Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 7/1 p. 6
  • ‘Ku Ƙaunaci Juna’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ku Ƙaunaci Juna’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • “Ku Yi Zaman Ƙauna”
    Ka Kusaci Jehobah
  • Me Za Mu Yi don Mu Ci-gaba da Ƙaunar Juna Sosai?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Ƙauna Ta Gina Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Kada Ku Bar Ƙaunar da Kuke wa Juna ta yi Sanyi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 7/1 p. 6

‘Ku Ƙaunaci Juna’

“Sabuwar doka na ke ba ku, ku yi ƙaunar juna; kamar yadda ni na ƙaunace ku, ku ma ku yi ƙaunar juna. Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.”—YOHANNA 13:34, 35.

Abin da Hakan Yake Nufi: Kristi ya gaya wa mabiyansa su ƙaunaci juna kamar yadda ya ƙaunace su. Ta yaya Yesu ya ƙaunace su? Ya so dukan mutane duk da cewa nuna bambanci ga mata da kuma mutanen wata ƙasa ya zama ruwan dare a zamaninsa. (Yohanna 4:7-10) Ƙauna ce ta sa Yesu ya sadaukar da lokacinsa da kurazarinsa da annashuwarsa don ya taimaki mutane. (Markus 6:30-34) A ƙarshe, Kristi ya nuna ƙauna a hanya mafi girma. Ya ce: “Ni ne makiyayi mai-kyau: makiyayi mai-kyau yakan bada ransa domin tumaki.”—Yohanna 10:11.

Yadda Kiristoci na Farko Suka Yi Abin da Yesu Ya Ce: A ƙarni na farko, Kiristoci sun kira junansu “ɗan’uwa” ko “’yar’uwa.” (Filimon 1, 2) Akwai mutanen al’umma iri-iri a cikin ikilisiyar Kirista, domin sun gaskata cewa “ba wani bambanci tsakanin Bayahude da Ba’al’umme. Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa.” (Romawa 10:11, 12) Bayan Fentakos 33 A.Z., almajiran da ke Urushalima “suka sayar da abin mulkinsu, da dukiyarsu, suka rarraba wa jama’a bisa ga bukatar kowa.” Me ya sa? Saboda sababbin da suka yi baftisma su zauna a Urushalima don su “lizima a cikin koyarwar manzanni.” (Ayyukan Manzanni 2:41-45) Me ya sa suka yi hakan? Kusan shekara 200 bayan mutuwar manzanni, Tertullian ya yi kaulin abin da wasu suka ce game da Kiristoci: “Suna ƙaunar juna . . . kuma a shirye suke su mutu domin junansu.”

Su Wane Ne Suke Bin Wannan Misalin a Yau? Littafin nan The History of the Decline and Fall of the Roman Empire (1837) ya lura cewa tun ƙarnuka da dama, waɗanda suke da’awar cewa su Kiristoci ne sun “tsananta wa junansu sosai fiye da yadda arna [marasa bi] suka tsananta musu.” Wani bincike na kwanan nan a Amirka ya gano cewa mutane da yawa da suka ce suna bin addini sawu da kafa, kuma yawancinsu suna da’awar cewa su Kiristoci ne, suna nuna wariyar al’umma. A yawancin lokaci, masu zuwa coci ɗaya ba sa cuɗanya da ’yan ɗarikarsu da ke wata ƙasa, kuma sa’ad da bukata ta taso, ba sa taimaka wa juna.

A shekara ta 2004 bayan jerin mahaukaciyar gugguwa da ruwan sama da aka yi a Florida sau huɗu a cikin wata biyu, shugaban Kwamitin Ba da Agaji na Florida ya kai ziyara don ya tabbatar da cewa an yi amfani da kayan da suka kai yadda ya kamata. Ya ce babu wata rukuni da take da tsari mai kyau kamar Shaidun Jehobah, kuma ya yi alkawarin yi musu tanadin duk wani abin da suke bukata. A shekara ta 1997, rukunin ’yan agaji na Shaidun Jehobah sun kai wa ’yan’uwansu Kiristoci mabukata tare da wasu mutanen da ke Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango magani da abinci da tufafi. Shaidu a ƙasar Turai sun ba da gudummawar kayayyaki da suka kai dala miliyan ɗaya na Amirka.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba