Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp20 Na 1 pp. 12-13
  • Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Fada Game da Mulkin Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Fada Game da Mulkin Allah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Yesu Ya Koyar Game da Mulkin Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Game da Mulkin Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Minene Mulkin Allah?
    Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
  • Mene ne Mulkin Allah?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
wp20 Na 1 pp. 12-13
Hoton duniya daga sarari sa’ad da rana take haskaka ta

Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Faɗa Game da Mulkin Allah

Yesu ya koya wa mabiyansa su riƙa wannan addu’ar: “Ubanmu wanda yake cikin sama, a kiyaye sunanka da tsarki. Mulkinka ya zo, bari a yi nufinka a cikin duniya.” (Matiyu 6:​9, 10) Mene ne Mulkin Allah? Mene ne Mulkin zai magance mana? Kuma me ya sa ya kamata mu riƙa addu’a Mulkin Allah ya zo?

Yesu ne Sarkin Mulkin Allah.

Luka 1:​31-33: ‘Za ki ba shi suna Yesu. Zai zama babban mutum, kuma za a ce da shi Ɗan Mafi Ɗaukaka. Ubangiji Allah zai ba shi kujerar mulkin kakansa Dauda. Zai yi mulkin gidan Yakub har abada, mulkinsa kuma ba zai ƙare ba!’

Abin da Yesu ya yi wa’azi a kai musamman shi ne Mulkin Allah.

Matiyu 9:35: “Yesu ya bi dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami’u, yana shelar labari mai daɗi na Mulkin Allah, yana kuma warkar da mutane daga kowane irin ciwo da rashin lafiya.”

Yesu ya gaya wa almajiransa alamar da za ta sa su san cewa Mulkin ya yi kusa.

Matiyu 24:7: ‘Al’umma za ta tasar wa al’umma, mulki ya tasar wa mulki. Za a kuma yi yunwa da girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam.’

A yau, mabiyan Yesu suna wa’azi game da Mulkin Allah a ko’ina a duniya.

Matiyu 24:14: “Kuma za a ba da wannan labari mai daɗi na mulkin sama domin shaida ga dukan al’umma, sa’an nan ƙarshen ya zo.”

Abin da Ya Kamata Ka Sani Game da Mulkin Allah

Wurin da aka kafa shi. Mulkin Allah, gwamnati ce da Allah ya kafa a sama.​—DANIYEL 2:44; MATIYU 4:17.

Dalili. Mulkin Allah zai sa duniya ta zama aljanna, inda dukan ’yan Adam za su zauna lafiya kuma ba za a ƙara yin rashin lafiya ko mutuwa ba.​—ZABURA 37:​11, 29.

Shugabannin Mulkin. Allah ya zaɓi Yesu ya zama Sarkin da zai yi mulki a sama tare da abokan sarauta guda 144,000, waɗanda aka fanshe su daga duniya.​—LUKA 1:​30-33; 12:32; RU’UYAR DA AKA YI WA YOHANNA 14:​1, 3.

Mutanen da za su amfana daga Mulkin. Waɗannan mutanen za su zauna a duniya. Za su goyi bayan sarautar Yesu kuma za su bi dokokin da aka kafa da son ransu.​—MATIYU 7:21.

Me Ya Sa Yesu Ne Ya Fi Dacewa Ya Yi Sarauta a kan ’Yan Adam?

Sa’ad da Yesu yake duniya, halinsa da ayyukansa sun nuna cewa shi ya fi dacewa ya zama sarki domin

  • Ya nuna cewa ya damu da talakawa.​—LUKA 14:​13, 14.

  • Ya tsani cin hanci da rashin adalci.​—MATIYU 21:​12, 13.

  • Ya nuna iko a kan guguwa da ruwa da makamantansu.​—MARKUS 4:39.

  • Ya ciyar da dubban mutane.​—MATIYU 14:​19-21.

  • Ya tausaya ma marasa lafiya kuma ya warkar da su.​—MATIYU 8:16.

  • Ya ta da matattu.​—YOHANNA 11:​43, 44.

Abubuwan da Mulkin Allah Zai Sa Ka Mora Yanzu

Za ka sami kwanciyar hankali idan kana goyon bayan Mulkin Allah. Dalilin shi ne, magoya bayan Mulkin Allah

  • Suna ‘iyakacin ƙoƙari su zauna lafiya da kowa.’​—IBRANIYAWA 12:14.

  • Suna jin daɗin zaman lafiya da haɗin kai a iyalansu don ma’aurata suna ƙauna da kuma mutunta juna.​—AFISAWA 5:​22, 23, 33.

  • Suna farin ciki kuma suna jin daɗin rayuwa don suna “jin Kalmar Allah,” kuma suna “kiyaye ta.”​—LUKA 11:28.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba