Ya San Kasawarmu
Levitikus 5:2-11
“NA ƘOƘARTA sosai, amma ban taɓa samun gamsuwa ba.” In ji wata mata game da ƙoƙarce-ƙoƙarcenta na faranta wa Allah rai. Jehobah Allah yana amincewa da iya ƙoƙarce-ƙoƙarcen masu bauta masa kuwa? Yana yin la’akari da iyawarsu da kuma yanayinsu kuwa? Don amsa waɗannan tambayoyin, yana da kyau mu yi la’akari da abin da aka ce a Dokar Musa game da wasu irin hadayu, kamar yadda yake rubuce a littafin Levitikus 5:2-11.
A ƙarƙashin Doka, Allah ya bukaci hadayu dabam-dabam don neman gafara na zunubai. A yanayin da aka kwatanta a waɗannan ayoyin, mai zunubin ya yi zunubi ne babu zato. (Ayoyi 2-4) Sa’ad da aka gaya masa abin da ya yi, wajibi ne ya furta zunubinsa kuma ya ba da hadaya domin laifinsa, wato, “’yar tunkiya, ko akuya.” (Ayoyi 5, 6) Amma idan shi talaka ne fa kuma ba shi da ’yar tunkiya ko kuma akuya da zai bayar? Shin Dokar ta ce dole ne ya ari wannan dabbar, da haka ya ci bashi? Shin yana bukatan ya yi aiki ne har sai ya samu damar sayan wannan dabbar, ta haka ya yi jinkirin neman gafarar zunubansa?
Don nuna tausayin Jehobah, Dokar ta ce: “Idan kuwa arzikinsa ba ya kai ya kawo yar tumkiya ba, sai shi kawo hadayassa ta laifi domin zunubin da ya yi, kurciya guda biyu, ko kuwa yan tantabarai biyu, zuwa ga Ubangiji.” (Aya 7) Za a iya juya furcin nan “idan . . . arzikinsa ba ya kai ya kawo” zuwa “idan . . . hannunsa bai kai ga.” Idan Ba’isra’ile bai da arzikin sayen tunkiya, Allah zai karɓi abin da mutumin zai iya bayarwa, wato, kurciya guda biyu ko kuma tantabaru guda biyu.
To idan mutumin bai da arzikin sayen kurciya biyu ko tantabaru biyu fa? Dokar ta ce: “Sai shi kawo hadayatasa domin zunubinsa da ya yi, kashi ɗaya cikin goma na ephah [kofi takwas ko tara] na gari mai-labshi domin hadayar zunubi.” (Aya ta 11) Ga talakawa marar arziki, Jehobah ya ce su ba da hadayar zunubi ba tare da jini ba.a A Isra’ila, talauci bai hana kowa samun albarkar neman gafarar zunubi ba ko kuma yin sulhu da Allah.
Menene muka koya game Jehobah daga dokar da ya bayar game da hadayun zunubai? Shi Allah ne mai tausayi da fahimta, wanda yake yin la’akari da kasawar masu bauta masa. (Zabura 103:14) Yana so mu kusance shi kuma mu yi dangantaka mai kyau da shi ko da muna fuskantar yanayi masu tsanani, kamar tsufa, rashin lafiya, nauyi na iyali da sauransu. Za mu iya samun ƙarfafa ta wajen sanin cewa Jehobah Allah yana farin ciki idan muka yi iya ƙoƙarinmu.
[Hasiya]
a Abu mai daraja a dabbar hadaya ita ce jininta, domin abu ne mai daraja a gaban Allah. (Levitikus 17:11) Hakan yana nufin cewa garin da talaka zai ba da bai da daraja ne? A’a. Jehobah ya ɗauki halinsu na tawali’u da kuma yardar rai da suke nuna wajen ba da waɗannan hadayun da tamani. Bugu da ƙari, ana gafarta zunuban dukan al’ummar, har da na talakawa, bisa hadayar da ake yi wa Allah a Ranar Kafara.—Leviticus 16:29, 30.