewa ba lokaci zai zo da Mulkin zai zo ya sa a yi nufin Allah a duniya.b

Ta yaya ne zuwan Mulkin Allah zai shafi rayuwarka? Hakan ya dangana ne da yadda ka zaɓi yin na’am da saƙon Yesu.

[Hasiya]

a Furcin nan “mulkin sama” ya bayyana sau talatin a cikin Linjilar Matta.

b Don cikakken tattaunawa game da yadda muka san cewa Mulkin Allah yana nan tafe, ka duba babi na 9, “Muna Rayuwa ne a ‘Kwanaki na Ƙarshe’?,” da ke cikin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa shi.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba