‘Na Bayyana Sunanka ga Mutane’
‘Na bayyana sunanka ga mutane waɗanda ka ba ni daga cikin duniya; na sanar masu da sunanka, zan kuma sanar da shi.’—YOHANNA 17:6, 26.
Abin da Hakan Yake Nufi: Yesu ya sanar da sunan Allah ta wajen yin amfani da shi a hidimarsa. Sa’ad da Yesu ya karanta Nassi, kamar yadda ya saba, ya ambata sunan Allah. (Luka 4:16-21a) Ya koya wa mabiyansa su yi addu’a cewa “Uba, a tsarkake sunanka mulkinka shi zo.”—Luka 11:2.
Yadda Kiristoci na Farko Suka Yi Abin da Yesu Ya Ce: Manzo Bitrus ya gaya wa dattawan da ke Urushalima cewa Allah ya jawo jama’a daga cikin al’ummai “domin sunansa.” (Ayyukan Manzanni 15:14) Manzanni da sauran Kiristoci sun yi wa’azi cewa “dukan wanda za ya kira bisa sunan Ubangiji za ya tsira.” (Ayyukan Manzanni 2:21; Romawa 10:13) Kuma sun yi amfani da sunan Allah a rubutunsu. Wani tarin dokokin Yahudawa da aka kammala rubutawa wajen shekara ta 300 A.Z. ya ce game da littattafan Kiristoci da masu hamayya suka ƙona: “Sun ƙona dukan littattafan marubutan Linjila da kuma littattafan minim [waɗanda ake tunanin cewa Kiristoci ne Yahudawa]. Sun ƙona su ƙurmus . . . har da sunan Allah da ke cikin littattafan.”
Su Wane Ne Suke Bin Wannan Misalin a Yau? Revised Standard Version, wanda Littafi Mai Tsarki ne da aka wallafa da izinin National Council of the Churches of Christ in the United States ya ambata a gabatarwarsa cewa: “Kafin zamanin Kristi, masu bin Yahudanci sun daina amfani da sunan Allah domin shi kaɗai ne Allah, saboda haka babu wani muhimmancin yin amfani da sunan da zai bambanta shi da wasu alloli; kuma hakan bai da wani amfani ga bangaskiyar Cocin Kirista.” Saboda haka, suka sauya sunan Allah da lakabin nan “UBANGIJI.” Kwanan baya, Paparoma ya umurci limamansa cewa: “Kada ku yi amfani ko kuma ku furta sunan Allah da aka rubuta da baƙaƙe huɗu, wato, YHWHb a waƙoƙi da kuma addu’o’i.”
Su wane ne suke amfani da sunan Allah kuma suke gaya wa mutane game da shi a yau? Sa’ad da Sergey yake matashi a ƙasar Kyrgyzstan, ya kalli wani fim ɗin da ya nuna cewa Jehobah ne sunan Allah. Amma bai sake jin sunan ba har tsawon shekara 10. Bayan Sergey ya kaura zuwa Amirka, Shaidun Jehobah biyu suka ziyarce shi a gidansa kuma suka nuna masa sunan Allah a Littafi Mai Tsarki. Sergey ya yi farin cikin samun rukunin da ke amfani da sunan nan Jehobah. A ƙamus ɗin Webster’s Third New International Dictionary, a ƙarƙashin “Jehovah God” (Jehobah Allah) an bayyana cewa “shi kaɗai ne mafi iko da Shaidun Jehobah suka sani kuma shi kaɗai ne suke bauta wa.”
[Hasiya]
a A Luka 4:18, Yesu ya yi kaulin Ishaya 61:1 wadda ta yi amfani da sunan Allah Yahweh, wato Jehobah.
b A Hausa, ana kiran sunan Allah “Jehobah.”